POST 13

79 11 2
                                    

Zaune ta ke a gaban Malam Zailani abin duniya duk sun haɗe mata goma da ashirin, sa ke duba ƙasan ya yi sannan ya ce.

"Gimbiya akwai matsala mai girma da ta ke tunkarar kujerar ɗanki Sameer kuma in har ba mu yi kokarin gano bakin zaren ba to tabbas da matsalar za ta gagare mu gaba ɗayanmu asirinmu zai tonu, sannan abu na biyu dole fa sai an gano in da Tsohuwar nan ta ke don ita ce za ta warware kullin da ta yi, kuma Gimbiya dole da hannunki zaki warware domin warwarewar shi ne kwanciyar hankalinmu gaba ɗaya."
      Shuru Fulani Bilkisu ta yi tare da zurfafa tunani sannan ta ce.

"In don wannan ne babu matsala saboda mun san in da tsohuwar ta gudu ta ɓuya, yanzu ni babban matsalata shi ne gano wanene wannan fuskar da yake razanar da Sameer a gaban kowa kuma ba ta re da sanin 'yan majalisar fada ba Malam."
     Murmushi ya yi wanda ya bai yana jajayen hakwaransa sannan ya ce.

"Da tuntuni kun gano hakan kuma kunwa tumfar hanci da duk hakan bai faru ba Gimbiya Bilkisa, sanin asalin fuskar dake razanar da Sameer a fada daidai yake da sanin ainihim abinda ke binne cen karkashin kasar makabartan Agadas, ba shawara na ke ba ki ba kuma ba umurni ba ne amma duk yadda kika yi daidai ne, to amma ki sani Gimbiya Bilkisa babu ruwan Zailani akan duk abinda ya biyo baya kuskure an ri ga da an yi tun farko amma maimaita kuskuren zai zama ganganci a gareku da ni."
        Gaban Fulani Bilkisu ya faɗi saboda tuno mata abinda ta manta da shi, sharce zufar fuskarta ta yi za ta yi magana ya yi saurin ɗaga mata hannu tare da cewa.

"Wani kuskuren za ki ƙara tafkawa Bilkisa yin maganarki a yanzu daidai ya ke da buɗe bakin gawar da aka binne a ƙasar Mali, karki kuskura kice komai yanzu don an fusata da halinki ki ta shi kije zan ne me ki kamar yadda na ne me ki a yanzu."
       Ci gaba da bubbuga ƙasar ya yi tare da biris da ita don shi ma a fusace ya ke da ita saboda kuskuren da take tafkawa shi yake dawo wa ma a ka, ƙuri ta yi masa da ido sannan ta ta shi tabar ɗakin gaba ɗaya, ta kofar da ta fita ta nan ta koma ba tare da sanin kowa ba da ga cikin kuyanginta.

BAYAN MAKO GUDA

Alkur'ani ne a gabanta tana karanta suratul Yusuf aya ta sha biyu (12) sai ta ji hawaye na surnanowa a kan kuncinta saboda tuno abinda ya faru da ita a shekarun da suka shuɗe, kara maimaita ayar ta yi tare da zubar da hawayen lallai wannan ayar ta tuno mata da ranar da su ka zo gare ta tare da rokonta Yaya yaje su kwana tare don shi ma ya san ya za ma namijin da zai kwana ba'a ƙarƙashin ɗakin Ummansa ba, sharce hawayen ta yi sannan ta sake tuno a ya na yin da ta samu Yaya yana halin fitar rai, kuka take yi mai cike da nadamar barin Yaya da ta yi ya bi su a wannan ranar.

"Na yi nadamar barinka tare da su Yaya! NADAMATA ta zamo mara amfani tunda har na kasa kula da rayuwarka ba zan daina kuka akan sakacin da na yi da kai ba har ka rasa rayuwarka Yaya!"
      Cikin kuka take magana, kukan da ba ta bukatar rarrashi rufe Alkur'anin ta yi sannan ta faɗa banɗaki ta ɗauro alwala don nema masa gafara da kwanciya cikin salama a kabarinsa, ta daɗe tana neman gafarar Allah akan sakacin da ta yi na wannan ranar da ta zame mata ranar nadama, ranar da farin cikinta ya yi sallama da duniya haka kuma ranar da ta za me mata ranar nadamar rayuwarta, ranar da ba ta addu'a ko a mafarki ta ƙara cin karo da irin wannan ranar sannan ranar da ta za me mata silar shigarta cikin halinda take ciki kuma babu ranar fitarta a wannan ranar har sai ranar da ita ma ta bi shi in da ya ta fi.

Wannan Ke Nan

Abba ne zaune da doguwar fallen takarda a hannunsa zufa sai karyo masa take yi don bai son ta in da zai fara neman kuɗin da suke nema ba, Yaya Bilal ne tsaye a kan Abba yana magana amma kwata-kwata hankalinsa ba ya gurin shi fallen takardar ya amsa tare da karanta abinda ya ke ciki kamar haka.

JAN KUNNE!

