12

77 4 4
                                    




Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Haka rayuwa tayi ta tafiya har Cikin Mama Hanne ya isa haihuwa ta haihu. Wannan Karan ta haifi danta namiji .
Wohoho zo kuga farin ciki daga wajen Alhaji Buba baka dan ba. Dan daman yana son da namiji dayake Allah bai basa ba sai bai nuna wata damuwa ba. Yayi godiya da wanda ya basa. Kuma daman shi yafi son Mama Hanne ta fara haifo masa da namiji kafin sauran Allah cikin ikonsa ya amsa masa adduarsa ya cika masa wannan buri.
Yan uwansa ma sunyi farin ciki sosai sai de dukka jikinsu yayi sanyi ba kadan ba. Kunyar duniya ya kamasu. Duk abun da suka mata yasa ko barka da sukaje sun kasa sakewa. Ranar suna aka sakawa yaro suna IBRAHIM.
Yinin sunan ADDA ABIDA kanta akasa ta kasa hada ido da Mama Hanne bare danginta. Su ko basu nuna musu komai ba. A mutumce suka karbe su yadda suka saba. Kunya ya kara kamasu da danasanin abun da sukayi mata Dan sunyi mamakin yadda aka karbe mu da karramawa sun sani da yau Goggo Marka ce sai sunsha Bakaken maganganu da cikin fiska sai gashi an karbe mu kamar babu abunda ya baru.
Yamma nayi sun hada kansu zasu tafi sukaje suka samu Mama Hanne da danginta suka nemi yafiyarsu da basu hakuri akan abubuwan da ya faru.
Wata innar Mama Hanne tace musu su basu rike su a zuciya ba. Komai ya wuce. Haihuwa ta Allah ce shi yake bawa wanda ya so kuma wanda bai samu ba ba yin kansa bane shima Allah na sonsa. Sannan mace ko namiji shima Allah ke bayarwa. Mutum de yayi fatan Allah ya azurtasa da yara masu albarka nagari.
Ta musu wa'azi da nasiha sosai akan rayuwa.
Haka aka watse kowa jikinsa yayi sanyi.
Rayuwa kenen.

Haka rayuwa yaci gaba yau da gobe bata bar komai ba. Yanzu Goggo Marka ta sauko tana zaman lafiya da Mama Hanne sakaninta da Inna indo kuma kowa na harkar gabansa babu mai shiga tsabgan wani.
Ana haka har lokacin haihuwar inna indo yayi ta haihu danta namiji ranar suna aka saka masa suna ABDALLAH. Kowa ya nuna murnarsa sosai. Amma wannan karan babu habaici domin yanzu ansamu abunda akeso kuma duk jikinsu yayi sanyi da lamarin duniya tun haihuwar IBRAHIM.
Goggo Marka taji zafin haihuwar nan sosai. Amma batace komai ba. Haka take shiga bandaki tasha kuka ta share hawayenta. Tana adduar itama Allah ya bata da namiji a haihuwar gaba.

Manage this.
I am a bid busy.
Thank you for the votes and comments.
❤️❤️❤️❤️

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now