11

83 6 3
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Akwana a tashi asarar mai rai cikin Goggo Marka ya shiga watar haihuwa ta haiho yarta aka saka mata suna BARA'ATU . Wannan haihuwa yadan bata ran wasu daga dangin Alhaji Buba Dan kuwa Duk yawanci tsammaninsu namiji zata haiho sai sukaga akasin haka. Wasu sun fara kananun maganganu duk da manyan basu dauke sa da muhimmanci sosai ba acewarsu wasu mata sai sunhaifo mata biyar kafun suke fara haifan maza babu tsayawa har haihuwa ta tsaya musu. Da wannan bayanin aka tsayar da kananun maganar. Goggo Marka ma de ita ma a son ranta taso ace namiji ta haifa Dan har ta siya kayan maza ta ajiye.😂😂 Dan duka lissafin ta namiji zata haifa.
Allah ya kyauta.

BARA'ATU nada shekara 2 ta kuma samun ciki ta haihu yarta mace aka saka mata suna KALTUME, tana yaye ta tasamu wani cikin ta haifi FATI sai Kuma IKLIMA.
Dangin Alhaji Buba yanzu lamarin ya fara isansu. Dan sun fara gajiya da haihuwa yara mata da take yi. Yanzu sam sun dena wani marmarinta. Duk wani kauna da girmamawa dasuka nuna mata sun fara jan baya da ita.
Manyan ma sun fara korafi. Hmmm rayuwa kenen fa. Bani adama abun tsoro abun mamaki. Kamar fa ba ita suka fifita da farko ba Amma yanzu Duk sun chanza sun manta da komai tsaban son zuciya.
Ana cikin haka sai kwatsam Mama Hanne ta samu ciki lokacin haihuwa yayi ta haifo yarta mace aka saka mata SUMAYYYA, Goggo Marka ma ta haifi ZULAI.
Kamar hadin baki sai suka sake samun ciki tare Mama Hanne ta haifi AISHA . Goggo Marka ta haifi BADARIYYA.
Dangin Alhaji Buba abun duniya ya ishesu. Suka rasa wani irin haihuwace wannan na yara mata ne da matan dan uwansu suke. Daga nan aka shiga zuga ADDA ABIDA babbar yayarsu akan gaskiya ya kamata tasa ALHAJI BUBA ya karo aure.
Bayan AISHA da BADARIYYA sunyi wayo Goggo Marka da Mama Hanne duk suka dau ciki.
Lokacin haihuwa suka kuma haifo yaransu mata aka saka musu BINTA da WASILA.
To de wannan haihu ba karamin bata ran ADDA ABIDA yayi ba kuma daman gashi tasha zigi da ga wajen dangi, kawaye da shedan.
Hmmm ranar yinin wannan suna anyi tashin hankali da rashin mutumci tsakanin dangin Goggo Marka da dangin Alhaji Buba. Dangin Mama hanne kuma duk da abun ya musu zafi sosai ba kadan ba sai suka ja gefe suka zama yan kallo.
Anyi zage zage, dambe, cizo da tofin ala tsine tsakanin Dangin Goggo Marka da Alhaji Buba kamar basu ne suka hadu suna zuba ma Mama Hanne habaiciba da gori ranar da ta fara haihuwa ba. Kamar basune suke girmama taba. Kamar ba itace wannan da suke kirada matar so ba mai haihuwa ba.Sai gashi yau ana jinkansu. Sun fito fili sun nuna mata iyakarta.Duniya!duniya !!hmmm. In kika ga ana ciya kishiyarki mutumci ana wani nuna miki so Toh wallahi kar ki biye musu kice zaki raina kishiyarki ko musguna mata. Su dangi miji ba'a hada kai dasu aci mutumcin kishiya. Yau suna ta taki gobe ajiye ki zasuyi suyi maraba da wata babu ruwansu. Dan haka ki rike mutumcinki kowa ya tsaya matasyinsa. Ki kyautata musu amma ki iya bakinki da takonki da kinga ana kawo miki kananan magana karki bada wata kofa munafurci. Babu ruwan ki.
Allah ya kyauta. Ameen.
Ana cikin haka maza sukaji labari suka shigo to anan ne ADDA ABIDA tace wallahi ta bawa AlHAJI BUBA sati biyu ya kara aure idan ba haka ba to ya nemi wata yar uwar amma ba ita ba.
Haka yace ya amince kafun suka tattara nasu inasu suka bar gidan.
Bayan sati hudu ya auro Inna Indo. Goggo Marka babu abun da ta sana a duniya kamar Inna indo dan yanzu bata kishi da Mama Hanne sai ita.
Dukka de Inna indo bata kaisu girma ba amma tana da wayo sosai, hakuri da kuma iya zama da mutane. Da fari taso su zauna lafiya da kowa amma da taga yadda Goggo Marka ke nuna mata tsana a fili zai ta kama kanta duk hakurin ana mata rashin mutumci zata rama. Suna zaman lafiya da mutumta juna tsakanin ta da Mama Hanne. In ka gansu bazaka ce kishiyoyi ba sai de ya da kanwa. Wannan shirin nasu ya sake bakan ta ran Goggo Marka.
Ana haka da wata takwas sai Mama Hanne tasa mu ciki haka itama Goggo Marka haka rayuwa ya ke tafiya a gidan Alhaji Buba. Dangin Alhaji Buba sai sintiri suke zuwa gidan suga ko Inna Indo tasamu ciki lokacin da suka ji labarin shigar cikinsu Mama Hanne da Goggo marka amma shiru. Sai da cikin Mama Hanne yakai wata biyu . Goggo Marka kuma hudu kafun inna indo ta samu ciki.
Murna agun dangin Alhaji Buba ba'a magana. Danfa ADDA ABIDA har girki take aiko mata. Da rubutu dan ta haifo namiji.
Ana haka Goggo Marka ta haifi yarta aka saka mata suna YUSRA. Dayawa daga dangin sa basu zo ba. Wanda suka zo kuma bakaken Magana suka fada mata suka wuce dakin Inna indo suna cewa kwanan nan za'a haifo musu da namiji a gidan nan.
Wannan abun ya mata ciwo sai ya tuna mata da rashin mutumcin da tayi wa Mama Hanne. Ashe daman haka gori yake? Ashe ita ma za'a mata. Lalle wannan hakki ne. Hakkin Mama hanne ne. Tayi dana sani baka Dan ba. Gaskiya wannan shine ake cewa sharri Dan aikene zai dawo maka. Sannan abun da kama wani tabbas kaima za'a maka. Shiru tayi batace musu komai ba.
Bayan anyi suna an watse a daren Goggo Marka ta samu Mama Hanne har cikin dakinta akan ta yafe mata abubuwan da ta mata sharrin zuciya ce da ta shedan.
A nan Mama Hanne ke nuna mata komai ya wuce. Kuma ta yafe mata da jimawa. Duniyar ma nawa take. Ta kara mata da tayi hakuri. Dan lamarin duniya sai hakuri watarana sai labari.
Godiya ta mata sosai. Ta koma dakinta ta ci gaba da jego.

Wannan kenen.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now