7

115 6 0
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Ina godiya ga masu yin vote da comment . Nagode sosai 🙏 domin vote naku da comment naku na motivating dina sosai wajen cigaba da rubuta wannan labarin mai cike da ilimantarwa da darasin rayuwa.
Karku manta ku cigaba da danna wannan tauraruwar bayan kun karanta wannan shafin.
Shukuran ❤️



Washe gari kamar yadda Hajiya Maryam wato Mama ta tsara MUDDASIR na zuwa bayan ya kammala dukka ayukansa kamar yadda ya saba kullum tasa aka kirasa don su tattauna akan zancen shigarsa makaranta.
MUDDASIR zanso in babu damuwa a kaini wajen mahaifiyarka ina so nasan asalinku kuma na tattauna da ita akan kudirina a saka a makarantar boko.
Dago kansa yayi yace Hajiya Makarantar boko? Nidin ne zan shiga makarantar boko?
Tace tabbas kai kuwa in sha Allah kai nake son sawa a makarantar boko kuma Al-AFIYAH.
Kuma daga kai yayi cikin mamaki da kaduwa .
Yace mene hajiya? Dan kuwa fa gani yace kunnen sa bata jiwo masa daidai ba.
Maimaitawa tayi tace Al- AFIYAH makarantata shi zaka fara zuwa in innarka ta amince.
Mamaki da shock yasa ya sake baki kusan 2 mins bai ce komai ba har sai da kuma cewa MUDDASIR!
Ko baka ji abinda nace ba? Yaushe zaka kaini wajen innar ta ka?
Hajiya am ah wallahi yama rasa me zai ce.
Yace Hajiya Duk lokacin da kika shirya sai na kaiki
wajen innar.
Toh shikenen Sai muje da bayan sallar azahar ko?
Toh Hajiya ba damuwa. Allah ya kaimu.
Nagode sosai Allah ya taimaka.
Allah ya kara lafiya ya kara budi.
Murmushi tayi domin taji Dadin addu'ar tasa.
Ameeeeen MUDDASIR.

Kamar yadda suka tsara Suna Sallar Azahar suka kama hanya har kasan layinsu wajen tsofofin gida.
Suna isa ya sauka ya bude na Hajiya motar yana dari dari yana tsoron kar Hajiya tace baza ya iya shiga idan nasu ba.
Da mamakinsa yaji Hajiya na cewa MUDDASIR shiga ciki ka fada ma innar ka zamu shigo.
Da sauri ya shiga cikin gidan kamar kullum ya samu innarsa a zaune a tsakar gidan akan tabarma tana shan iska.
Assalamu Alaikum
Wa Alaikum salaam
Babana! ka dawo?
Eh Inna da ba kuwa nazo?
Ba kuwa kuma Babana? Inna kasamo bakuwa?
Hajiya ce wadda nake mata aiki . Tana waje itace tace na miki sallama zata shigo.
Mikewa tace Babana Ina fata lafiya ba laifi kai ba ko?
A'ah innah.
Toh je ka shigo da ita. Ta fada tana shiga cikin daki.
Fita yayi sai gashi da Hajiya Maryam Mama tana biye a bayansa.
Assalamu Alaikum
Wa Alaikum salaam Inna ta amsa cikin fargaba tana shifidama Hajiya Maryam Sabuwar Sallayar da a ka bawa MUDDASIR kyautarsa da ya ci gasar Juz Biyar da akayi a makarantar allonsu.
Murmushi Mama tayi tace Mun sameku lafiya tana zama akan sallayar.
Lafiya lau Hajiya . Ya fama da jama'a?
Alhamdulliah!
Inna fata Hajiya Babana ba wani laifi yayi bako?
A'ah MUDDASIR Dan Albarka baiyi laifin komai ba.
Sauke ajiyar zuciya tayi tana sake murmushi. Dan gaskiya ya tsorata da ganin Hajiya Maryam cikin gidansu Duk da tana da kyakyawar shaida akan danta. Tasan shi basada wata karanbani Kuma baya sata bare wata mummunar wata hali. Amma azonta ko ya fasa wani abune cikin kuskure shine aka taho dashi gida.
Tace Alhamdulliah.
Ta sake gaidata ta kawo mata pure water Duk da de har yanzu tana dari dari da tsoro ta ajiye pure water akan plate na roba acikin sanyin jiki.
Hajiya Maryam na lura da yanayinta. Ba tayi niyyar shan ruwan ba asalima basa shan pure water sai ruwan roba Amma Dan Inna ya sake jiki da ita sai ta dauka tayi bismilla ta shanye pure water tas.
Zaro ido innah tayi jikinta ya kuma yin sanyi da har ga Allah itafa kawai ta kawo ruwan ne amma bawai tana zaton Mama zata juya tamasa Kallon arziki bane bare ma har Tasha ruwan . Tab Gaskiya wannan matar ta burge ta bata da girman kai da kyankyamin talaka.
Gyaran murya hajiya Maryam tayi tace daman nazo ne akan batun in babu matsala kuma kin amince zan sa MUDDASIR a makarantar boko.
Wata muguwar bugun zuciya inna taji har sai da ta kai hannunta kan zuciyar tace Hajiya Makarantar BoKo?
MUDDASIR din ne yace yana son kisasa makarantar boko?
Ko daya . Nine de na yaba da hankalinsa da nutsuwarsa da kuma tarbiyarsa komai da ake nema awajen danagari Akwai a tattare da MUDDASIR. Abu daya ya ra shine ilimin boko wanda awannan zamani ita ce zata taimaka masa .
Murmushi tayi tace inna tayi tace Hajiya hakika kin tsosamun inda yake mun kaikayi wallahi naso ace nasa MUDDASIR a makarantar boko amma halin rayuwar da na sinci ci kaina tun bayan rasuwar mahaifinsu yasa ban samu halinda na sashi a makarantar boko ba. Kuma mahaifinsa burinsa a kullum shine 'ya'yansa su samu ilimin boko amma Allah bai sa yayi dogon kwana da zai ciki wannan buri nasa ba. Ta fada tana share hawayen da suka zubo mata.
Innar MUddassir ko zaki iya bani labarin ku in babu ta kura?
Dago kanta tayi ta kafe Hajiya Maryam da ido tayi shiru tsawon minti biyar kamar bazatace komai ba sai tafara.

