Babi na Daya

616 30 5
                                    

Sansanyar iskar damuna ce take kadawa azaune macece Yar kimanin shekara 34 zuwa da 35 kyakkyawa ce irin kalar Nan da ake Kira da chocolate wato black American azaune take a kan kujerar roba a matsakaicin tsakar gida tana tsinke ganyen zogale tana Tarawa a wani madaidaicin kwano yayin da radio ke Yi agefen ta Shirin ku karkade kunnuwa take ji a tashar Freedom radio dake jihar Kano littafin da ake karantawa na wacece Uwa? ya tafi da ita matuka acikin zuciyar ta take sakawa wato kowa dai da tashi kaddarar ,kalmar kaddara da ta gifta azuciyar ta ta dauke ta ta hulla duniyar tunani rayuwar ta ta baya wajejen shekarar 1992" zo nagani ko kin iya rubutu durkusa Naga ba tare da tunanin komai ba ta dur kusa shi Kuma ya fara abunda ya Saba"salamu alaikum Umman mu kin ganni Sai yanzu ko ,abunda ya dawo da ita daga duniyar tunani kenan tai saurin share idonta Don Kar yarta tagani ta kakaro murmushi ta Dora afuskar ta, ai nasan halin ki indai kuka hadu Sai Allah yanzu Ina dinkin kin karbo eh na karba cewar Ni'ima baki ga dinkin ba Umman mu yayi kyau Bari waalida ta dawo nasan itama zai burgeta Nan suka cigaba da gyaran zogale ita da Ni'ima suna Sansa musaman da yake da amfani ga jiki.
Bayan sallar magarib suka zauna cin abinci mazan kwano daya Sai su Ni'ima tare da ummansu kasancewar Mai gidan baya gari Sai weekend yake zuwar masu shima ba kowanne sati ba ya danganta da yanayin aiki sa lokacin kasancewar hydrologist su kan shafe lokuta suna field work .Karfe Tara dai dai yaran suka wuce makwancin su Waleed da Nura dakin su daya daga farkon falon su Sai ka wuce corridor Inda zaka fara tarar da dakin abbansu Sai na umma sannan nasu walida akarshe kowannane da toilet cikinsa ,sannan akwai toilet a drive in din su saboda baki maza , ta shige dakin ta ta zauna agefen gadon sannan ta Kara Kiran maigidan in da suka Dade akan layin wayar su na tattaunawa ba komai suke tattaunawa Sai game da al'amuran yau da kullum karfe 10:30 sukai sallama kasancewar gobe tana da aiki.
Karfe 7:30 yaran suka kammala Shirin makaranta Banda Ni'ima kasancewar admission take jira a university bayan fitar su itama ta Soma kimtsawa tai Shirin fita aiki Ni'ima tana tambayar umma Mai za'a dafa tace duk bunda yazo Miki ki dafa sauri nake kafin na shiga aji zanyi submitting abstract na conference paper Dana ce Miki na promotion dau waya ta ki nemon opay kan na gama ya zo , umma kina son opay wlh cewar Ni'ima ta bata amsar ba dole ba Yan sahu suyi ta hada maza da Mata Kai magana su fada maka bakar magana in kuwa opay ne na dauki shata har kofar Central admin Ina submitting Sai na bi ta cikin legal na shiga management class Din da zanwa lecture public ne Adan baya baya suke rufe bakin ta ke da wuya Mai opay yai waya akan cewa ya iso Ni'ima ta raka ta har gate umma gaskiya ya kamata ki Sai Mana mota to Ni'ima Sai nai Miki aure suka Dara gaba tai Mata fatan dawowa lfy ita Kuma suka dauki hanya zuwa Central admin KSP.
