3

131 8 2
                                    


Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

MUDDASIR! MUDASSIR!
Naam Hajiya!
Akwai abunda zan miki ne ?
Eh! Ina so ka bi driver zai je dauko yara makaranta sai ka siyomun abunda yake cikin list din nan.
Lizz? Hajiya mecece Lizz? Ya tambaya 😂😂
Ba Lizz ba! List nace Ina nufin abun da na rubuta a cikin wannan takaddar .
Ina ka iya karatu?
Ayyah Hajiya wallahi ban fahimce ki ba.
Gaskiya ban iya karatun Boko ba Ina dai kokarin koya ne.
Allah sarki na zata ka iya ne ai dake ILYASU DA HARUNA Duk sun iya( Almajiranta na da da suke mata aiki! Sun iya karatun turanci sosai . HARUNA kam har wani slang yake yana karya murya in yana turanci. HARUN ENGLISH GUY ake kiransa Dan tsaban karya da son ace ya iya turanci a cikin almajirai. Har makarantar boko ya shiga. Karantun allon ba wata damuwa yayi da ita ba. Burinsa kawai ya iya turanci kamar YUSOOOF Babban Dan Hajiya ! ILYASU ma wajen YUSOOOF ya koya. Saboda YUSOOOF bashida girman kai da yake shi daya ne namiji duk kannensa matane sai Dan autansu Dan shekara 4 shine namiji. Sai ya ringa shiga cikinsu almajiran yana koya musu abubuwa baya kyamatarsu har kayansa da takalmansa yake basu yanzu ma yyana karatu a SHARDA UNIVERISITY dake New Delhi a kamar India. Shiyasa MUDASSIR bai sansaba).

Shiru tayi sannan tace ok babu damuwa yanzu dai ka bi driver in kun dau yaran sai ka bawa ZAHRAH sai kuyi siyayyar tare tunda ba wani yawa ne dashi ba.
Toh hajiya ! Ya fita ya iske MUSA driver ya shiga suka tafi AL- AFIYAH INTERNATIONAL ACADEMY daukan yaran.

Wacece Hajiya?

Hajiya wato Hajiya Maryam Muktar mata daya tamkar ga dubu a wajen Alhaji Maina Sidi. Mace mai hakuri, takwalli, addini, mai zuciyar neman nakanta da taimako. Duk irin kudinda take dashi da kuma matsayin mijinta bata dau duniya da zafi ba. Ita take girkinta kuma har mai gadi da masu aikin gidan ita take girka musu abinci. Haka zata zaga idanta ta taya masu aiki suna gyara gidan tare. Ga saukin Kai shiyasa Alhaji Maina ke masifar ji da ita.
Alhaji Maina Sidi kanuri Dan Bama daga jahar Borno. Yayi commissioner sau uku a zamanin mulkin SAS , Sannan yayi minister mai sau biyu a lokacin shugaban kasa Umaru musa yaradua Ya kuma maimaitawa a mulkin Good luck Jonathan in da aka mayardashi minister kula da lafiya wato minister of health. Yana taba kasuwanci sosai dake daman babansa Dan kasuwa ne shima da ya girma ya gaji kasuwanci babansa. Allah yasa mai Albarka sosai kasuwanci har yafi baban nasa. Hajiya Maryam kuma hausa- fulani ce, daga Zaria.
Acan suka hadu da Alhaji Maina a jami'ar ABU Zaria . Ita tana karanta fanin Education shi kuma Political Science.
Haka suka fara soyayya mai tsafta har takai sukayi aure bayan sun kamala karatunsu.
Suka dawo Maiduguri da zama. Da ya zama Minister ne suka tattara suka koma abuja da zama.
Suna da yara shida. Maza biyu sai mata hudu.
Babban dansu shine YUSOOOF (21), sai ZAHRA(18) WALIDAH(16), MABRUKA(12), FIDDAUDI (8) sai autan su IBRAHIM(4).
Hajiya Maryam na da burin koyarwa Amma sai Alhaji Maina ya bata shawaran ta bude makarantan kanta. Shine ya taimaka mata ta bude makaranta mai Kyau mai suna AL- AFIYAH INTERNATIONAL ACADEMY. Yaransu ma Duk Chan suke zuwa. Makarantar Akwai karatu sosai. British curriculum suke. Sannan Akwai Islamiya bayan an tashi .Akwai na weekends da hutu. Har matan aure na zuwa. Manyan maza ma ba'a bar suba a baya ba Akwai nasu islamiyar. Sannan Akwai adult classes ga wanda basu taba zuwa makarantaba ( Dan su yi yaki da jahilci). Sannan itama tana business na laces , atampa, jaka, takalmi da sauran kayan mata. Shaguna biyu gareta. Bata da matsalar KUDI
Wannan kenen!