Labarin Asalinsu Muddasir!

Mu asalin mutanen Gombe ne.
Mahaifin Muddasir Wato Mallam Ibrahim Buba Muddasir wanda ake kira da Ibro Dane ga Alhaji Buba Muddasir da Mama Hanne. Itace matarsa ta farko kasancewar matansa uku. Mama Hanne, Goggo Marka da Inna indo sune matansa. Yaransa Goma sha takwas. Inda guda goma sha shida duka mata ne sai biyu ne kadai maza.
Hajiya Hanne nada yara hudu(4 ), uku duka mata (Sumayya, Aisha, Binta sai autanta shine namiji Ibrahim (ibro)
Goggo Marka yaranta mata ne su guda goma sha daya (11)( Abida, shamsiya, bara'autu, kaltume, fati,iklima,Zulai, badariya,wasila,Yusra da auta faiza. Inna indo ita ma yaranta uku(3) Abdullahi shine danta na farko kusan sa'ani yake da ibrahim Duk da shi ibrahim ya girme sa da wato biyu. Amma shekara daya a haifesu . Sai yan biyu Surayyah da Safiya
Alhaji Buba dattijo ne wanda yasan darajan mutane , kuma tsayyeye a gidansa. Yana masifar kaunar Allah ya basa da namiji. Lokacin da ya auro Mama hanne sai da tayi shekara uku babu maganar ciki babu labarinsa. Hakan yasa ta basa shawara ya karo aure tunda tasan mijin nata mai son haihuwa ne. Baiso hakan ba amma da ya duba yana son haihuwar sai ya amince ya fara neman aure . Anan ne wani abokinsa ya masa tayin kanwarsa wanda mijinta ya rasu wata shida da aurensu wato Goggo Marka. Haka yaje ya gana da ita Duk da gaskiya ya lura ta cika surutu Amma Kawai sai ya basar ya turo aka nai mamasa aurenta. Bayan sati biyu a ka daura aurensu ta tare gidan Alhaji Buba.
Tunda ta shigo gidan taga Mama Hanne sai raina kanta domin tafita da komai Duk da ba ita markan tafita hasken fata sosai amma ita din Mama hanne tana hasken fata irin mai tsadan nan ga ta kyayyawa da gashi baki wuluk. Sannan ga tsafta dakinta kamar a zuba abinci a kasa aci. Komai tana yinsa akan sari sai de bada surutu. Kuma maganar ta acikin sanyi take yinsa. A wajen girki ma ta fita bana wasa ba babu kalar abincin gargagiyarda bata iya girkawa ba.
Kuma ta lura Alhaji buba yana sonta sosai kawai rashin haihuwarta ce kawai masalanta.
Ina ita kuma Goggo Marka ta dau alwashin kar katoda soyayyar Alhaji buba gare. Tacika gidan da yara. Ta fitar da Mama Hanne Gidan ya zama nata da yaranta kawai.
Wannan kenen.
Ana cikin haka bayan wata shida. Goggo ta tashi da ciwon ciki da amai da zazzabi mai zafi. Haka Mama Hanne ta taimaka mata ta bata abinci taci. Alhaji buba ya kaita asibiti. Kwajin farko aka shade musu tana da shigar ciki har na wata biyu.
Murna a wajen Alhaji Buba kamar yayi rawa. A yayinda Goggo Marka take hango yadda zata haife wannan ta kuma dau wani cikin har sai ta cika gidan taf da yara. Ta kore Mama Hanne.( hmmm)
