POST 15

83 12 2
                                    

Duk wani abinda yasan ya tara ko kuma yake kai wa gurin ajiya ya karɓo har da bashi ya haɗa don dai kawai ya gyara fentin motar amma har yanzu ko rabin kuɗin fentin bai haɗa ba, abin duniya duk ya ishe shi ga shi yana son ganin Baseera a ko wani irin hali a yau, yanke shawarar ɗaukar motar ya yi don zuwa gurin ta amma ko da ya isa numbern ta ba ya shi ga don dole ya samu yaro ya aika, tare da Yaya Bilal yaron ya fito ya nuna masa mai kiran Baseerar, kwankwasa gilashin motar Yaya Bilal ya yi Zaid ya yi saurin fito wa saboda kamannin Baseera da ya gani a tare da Yaya Bilal, miƙa masa hannu Yaya Bilal ya yi amma Zaid yaƙi amsa, abin nan da ya yi yasa Yaya Bilal ƙara aminta da shi.

"Kai ne me zuwa gurin Baseera?"
       Cewar Yaya Bilal. Zaid ya yi saurin amsa wa da eh kan shi a ƙasa, gyara tsayuwa Yaya Bilal ya yi sannan ya ce.

"Da gaske kake son ƙanwata ko kuma da wata manufa ka zo?
       Zaid ya ce.

"Wallahi da gaske na ke sonta kuma niyyata in aureta shi ne dalilin da yasa na ke zuwa gurinta."
     Murmushi Yaya Bilal ya yi sannan ya ce.

"To in har da gaske kake yi ka je ka turo manyanka saboda a tsaida magana domin ba na son ta wuce wata huɗu a gidan nan."
          Farin ciki ne suka bayyana a kan fuskar Zaid har kasa magana ya yi, Yaya Bilal ya fuskanci halin da ya ke ciki yasa ya yi masa sallama tare da koma wa gida, tun fitar Yaya Bilal da ɗan aiken Baseera ta ke cikin zullumi saboda ta san dai gobe Chocho zai yi tafiya Zaid kuma kusan sati uku ke nan rabon da ya zo gidan su.

'Allah ka sa Chocho ne ya zo sallamata don ni har yanzu zuciyata ba ta gama aminta da Z Guy ba saboda gayen ba wani kuɗin a zo a gani ya tara ba, amma dai ya na da bright future a nan gaba don a yadda na lura nan gaba shi za a ba wa M.D a kamfaninsu saboda kwazo da jajircewarsa a kan aiki, sannan in za su yi taro shi ne yake wakiltarsu ko dan ƙetare ƙasashe da yake yi zan yi maleji na aure shi, amma in so zai zama samu to ni Chocho nake so da aure Guy ɗin ya iya making love kuma hannunshi a buɗe ta ke ba irin Zaid ba da kyautarshi bai wuce dubu goma zuwa sha biyar.'
       Shi go war Yaya Bilal ne ya katse mata maganar zucin da take yi kusa da ita ya zauna tare da cewa.

"Baseera kamar yadda na faɗa miki ne a ba ya, to yau Allah ya cika min burina kuma mun daidaita da yaron zai turo manya don maganar gemu da gemu yafi karko a kan maganarmu mu yara, amma ki sani ba za mu muki dole ba in har ba kya son sa yanzu zan koma in ce masa ba kya so kuma karya ƙara zuwa gurinki."
      Gabanta ne ya faɗi tuno wa da maganar Chocho sannan ga kuma maganar Zaid.

'Me zan kai wa Zaid a matsayin tukwicin soyayyar da ya min? Wani bakin ciki zai shi ga a ranar da na za ma matarsa? Saki na zai yi na dawo gida ko kuma wulakantani zai yi?'

    Maganar zucin da take yi ke nan amma a fili ƙaƙalo murmushi yaƙe ta yi sannan ta ce.

"Ina son duk wanda ka yarda da hankalinsa da nutsuwarsa nima ina sonsa."
        Murmushi Yaya Bilal ya yi sannan ya ce.

"Ja'ira ko kunyar nan ke babu wato kina sonsa ke nan, kuma gaskiya yaron akwai nutsuwa da ga gani ya samu tarbiyya da ga gida sannan kin ga kafin mu je kauye za a tsayar da rana da mun je sai a faɗa musu mu ma mun wuce gorin mutanen kauye."
       Ya na kai wa ya ta shi yabar gurin, gyara jikinta ta yi tare da sallamar Umma da tun ɗazu bakinta ya ki kulluwa saboda farin cikin yau ɗaya autarta ta tsayar da mijin aure.
     Kwankwasa gilashin ta yi kafin ya buɗe mata motar duk sai da ya share zufar da yake karyo masa saboda lokacin da suke magana da Yaya Bilal wani yaro ya zo wuce wa da ƙusa a hannunsa ya karce jikin motar, Yaya Bilal ne ya yi kokarin korar yaron amma Zaid ya ce a bar shi ai yaro ne amma a cikin ƙasar zuciyar shi kamar ya kurma ihu yake ji, don da zai samu damar dukan yaron da Allah ne ka ɗai ya san irin dukar da zai masa.

"Sannu da zuwa Habibina."
        Yaƙe ya yi wanda a ka ce ya fi kuka ciwo ya ce.

"Sannu da fito wa sarauniyar matan duniya wacce ta fi ko wata mace iya ado da tafiya."
       Farin ciki ne kwance kan fuskar Baseera sannan ta ce.

