14

103 8 9
                                    


Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Toh haka rayuwa taci gaba da tafiya a cikin gidan Alhaji Buba daga kwanaki zuwa makonni, watanni har zuwa shekaru yara Duk sun girma.

Hudu 4 daga cikin yaran Goggo Marka har an fara zancen za'a musu aure saboda yawan samari ke zuwa musu zance kofar gida.

Goggo Marka dadi take ji yaranta akwai farin jini sosai shiko Alhaji Buba baya son yadda aka mayar masa kofar gida kamar titi samari kala kala Dan haka yace ko wacce daga cikinsu ta fidda gwani a cikin samarin ta ya turo magabatansa asan abinyi Dan sam bazai lamanci wannan dabi'arba.

Ita de ABIDA babbar yarsu KAMALU dan autan ADDA ABIDA zata aura Dan Kasuwa ne yana zuwa Lagos ya saro kayan yara da takalmar yara ya siyar yana da babban shago acikin kasuwa.

SHAMSIYA kuma IDRISA zata aura shi malaminsu na islamiya zata aura.

BARA'ATU zata auri USMAN shima Dan kasuwa ne yana siyarda kayan abinci yana da shago acikin anguwa.

KALTUME kuma ISA zata aura zaria za'a kaita domin acan yake aikin gwamnati.

FATI zata auri YUSUF Dan Maiduguri ne can zata zauna yazo bautan kasa makarantarsu suka hadu suka fara soyayya har takai yanzu zasuyi aure banker ne shi ne kuma a can Gt bank Maiduguri branch yake aiki.

Biki yazo akayi al'adu da shagalguna na gani na fada an kai kowacce amarya dakin mijinta.

Sai fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuriar dayyibba.

Haka rayuwa tayi ta tafiya a yayinda ABDULLAH da IBRAHIM ke shiri sosai.

Akwai soyaayya, kauna da shakuwa na ban mamaki sakaninsu.

Komai daya ya samu to nasu ne duka.

Kullum suna tare. Ko ina tare suke tafiya. Haka makarantar boko da ta islamia duk tare suke tafiya ajinsu daya wajan zamansu daya.
Dukkansu akwai kokari da sa kai a karatu.

Sam basa wasa da karatunsu. Yanzu haka suna shirin yin sauka a islamia a yayinda suke SS2 a makarantar boko.

A yayinda ABDULLAH yake Science class shi kuma IBRAHIM yake Art class,  dayake suna da burin shiga jami'a bayan sun kamala secondary.

Shi ABDULLAH Architect yake so ya zama. Yayinda IBRAHIM yake so ya zama Lawyer.

Duk cikin yan uwansa mata IBRAHIM yana matukar kaunar yan biyu wato SAFIYA da SURARRYA.

Amma sunfi shakuwa da SURARRYA da yake tasu tazo daya itama tana da son karatu sosai sannan bata cika surutu ba gata da hakuri.

A yayinda SAFIYYA take akasin haka domin ita akwai surutu sosai sannan tana da son yawo da fada.

Ba'a mata ta kyalle duk da tana da ilimi sosai daya ke she is just gifted ne amma bata son karatu. 

Kawai Allah ya taimaka mata tana daukan takadda last minute take haddaceshi kuma cikin ikon Allah ita take Zuwa 1st a class nasu a yayinda SURRAYYA take zuwa na biyu.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now