Barrister Aisha Umar kafin madaki kenan Yar asalin garin kafin madaki dake jihar bauchi wacce aure ya kawo Kano kasancewar mijin ta Dan jihar Kano a unguwar dogon nama Wanda suke zaune a unguwar tudun Yola tana da yara hudu Ni'ima itace Babba Sai Waleed Wanda sunan babanta yaci wato Umar Sai kuma waleeda wacce ta ci sunan kakar ta gun uba wato Nafisa Sai kuma auta Nura.Lecture ce a Kano poly sannan Kuma tana cikin kungiyar lauyoyi Mata dake yaki da fyade da cin zarafin Mata ,tana da kirki sossai Amma Bata da yarda musaman ga opposite jinsin ta (maza)Bakomai ya janyo haka ba illa bakin fentin da suke dashi a idon ta al'amari da ya wanzu tun tana shekarar 7-9 Amma bai bar kwakwalwar ta ba ko abbasu Ni'ima ya Sha fadi tashi kan auren, su mikin Yana zuciyar ta Har Abada Bata taba fadawa kowa abunda ta sani duk sanda ta zauna ita kadai Sai abun ya fadomata sannan Abu daya ta rike shine ta barshi da Allah zai Mata sakayya domin baya bacci Yana sane duk wani azzalumi ,ya saka rigar mutumci a idon iyayenta da sauran dangi Kai har ma da mutanen gari Amma ita idonta ya fi bakin kumurci Muni shiyasa fa Bata gaisheshi to ta gaida shi tace ta gaidawa Wanda yaso cutar ta Allah ya tserar da ita mutane irin sa sunawa iyaye illa matuka saboda an yarda dasu Ashe suna can suna zalumtar su ta Inda Basu zata ba ai koma meye halaccin iyayen ta gareshi bai kamata ya saka masu da haka ba Hajiya mun iso kiyi making payment din , bayan ta biya ta sauka ta shige Central admin.
Aji ta wuce kasancewar lokaci yayi tai musu lecture ta 2hours daidai sannan ta fito Wanda yai daidai da karfe 12 na Rana opay ta Kara Kira Don gida takeson wucewa tayi kwa sa'a ta samu akan Kari ba tare da Shan wuya ba kasancewar garin da go slow yasa ta Dan Jima Bata Isa gida 1 saura ta Isa Ni'ima ta tarar na kallon MBC 2 in da suke nuna Harry Potter and the half blood prince tai ma umma sannu da zuwa tace to a tashi ai sallah Don in kuka dasa t.v agaba to bakwa gajiya barin wannan tatsuniyar dariya Ni'ima tai tace to umma suka Mike Don gabatar da sallar Azhar bayan sun idar suka saka abinci suna ci tare Don sun San su waleeda Sai 2 Kuma kan su iso Sai 2:30 bayan sun gama cin abinci suka Dan Mike Sai ga su waleeda sunyi salama uhm umma yauwa ai makaranta har gitsewa tai an kaama wani mutum zai shiga toilet da wani Kullin Abu Ana ta kacaniya shine aka Kira Yan sanda suka tafi shi duk suka Kama salati lamarin duniyar Sai addu'a umma tace to nasan dai kunyi sallah amakaranta to kuje ku kintsi kuzo kuci abinci Don Kar a makara a islamiyya Waleed cike da tsokana yace ai umma waleeda Zaki fadawa itace sarkin makarar da mutane Sai ta tsaya ita Sai gogangen hijab duk aka saka dariya Banda waleeda data hade Rai Nan suka Mike sukai daki waleeda na cewa Yaya Ni'ima yaushe aka fara Harry Potter ,kan ta bata amsa umma tace kin wuce ko sainazo Ana maganar islamiyya tana maganar wani Harry Potter ke da kike da abubuwan Yi agabanki yau zamu jira ma tare zamuyi girkin dare da mutum Ni'ima ta kunshe dariya Don tasan halin waleeda da rashin son motsa jiki sai son jiki Kamar Yar mage

*Wannan labari kirkiranrene it's fiction*
#H.A#
*Mrs Sadi*

Har AbadaWhere stories live. Discover now