4

83 5 0
                                    


Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

MUDDASIR na fita straight gidansu ya wuce wajen Innarsa. Ya same ta kamar kullum tana zaune a sakar gidan tana shan iska.
Salamu Alaikum
Walaikum salaam! Babana!
Inna na dawo. Inna wuni innah?
Ya zaman gida?
Zaman gida Alhamdulliah Babana.
Ya aiki?
Alhamdulliah Inna.
Masha Allah , Allah yasa albarka ya taimaka.
Ameeen inna.
Ajiye kwanan abincin yayi ya dauko pure biyu da ruwan wanke hannu.
Yace Bismillah Innah ga abinci.
Murmushi tayi Toh Babana Allah yayi albarka.
Haka suka ci abinci yauma kamar kullum yana bata labarin abubuwan da yayi yau. Haka yake baya boye mata komai a rayuwarsa. Komai yasamu innarsa! Komai zai yi sai ya fada innarsa. Bashi da amini kaf duniyar nan kamar innarsa, Itace komai nasa. Ita kuma haka zata saurareshi tas koyayi ba daidai ba bata magana har sai ya gama fada mata. Sannan ne zata gyara masa duk kuskurensa, ta karamasa karfin guiwa ,sannan tabasa shawarwari , ta masa nasiha a karshe tayi masa addua sosai.
Haka suka zauna suna ta hira kamar kullum har zuwa lokacin sallah tunda yanzu ya daina bara.  Sannan ya mike ya shiga bayi don kama ruwa yayi alwala ya dau allon karatunsa zai fice masallaci daga can ya tsaya karatu . Haka innarsa ta bisa da adduar sa'a, kariya da shimar albarka kamar kullum yayinda itama ta mike don daura nata alwalar.

Yana iddar da Sallah ya zauna daukar karatu . A inda yake bada haddarsa na suratul Rahman. Inda malamin yake masa fassar suran. Saurara yake yana jinjina wannan surah mai daraja.
Malamin yake masa bayani wannan surar itace surar da Allah zai karanta dakansa da wata murya mai dadi kanar da babu kowa a duniya. Inda Allah zai fara tambaya yace : Limanin mulkul yauma? Ma'ana yau mulkin nawanene? Waye keda mulki yau?
Ayayinda duniya tayi shiru tsit babu komai babu kowa . Duk Muna kwance a kabarinmu kasa ta rufe mu rub babu rai a jikinmu.
Sannan ne Allah zai amsa da kansa yace Shine da mulki. Mulki nasa ne.
Sai ya fara karanta wannan surah mai tarin daraja wato Suratul Rahman. Inda yake bayyana mulkinsa da sarautarsa.  (Subhanallah🥺😭Allah ka yafe mana! Hakika bamu iya ba bazamu iyawa kanmu ba ka iya mana, bamuda wata Gata a duniya da lahira sai naka).
Sannan Malamin ya daura da cewa Suratul Rahman na da falala dayawa.
A cikin falalar karanta Suratul Rahman itace waraka ce daga yaye damuwa da kunci (depression).
Suratul Rahman na wanke dattin zuciya .
Sannan likkitocin addinin sun sheda yana warkar da cutar cancer. Kariyace ga mai yawan karantata yana zamo Jagora ga rayuwar mai karantata.
Zata zo a suffa kyayyawa ga mai karantata rannan Alkiyamah ya yi Magana a madadin mai karantata.
Sannan ita din rahama ce ga mai yawan karanta ta.
Yana sanya haske da kyawun fuska (glow) ga mai karantata.
Farkon Ayar Suratul Rahman - wato AR-Rahman daya daga cikin sunan Allah ne dake cikin 99 Asma'ul lahil husna ( Sunayen Allah) bi ma'ana mai yin rahama ga bayinsa.  Suratul Rahman tana da falala dayawa wanda ba'a baiyana taba.
Wallahu ala lamu.
Haka suka kammala karatun ranar ya koma gida yana mai jinjina girman da falalar wannan surah mai daraja. Dakuma godewa Allah da ya azurtasa da addinin musulumci.
Domin tabbas Allah yayi ka acikin wannan addinin mai tarin daraja wanda komai yake asare ba karamar arziki Allah ya maka ba. Addinin musulumci bai bar kowacce Babi ba. Annabi bai bar duniya ba sai da ya kammala mana komai game da addininmu. Kada kansa yayi yace Allah kasa mu mutu acikin wannan addinin. Allah kasa mu cika da kalmar La'ilaha illahu Muhammadun rasulllahi. Tsoron Allah da Soyyayar da kaunar addinin musulumci na dada shiga zuciyarsa.

Wannan kenen.

SOPHIE kuwa bata bar wajen Mr Andy ba har zuwa karfe 11 na dare. Inda Mr Andy ya kafe ya tsare ta da magiya haka babu yadda ta iya ta hakura zata kwana Amma sai da yayi mata alkawarin zai siya mata sabon mota Sannan zai ninka mata kudin da zai bata . Murmushi take har cikin zuciyar ta tana mai jindadi itace da ribar wannan ranar ba shi ba. Haka suka kwana suna badalansu babu abunda ya damesu🤷🏻‍♀️. ( Allah ka shiryemu! Allah ka kare mu daga sharrin zuciya da sharrin zina).