"Honey Allah dai ya kusan cika mana burin mu zan zama matarka ta har abada."
        Shi ma murmushin ya yi sannan ya ce.

"Zan kai ki in da baki bai taɓa furta wa ba zuciya bai taɓa hasasho miki ba, ƙafa bai taɓa zuwa ba, sannan zan shayar da ke zumar soyayyar da ba ki taɓa ji ko ganin irinsa ba, zan kai ki gidan da ba ki taɓa zaton shi ga ba ko a mafarki, sannan kuma zan ba ki dama ki zaɓo mana in da ki ka ga ya dace muje shakatawa bayan aure don ba na son auren ya ɗauki lokaci mai tsawo, kamar yadda Yayanki ya faɗa nima hakun na ke so."
       Farin cikinta mai musaltuwa ne ko shi ma ya gano hakan, amma abinda ke damunsa ba ta taɓa kai shi gidansu na Malali G.R.A balle ya san 'yan gidan suma su san shi kasa hakuri ya yi har sai da ya furta ya ce.

"Bassylurv ba ki taɓa kaini cen gidan mun gaisa da su ba ko kina tunanin nan zan kawo kuɗin aurena kuma a nan za a ɗaura mana auren.?"
       Gabanta ya ne faɗi rasa abin faɗa ta yi sannan ta ce.

"Haba ba haka ba ne kasan da ya ke daddyna bai cika zama a garin nan ba ne saboda duk harkokinsa a cen ne, Italian shoes yake kawo wa ƙasar nan kuma duk 'yan majalisar ƙasar na da gwamnoni da shugaban ƙasa shi yake kawo musu takalma, wannan dalilin yasa bai cika zama a nan ba kuma ni ina zaune da Uncle dina ne kamar yadda na faɗa maka ne tun farko nafi son rayuwar talakawa a kan foreign life shi yasa na ke nan, sannan ai daddy ya san da kai har cewa yake yi in gaisheka kuma ka ga yau babu wanda zai kai shi farin cikin tsayar da mijin auren da na yi kila gobe ko jibi ya ce mu je Saudiyya saboda fara siyayyar kayan aurena."
        Fatar jikinta ka ɗai ya kalla ya tabbatar da abinda ta ke faɗa saboda kashe mi shi kuɗin da take yi.

"Ni da ma so nake ya san da ni tunda ya sani ai shi ke nan kuma Yayankin nan ya na da kirki sosai."
         Cewar Zaid. Ci gaba da hirar soyayyarsu suke yi da kuma yadda bikinsu zata kasance in lokacin ya yi Zaid bai faɗa mata lokacin da a ke son bikin ba kuma ita ma ba ta tambaya ba a haka suka rabu. Ko da koma warta gida hirar auren Umma suke yi da Yaya Bilal ba ta shi ga hirar ba, sai ma ɗaki da ta shi ge abinta har sai da Abba ya dawo sannan ta fito, kusa da shi ta zauna ta re da ce.

"Abbana."

"Na'am autata."
       Cewar Abba, sadda kai ƙasa ta yi sannan ta ce.

"Abbana ka ga yanzu maganar aurena zaku fara shi ne nace ni ku bani kuɗin komai zan siya da kaina saboda na fi ku sanin kaya masu kyau kuma na zamani, ka ga Abba in ku ne ba za ku zaɓa min kaya masu kyau ba ka ji Abbana?"
     Shuru Abba ya yi saboda bai san ta in da zai fara maganar kayan auren ba sauke ajiyar zuciya ya yi sannan ya ce.

"Karki damu 'yar Abba, Babana da Yayanki suma sun san kaya masu kyau 'yan yayi kuma na zamani wanda zasu dace da zamaninki kin ji ko? Don haka ki kwantar da hankalinki komai za a miki yadda ke ki ke so ko auta? Oh! Auta ko kunyar nan babu kawai in ba ki kuɗi ki haɗa kayan aure ko dama tuntuni an gaji da zaman gidan Abba ne auta.?"
     Saurin rufe fuskarta ta yi ta ta shi da gudu tabar gurin da dariya ya rakata sannan yana yin fuskarsa ta canja zuwa baƙin cikin yadda zai fita kunyar Baseera, bai san da wasu kalmomi zai fara ba ta hakuri a kan kayan auren da zasu mata ba sannan ga Boyayyen Amini shi ma kuɗi yake bukata kuɗi masu yawa. Idanunshi ne suka yi jajir saboda baƙin ciki a ya yin da yake maganar zuci ya ce.

'Da na ji kunya idon 'ya'yana gwara na ji kunyar kai ki babu komai Auta saboda baƙin cikin bayyanar abinda ke ɓoye daidai yake da rasa rayuwata, ba zan jure ganinku cikin damu wa ba haka kuma ba zan iya ɓuɗe ido in kalli Ummu Aishatu cikin baƙin ciki da da na sanin aurena ba Baseera ki yi hakuri da sannu zan samu kuɗin da zan cika miki ɗaki da jere, amma yanzu kam ko tabarma na samu zan kai ki da shi in har asirina zai ci gaba da ɓoyu wa gurin Ɓoyayyen Aminina,'

Wannan Ke Nan

_______________________________

Ni Basira na ce Uhnmmmm duk yadda takwara Baseera ta ke zuzuta kayan ɗaki a ce da tabarma za a kai ta? Gaskiya akwai rigima a gaba tabbb!

Drop your comments about the charming chapter or i will stop posting the novel. Faƙat

Wattpad @Basira_Nadabo

Basira Sabo Nadabo Ce.

NADAMATA! PART ONE Where stories live. Discover now