MUDDASIR, sunje Al-AFIYAH sun dauko su ZAHRAH a school sannan ya bata paper list din. Daman Hajiya ta kirata ta fadamata.
Haka suka wuce new sahad store sukayi siyyah suka dawo.
Suka taradda Hajiya a babban falon kasa suna ta jera abinci a dining da alama Alhaji wanda suke kirada Abba yazo.
Karasowa ciki yaran sukai bakinsu dauke da salama. Suka durkusa har kasa suka gaisheta sannan suka gaishe da masu aikin da suke taya Mama wato Hajiya.
Murmushi tayi tace kun gaji ko yan albarka. Kushiga cikin kuyi wanka kuyi Sallah sai kuzo muci abinci ga Abbanku ma ya iso.
Wuce wa sukai ciki da murnar Abbansu yana gida.
MUDDASIR kai kuma kabi Nene ta baka abinci in kayi sallah.
Toh Hajiya !
Ya fita.
Yana idarda Sallah ya dawo ya amshi abincinsa ya ma Hajiya salama kan sai gobe zai sake dawowa.

Bayan yaran sunyi sallah. Dukkansu Abba, Hajiya da yaran duk sun zauna a Dining dan cin abinci tare. Haka al'adar gidansu yake . Tare suke cin abinci . Sannan su tattauna matsalansu. Dan ma abba bai cika zama ba yana yawan fita waje Harkan business nasa sannan ga meeting na siyasarsu da suke yawanyi yanzu. Amma Duk da haka . Haka suke zama Suci abinci da Hajiya ko baya nan. Haka in Yaya YUSOOOF yana nan Duk tare suke ci( ko shiyasa dukka suke Kaunar junansu kuma suka shaku da juna sosai? Ohoo! 🤷🏻‍♀️).

Haka Hajiya ta tashi tace Toh Yallabai me za'a zuba maka tana bude Warner's din dake kan dining table din.
Murmushi yayi yace Sarauniya komai inaso.
A'ah His excellency fada mun zaifi armashi tafada tana kashe masa ido.
Okay toh ya ce samun semo da vegetable soup din . Dan gaskiya ya tafi da imanina.
Dariya yaran sukayi kasa kasa Dan sun saba da salon soyayyar iyayensu.
Haka tayi serving nashi ta sa masa zobo dake shine favorite sannan tasa nata tayi zamanta. Sannan ZAHRA ta tashi ta sama kowa nashi.
Wow delicious gaskiya gimbiya kina kashe ni da betta wallahi. Kinsan Allah Duk time din da wata tafiya ta kamani Allah damuwa nake shiga inna tuna bazan samu irin kalar girkinki a ko ina ba. Shiyasa ko gidan abokai na nan cika cin abinciba. Allah ya miki albarka.
Ameen tace tana dariya.
Yaranma dariya suke sosai wai Abbansu na santi 😂😂.
Juyawa yi yace yara wallahi ku zage kuci abinci sosai Allah ne ya baku uwa gwana a iya girki da komai ma. Take mai kafa Hajiya tayi Dan da Allama Abba zai iya fadin wata kalmar su ji kunya😆😆😆.
Af🤭Hajjaju. Yace am telling you.
Gyaran murya tayi tace. Yallabai! Ina son muyi wata shawara dakai.
Ina jinki!
Ina wannan yaron nan da yake mana aiki nan MUDDASIR!
Eh, mai son aikin nan ko?
Eh shi
Toh ya akai?
So nake na sashi a AL-AFIYAH!
Dago kai yaran sukai gaba daya suna mamakin mamarta su.
Shima yayi mamaki. Amma da ya tuna wacece Hajiya Maryam zatayi fin haka Ma sai yayi murmushi!
Yace kinaga ba matsala?
Gaskiya Alhaji na yaba da hankalin yaron sosai wallahi.
Kinsan labarinsa?
Eh to gaskiya ba duka ba yade fada mun cewa mahaifinsa ya jima da rasuwa Amma mahaifiyarsa na da rai. Yanzu haka tare suke zama da mahaifiyarsa acan kasan layinmu wajen tsofin gidanjen nan.
Toh! Allah ya taimaka hajjaju!
Allah ya kyautata niya!
Uwar marayu Allah ya bada lada.
Shi kuma Allah yasa ya amfana da karatun.
Ameen Alhaji nagode sosai. A kullum kana saurarona idan nazo da Magana kuma kana bani goyan baya a duka lamarina.
Allah ya bar kauna.
Ameen .
Ba dole ba mutum yana da mata kamarki ai dole ne a saurareki tunda kullum kalaman bakinki masu muhimmanci ne.
Murmushi tayi.
Suka ci gaba da tattaunawa suna cin abinci.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now