Da gari ya waye ma taso tafiya da safe Amma still ya sake hanata yace Akwai surprise da zai bata. Haka ta yini tana murna.
Misalin karfe 5 na yamma yace su fito surprise nata ya iso. Aiko tsalle tayi kamar an mata albishir da gidan aljannah. Ya riko hannunta tana zuba murmushi har zuwa harabar gidan.
Motace sabuwa dal kirar toyota Mai kalar gold sai zuba sheki take. A wajen plate din motar an rubuta QUEEN SOPHIE. Hohoho su Sophie murna kamar tazuba ruwa a kasa Tasha takeji. Baki ya ki rufuwa. Tab! Motar da ta jima tana da burin hawa  a rayuwarta ko da dani ne? Sai gashi yau gabanta zata haushi a matsayin mallakinta. Maganar Mr Andy ne ya dawo da ita daga hirar zucin da take.
My Queen ! Do you like it?
Murmushi ta saki tana rungumarsa tace Oh my God ! My love, I love it. It's so beautiful. I can't really believe it's mine.
Dariya yayi ya riko hannunta ya kaita wajen boot din motar ya bude. Manyan akwatuna ne guda uku sai wata karamar kit a bayan motar. Yace wannan ma duka nata ne.
Bude su ta farayi. Ya dakatar da ita. Ya kira daya daga cikin ma'aikatan gidan yace su dau akwatun su kai ciki.
Haka suka dau akwatunan su ka kai cikin Falon.
A yayinda Mr Andy ya riko yana murmushi suka bisu zuwa ciki.
Suna shiga ta fara bude Babban akwatin cikin kayan sawa ne kamar su Atampha, Leshi, material, da shadda yar senegal da mali( kasancewar tana mugun sonsu kuma yana karbanta sosai) kowanne hade yake da gyelensa match.
Dayan kuma takalmace,da jakakuna , tularuka da man shafawa da kayan kwalliya. Da yar kuma underwear ce an raba su kashe biyu. Kashi daya normal pant da bra ne masu kyau. Kashi Dayan kuma wa iyazubillahi wasu arnayan bra ne hade da pant nasu set irin wanda turawa ke sawa. Da kuma sleeping dress cotton da slik riga da wando masu kyau sai kuma arnaye lingerie wanda suka fi bra da pants din bayana siyarici idan mutum yasa da ita da babu Duk dayace. Sai kuma kit din wanda a cikinta sarkar gold ce set biyu yar dubai da ta saudia duka full set. Hade da warwaro mai set shida shida a kowace hannu. English white gold daya itama set, sai kuma silver set itama wanda aka mata kwalliya da duwatsun diamond a jikinta.
Kuma kallon kayan tayi . Gaskiya kayan sunyi babu karya . Sai kace lefen aure? Kada Kai tayi tace wannan ai yafi lefe ma. Inama ace tana burin aure da tabbas Mr Andy sai ta musulmatar dashi kuma sai ta aureshi amma sam ita bata da wannan tsarin a rayuwarta.
Shima Mr Andy kallonta yake yana murmushi. Ba karamin dadi yake jiba yau domin yana kaunar yaga SOPHIE tana cikin farinciki barin ma ace wai shine sanadi. Gaskiya wannan abun shi yafi murna Ma fiye da ita.
Inama ace SOPHIE ta zama matarsa da babu abunda bazai iya mata ba aduniya Indai zai sata farin ciki to tabbas zai mata fiye da wannan ma . Amma shima yasan hakan ba mai yuwa bace ba.
Zuwa tayi ta zauna kusa dashi tace My love ! I don't know what to say. I don't know the words to use. I
Don't know what word can exactly express how much I appreciate them. thank you.
I really appreciate it. I love everything and I love you so much. Sai kawai ta fashe da kuka
Share hawayenta yake yana bubuga bayanta yace dont cry My Queen I love you . And I can do anything just to put a smile on  your beautiful face. I can trade my life for you My love! Daga kanta tayi ta dube shi sai ta kuka fashe wa da kuka. Ita kanta tarasa Mesa she is feeling so emotional haka. Me yasata kuka haka ba. Sai de amsar da tabawa kanta shine burinta ne na shekara da shekaru ya cika komai da take so ta samu yau. Dole tayi kuka.
Haka suka sake fada duniyar sabon Allah( inda suke sake jaddada ma junansu soyayyar da suke ma junansu) hmmm Allah ka shiryemu.
Sai dare kafun ta shirya suka fito zai kaita gida a yayinda kuma ya umarci driver ya kai sabon motar tata gida.
A kan hanyar ma hira suke . Mr Andy Duk jikinsa yayi sanyi domin ya so SOPHIE ta bisa. Haka kawai yake jin bazai iya tafiya ya barta ba. Itama a nata bangaran da suka gida kasa sauka tayi a motar ta zuba mai ido tana murmushi tace I will miss you. Kallonta yayi yace Life will be colourless without you. I don't know why but I don't want to leave you here.
Dariyan karfin Hali tayi Dan itama yanzu bata son tafiyar tashi haka kawai ta fara jin kewarsa tun kafun ya tafi. Tace I will wait for you till you come.
Tayi peaking nashi a goshi ta basa deep kiss a baki daya kusan sumar dashi. Sai ta fice da gudu. Tana waiving hannunsa tace bye My love!  Have a pleasant flight.
Kasa Magana yayi ya zuba mata ido kamar yayi kuka har ta shige cikin gidan.
Ya jima anan har driver ya zo ya shiga da motar tata ya tafi kafun ya iya jan motar ya bar wajen.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now