Malam Bashir kar ka ce min har ka manta da Amininka tun yaranta kuma kar ka ce min har yanzu ba ka shirya bai yanawa iyalanka ainihin waye kai ba? Haba Malam Bashir in har kai ba ka shirya faɗa musu ba ni zan zo har gida na bai yana musu ainihin zahirinka kuma waye kai, nasan kai ma kasan matarka har yanzu ba ta san wa ye kai ba haka kuma 'ya'yanka ba su san waye ubansu ba, don haka yanzu ma zan ƙara baka zaɓi biyu ko ka ba ni damar bai yana wa iyalanka zahirinka ko kuma ka turomin da kuɗi kamar yadda ka turomin a wancen lokacin, sannan ina ƙara jinjina maka da irin namijin kokarin da ka yi gurin ɗaura min riba akan abinda na nema gaskiya na jinjinawa tunaninka na rashin son iyalanka su san zahirin haƙiƙaninka Malam Bashir, na biyu kuma zaka turomin da kuɗi naira dubu ɗari biyu da hamsin domin kulle bakina wannan shi ne iya adalcin da zan maka gurin tayaka rufa maka asirin da kake tsoron tonuwarsa, sannan ina ƙara tuna maka babu ɗan sanda (Police) ko wani jami'in tsaro a har kan nan, kar ka man ta da nasan garin da Sani yake haka kuma nasan Bilal ya na gida tare da kai, sai kuma autarka farin cikinka ina sane da duk wani shi ga da fitarta, shawara ya rage ga mai shiga rijiya ko ya faɗa rijiyar ko kuma ya yi wa kansa salama gurin fasa shi ga rijiyar, sannan karka manta tsalle ɗaya ake yi a faɗa rijiya in ko aka faɗa sai a yi dubu ba'a fito ba, Malam Bashir babu jami'in tsaro a harkar alkallarmu ina jiran sakonka da ga yanzu da kake karanta wasiƙar har zuwa nan da sati uku, sati uku kacal na baka don ha ka zaɓi ya rage na ka ga akawun lambata nan (account number) ka turo da kuɗin ko kuma in tona maka asiri.

DA GA BOYAYYEN AMININKA.

"Boyayyen Amininka Abba? Waye shi kuma menene dangantakarmu da shi da har ya san mu gaba ɗaya sannan har ya san ina gida waye shi Abba?"
         Yaya Bilal ya yi wa Abba tambayar ba yan ya gama karanta wasiƙar zufa sai karyo masa yake yi kamar ya haɗiyi kwaɗo, Abba ma share zufar gaban goshin shi ya yi sannan ya ce.

"Babana karka damu da sanin ko shi waye saboda sanin hakan zai iya za me maka sanadiyar tarwatsewar farin cikinku da ni baki ɗaya, babban abinda ya ka mata mu yi shi ne mu fara nemo hanyar da zamu samo kuɗin da ya bukata tun kafin lokaci ya kure mana, sai dai abinda ke damun zuciyata shi ne wanene ya tura masa kuɗin da na yi alkawarin daina tura wa? Na so tun wancen lokacin ya yi duk abinda zai yi shi yasa ma ban tura ba amma to waye ya tura?"
        Tsare Abba da ido Yaya Bilal ya yi yana kallon karfin hali irin na Abba bai damu da shi yasan ko waye ba sai dai damuwarshi sanin wanda ya tura kuɗin, kallon shi Yaya Bilal ya yi sannan ya ce.

"Abba koma waye wannan mutumin ka bar min komai a hannuna zan binciko shi a duk in da yake a faɗin duniyar nan."
             Abba ya yi saurin taro numfashinsa da cewa.

"Karka fara ganganshin yin hakan domin yin hakan kamar fallasawa duniya zahirin abinda ke ɓoye ne a cikin duhu, Babana ina rokonka da ka ta ya ni zama duhun da zai baƙanta zuciyar mahaifiyarku da ni kaina a kan sanin haƙiƙanin zahirin abinda ke lulluɓe a duhu, haka kuma ba na tausayin kaina kamar yadda nake tausaya muku don Allah na rokeka karka yi tunanin binciko Boyayyen Aminina!"
        Idanun Abba sunyi ja kamar ba shi ba, jikin Yaya Bilal ne ya yi sanyi tare da fatali da duk kudurorin dake zuciyarsa ga me da Boyayyen Aminin Abba, sadda kansa ƙasa ya yi sannan ya ce.

"Yanzu Abba ta ina zamu fara samo wannan kuɗin da ya tambaya? Kuma in mun ba shi yau gobe ma kara tambaya zai yi a lokacin da bamu da komai Abba ba ka tunanin zai aikata abinda ya yi niyya a lokacin tunda bai samu abinda yake so ba?"
          Sauke ajiyar zuciya Abba ya yi tare da cewa.

"Akwai Allah Babana yanzu dai mu fara nemo kuɗin sannan duk wani tunani ya biyo baya, ni babban damuwana bai wuce rashin sanin wanda ya aika masa da kuɗin ba sannan ina gudun kar Sani yasan da zan cen don na shi ba zai yi kyauba, ba re kuma auta dole hankalinta ya ta shi."

"Amma Abba ba ka tunanin samun matsala a lokacin bikin auta? Saboda nasan dai gonar da ta rage mana kuma ake ajiyarta don bikin auta za'a siyar kar muji kunya fa Abba."
        Cewar Yaya Bilal, Abba ya ce

"Duk abinda ya sauwaƙa shi za'a kai mata ko gado da kujeru ne aka samu sai ta yi maleji kafin a samu wani kuɗin da za'a canja mata ko da a gidan mijinta ne"
        Yaya Bilal bai ce komai ba sai kallon Abba yake yi a ɗan ƙanƙanin lokaci duk ya fita hayyacinsa ya zama abin tausayi, ajiyar zuciya ya yi tare da maganar zuci.

'Ga wani abin tausayin na tankaro mu akan bikin auta dole sai an kai zuciya nesa don tursasata in ba haka ba akwai matsala, Allah ka shigo lamuranmu Ya Rabbi.'
        



_______________________________



@Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now