15

87 2 0
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Dadina dake SAFFIYAH wallahi har yanzu yaranta bata barki ba ke kullum komai a fadawa Abbah.

Eh lallai ba shakka FAIZA! in banda kin raina ni nice ma yaranta ke damu na ko? To tabbas yau zangen nan kamar ta kwana kunnensu yaya.

Dan Girman Allah karku fara.
Dadina daku kenen da an zauna da ku shike nan sai ku fara wannan iskancin nan naku. Wai ku ko kunya bakwa ji kuna yan uwa amma ace kamar Tom and Jerry sai fada? Gaskiya duk kanku baku san ciwon kanku ba har yanzu.

Bara ma na tashi naje nayi karatuna ya fiye mun zama da jin shirmenku.

Lallai mah SURRAYAH mu din ne bamu san ciwon kan mu ba?

Kya ji dashi ke deh kullum karatu kamar a kanki aka fara karatu yar wahala. FAIZA ta fada tana kwashewa da dariya.

Amma kuma tafi kwalliyar asara da karatun littafin banza SURRAYAH tafada tana zabga musu harara da murkuda masu baki.

Kwashewa sukai gaba daya da dariya

Kinga bakinki kuwa? Kamar anawa biri kiss 😂😂😂
FAIZA duba mun Kode idona ne?

Dariya FAIZA tayi tace SAFFIYAH idonki lafiyansu lau.
Wai fa ahaka bakin ta murguda Manah😂😂
Gaaskiya SURRAYAH mijinki yaga takansa .

Sake kwashewa da dariyah sukai har da tafawa.
Dan girman Allah ki kumayi mugani 😂

Hmm! SAFFIYAH da FAIZA kenen.
Allah ya shiryeku.

Ameen suka amsa gaba daya.

******************************

Da yamma ABDALLAH da IBRAHIM suna zaune kofar gida wata mota tazo ta tsaya agabansu ganin  basu gane mai motar ba sai suka kura mata ido har zuwa lokacin da matukin motar ya bude kofar ya zagaya ya bude kofar bayan.
Kara bada hankalinsu sukai dan suga wanda zai fito daga motar.

Wata matace da shekarata bazasu haura sama da shekaru Talatin da biyar ba, tana da madaidaicin tsayi , bata da kiba sosai , tana da kyau sosai , farace sosai Amma harda na mai sai de mai din irin mai gyara jikin ne ba me batawa ba, ma'abociyar murmushice  Dan tunda ta fito take sake murmushi da fara'a, gwanar adoce kamar dawisu, tafiyarta ma abun kallo ce.

Takowa tayi a hankali kamar mai tausayawa kasar da take takawa har ta iso gabansu.

Assalamu Alaikum
Wa'alykum Salaam suka amsa mata a tare.

Dan Allah nan ne gidan Alhaji Buba?
Eh nan ne suka amsa mata atare.
Inna tana nan?
Eh tana cike.
Masha Allah tace
Toh in bazaku damu ba ku mun iso cikin gidan manah?

Toh suka Mike atare suka nufi cikin gidan da salama
Tana biye dasu har zuwa bangaren inna.
Suna shiga sukace INNA kinyi bakuwa fa.
Bakuwa kuma yarannan ?
Tana fitowa sai taja ta tsaya abakin dakin.
Wa nake gani haka kamar ASIYAH?

Murmushi mai hade da dariya wannan bakuwar da inna ta kira da ASIYAH ma'abociyar murmushi ta sake tace INNA nice nan wallahi.

Salati ta rafka tana tafa hannu!
Fadi take oh ni AISHATU ! 
Wai da gaske ASIYAH ce?  ke ce a tafe? Yaushe a gari? Taho mushiga daki ta kama hannunta zuwa cikin daki ta zaunar da ita a kan gado.

Ban taba zata zan kara ganinki ba
Sai gashi yau kiinzo gareni a lokacin da na fara fidda ran sake ganinki.

Innata! Kinsan bazan taba mantawa dake ba.
Naso zuwa gareki da jimawa.
Amma duk lokacin da na tuna rashin mutumcin da su yaya suka mun sai na fasa zuwa.
Amma gashi yau Allah ya kawo ni.

******

ASIYAH 'ya ce ga Mallam Audu , babban yayansu INNA AISHA wanda rasu shekaru biyar da suka wuce. Tana auren wani bayerabe can a Lagos da danta daya mai suna ABDULSAMAD. 

Ta shaku sosai da INNO AISHA  sosai. Duk cikin yan uwar mahaifinta tafisonta Kamar itace  ta haife ta da yake mahaifiyarta ta rasu tun tana da shekara bakwai a duniya.

Tun lokacin da tayi aure bata kara zuwa ba sai kuma rasuwar mahaifinta kasancewar duk sauran yan uwanta basa kaunar aurenta da bayerabe a matsayinsu na fulani.

Shima a lokacin rasuwar sai da yan uba suka mata rashin mutumci da ita da mijinta suka koresu akan su basa son bare cikinsu. Haka ta bar garin tana kuka cike da bakin cikin abun da yan uwanta suka mata da kuma maraicin mahaifinta da tayi. Tun daga wannan lokacin kuma bata kara waiwayar garin ba sai yau da tazo wajen innarta.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Feb 27, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now