Haka suka dawo gida cike da murna Kai tsaye wajen Mama Hanne ya wuce ya shaida mata. Bakaramin murna tayi ba taji dadi sosai ta taya su murna ba kadan ba. Har sai da Alhaji Buba yayi nadamar kasa boye farincikinsa ya fada mata gashi tana murna Duk da yasan ta boye bakin cikinta na rashin samun haihuwar tana tayasu murna sosai. Sai Duk jikinsa yayi sanyi ya mike ya shige dakinsa ya kulle kansa.
Shiru shiru bai fito ba ta sai ta bisa dakin . Taba kofar tayi sai ta jita a kulle.
Kwankwasawa tayi tace Alhaji lafiya ?
Tashi yayi ya bude mata kofar ya koma ya kwanta a kan gadon ya juya mata baya.
Takowa tayi ta zauna gabansa tace Alhaji lafiya?
Muna cikin murna sai ka shige ciki na zata zaka fito sai na jika shiru.
Dago idonsa da suka rine suka koma ja yayi ya kafe ta da kallo Mika mata hannu yayi alamar tazo .tana zuwa ya Janyota jikinsa yace kiyi hakuri Hanne. Dan Allah ki yafe mun.
Alhaji ni ba Kamun komai ba. Me ya faru?
Kiyi hakuri! Na kasa boye farin cikina Duk da nasan kema kina son haihuwar. Kuma da so samune da zanso ki fara haifa mun 'ya'ya . Yakare yana mai karya wuya.
Murmushin karfin hali tayi tace Alhaji kenan.
Ai Duk abunda ya sameka ya sameni. Farin cikinka shine nawa.
Wannan Duk ci gabanmu ne baki daya.
'Ya'yanka tamkar 'ya'yana ne. Ko zakamun rowar yara ne ta fada tana sakin dariya. Dariya shima yayi yana jan hancinta!
Kuma Alhaji Haihuwa na Allah ce . In har Ina da rabon ganin nawa Dan in lokacin ta yayi sai Kaga na haifa nawa nima.Ta fada a yayinda hawayen da take tattalin kar su zubo suka fara zuba. Sauri tayi ta goge mu tana murmushi. Rungumarta yayi yace karki damu. Allah ya miki Albarka. Duk runtsi ina tare dake. Bazan barki ba. Kuma in sha Allah watarana zaki ga jininki.
Murmushi ta sake tana mai jindadin adduar da ya mata tace Ameeen ya Allah.
Ta bangaran Goggo Marka kuma haushi kamar ta mutu. Murnar da Mama Hanne ta nuna ba karamin bakan tamata rai yayi ba. Taso ace Mama Hanne ta nuna bakin ciki ta tada hankalinta ta da hankalin Alhaji tamasa rashin mutunci Amma sai taga akasin haka.
Ga yadda kuma shi uban gayyan maimakon yazo wajen ta Kawai sai ya wani wuce wajan matarsa. Wannan abun ya mata ciwo kuma tayi alkawarin ko tahalin kaka sai ta shiga tsakaninsu. Dan tsaban iskanci ita zasu nunawa soyayyah? Yan iska sun manta sune Layla da Majnun. Sakaran banza haka tayi ta mita tana zuba masifa har lokacin da Alhaji Buba ya bar dakin Hanne fuska a daure ta dauka ma fada sukai . Kawai sai tafara murna. Sai taga Hanne ta biyo sa. Ji tayi kamar ta fito ta mata Dan banzan duka.
Haka ta lallaba Duk da bata jin karfin jikinta ta labe a jikin kofar dakin tana sauraran maganarsu. Idan ranta sunkai dubu to tabbas dukka sun bace. Zuciyarta kamar ta faso kirginta ta fado take ji dan bakin ciki da takaici. Kishin Mama Hanne da tsanar ta take ji fiye da komai a duniya. Tajima tana tsaye a kofan dakin daga karshe ta sake wani shu'umar murmushi tabar wajen ta koma dakinta.
Muje zuwa.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن