8

98 6 2
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.
Not edited🚫

Shukuran !!
Godiya mai tarin yawa 👏👏👏👏 ga mabiya wannan littafin mai suna " KOMAI DAGA ALLAH NE"
Karku manta ku latsa wannan tauraron bayan kun kammala karanta wannan page.
One love ❤️ 😘.

💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Tun daga ranar Mama Hanne ta dauke duk wanne aikin wahala da Goggo Marka takeyi agidan. Ita take mata komai daga abinci, wanki da gyaran daki. Tsakani da Allah take kula da ita. Goggo Marka kuma taso yima Hanne iskanci Amma azabar laulayi tasa ta yin sanyi ta hakura har sai ta warke Amma ba wai ta fasa bane. Duk kyautatawar da Mama Hanne ke mata bata gani akullum burin ta ta warke ta fara zuba rashin mutunci a gidan. Alhaji Buba ya sha Hana Mama Hanne wasu aikace aikacen Amma tace ai Duk yiwa kaine.shi kuma ganin gaskiya kamar Aikin bauta take wa Goggo Marka ya sashi zuwa gidansu ya dauko kanwarsa wanda aurenta ya mutu tana zaman zawarci babu miji wato yahanasu. Tunda yahanasu tazo taga aikin bautar da Mama Hanne keyiwa Goggo Marka ta hanata tace wallahi gwara ita tayi hidima azaman kanwar miji Amma wallahi Mama Hanne bata isa ta bautawa kishi ba har dasu gyaran gado? Tabdi!
Zuwan Yahanasu gidan yasa Goggo Marka fara yin wasu aikace aikacen da kanta. Dan Mama Hanne in tace zata gyara ma Goggo Marka daki sai Yahanasu tace ita zatayi. Haka zata dau tsintsiya ta shige cikin dakin Goggo Marka da sunan shara. Tana shiga zata buga kafar Goggo Marka tace maza kitashi ki gyara dakinki kinsani Sarai ni bana daukan raini. Niba yaya Hanne bane wallahi karki ga kina dauke da cikin yaya buba wallahi tsab zan wawwanke wannan fuskar ta ki mai kamar yalo da maruka. Babu abunda ya dameni.
Haka zata miki ta fara gyaran dakin. Tas take sata ta gyara dakin tasa tularen tsinke. Sannan tace mata su masu ciki Manya . Toh Marka kishiga hankalinki banson iskanci da diban albarka. Ke ban dama daqiqiya bace ke mai kwakwalwar tolo tolo taya zaki dauki wanki ki bawa kishiya tana wanke miki har pant. Kan uban nan na rantse da Allah kika kuma daukan kayanki kika bawa yaya Hanne da sunar wanki sai jikinki ya gaya miki. Shashasha wanda bata San ciwon kanta ba.
Haka Goggo Marka zata sunkuyar da kanta Dan tasan ba wasa Yahanasu take ba tsab zata aikata wallahi. Bata da mutunci bata daukan raini ko kadan. Akan haka ne ma aurenta ya mutu. Inda uwar miji da kannensa uku suka sata gaba. Kullum zagi da cin mutunci suke mata har cikin gida uwarsu take aiko su mata rashin mutunci da fari bata Magana. Amma da suka Kai ta bango tsab ta cire bulala ta musu shegen duka. Da uwar mijinta tazo suka hadu suka mata duka suka faffasa mata kayan kallonta. Itako da tashi ta hau kan uwar mijin nata sai ta mata cizo mai zafi a wuya har sai da ya kawo jini🙆🏻‍♀️.Inda uwar mijin tasa yaron ta kan dole ya saketa Dan mayya ce jininta take son sha🤣.
Tun daga wannan ranar Goggo Marka ta fara aikinta babu mai tayata. Har cikinta Yakai wata tara inda yar uwarta Baraka ta dawo gidan da zama. Itama Baraka Akwai masifa da rashin kunya ta fadawa mutum bakaken maganganu ba abu mai wuya bane a gunta.
Tunda Baraka ta dawo gidan sai ya zama ita ta keyin komai Ma yayarta. Haushin Yahanasu take ba kadan ba. Gashi ta tsani Mama Hanne kamar itace Kishiyarta.
Sai ta fara iskancin Duk ranar girkin Mama Hanne sai Ta zuba lemon tsami , ko gishiri mai yawa, ko yaji, ko kalanzir acikin miyar Alhajibuba. Toh da fari baya Magana Amma daga baya dayaga abun ya fara wuce gona da iri sai ya fara gorafi. Abun ya basu mamaki sosai domin su abuncinsu babu abunda ya same sa. Lafiya lau yake. Haka de har yahanasu watarana ta dandanasa taji tsami da uban gishiri. Shiru tayi tana Dan nazari. Taje ta kuma girka wani ta kawo masa. Abun ya daure musu kai sosai. Amma sai Yahanasu ta bari ranar girkin Mama Hanne ya kuma zagayo wa , sai ta labe bayan magariba a cikin kitchen bayan an gama raba abinci babu kowa Duk an tafi Sallah . Sai ga Baraka ta shigo da kalanzir ta zuba a cikin miyar sai ta dauko uban barkano da gishiri ta zuba. Tasa cokali ta juya sosai ta goge ko ina ta gyara tsab kamar yadda  ta sameshi ta mike ta fice. Kan uba !😡Yahanasu tace . Sauri tayi ta fito ta chanja abincin zuwa wata kwano ta wanke kwanon nasa ta juye abincinsu baraka da goggo Marka cikin kwanon Alhaji Buba. Sai ta zuba mai kalanzir din zuwa nasu. Murmushi tayi tace zakuci ubanku. Wannan wasan tare zamuyita yan iska. Muzuba nida ku.
Haka aka rarraba kowa aka basa abincinsa.
Hmmm Baraka da Goggo Marka suna fara cin nasu suka tofar. Suka kalli juna cikin tsoro kalanzir?
Keh Baraka ya akai haka?
Shine kika juye manah kalanzir yau cikin namu girkin? Hala so kike yau yunwa ta kashe ni?
Wallahi yaya Kamar yadda na saba Duk Ran girkin Hanne a nasa na zuba yau ma. Bansan ya akai haka ta kasance ba.
Kedai yau kin cuceni . Kin jamun kwana da yunwa.
Haka tayi ta mita har gari ya waye.
Washe garima kuwa haka abun ya kasance musu abincin da Baraka ta zabga uban gishiri shi suka ci. Goggo Marka Kamar ta rufe ta da duka Dan haushi.
Wasa wasa sai da akai sati ana musanya musu abincinsu da ta Alhaji buba dake yanzu Hanne ke girki kullum ga kuma Yahanasu na taya ta saboda Goggo Marka ta kusa haihuwa. Kuma  dake babu Allah a ransu Baraka da Goggo Marka basu fasa lalata abincin Alhaji Buba ba dukda yanzu abincin a kwanonsu yake karewa.
A rana ta bakwai ne baraka ta kawo abinci mai kalanzir da barkono sun saka abincin agama suna mamakin wannan al'amari Dan Duk cikin gidan babu wanda ya nuna musu alamu yan San abunda sukeyi. Amma kuma kullum sai an musanya musu abincin!
Yaya Marka anya ba mutanen boye ke musanya mana abinci ba ?
Keh Baraka wallahi kamar kin shiga raina Dan fa wannan abun ya daure mun kai.
Ni tsoro na Ma kar su tona manah asiri watarana.
Tona asiri? Ai asirinku ya dade da tonuwa sukaji an fada daga bakin kofa!
Turus sukayi ganin Yahanasu tsaye bakin kofar tana murmushi. Duk wanda yasan yahanasu yasan ma'anar wannan murmushin.
zara ido sukayi suna kallon juna.
Ku da a tunaninku duk tsiyar da kuke tafkawa a cikin gidan nan ban sani ba?
Ah lalle! na zuba muku ido ne naga gudun ruwanku .Na dauka zaku hakura da mummunan kudurinku tunda duk jagogwalon da kuke zubawa jikin abincin Yaya Buba tana karewa a cikin kwanonku. Amma dake rubabbun kwakwalwa gareku sai kuka cigaba ko?
Toh yau ba gobe ba zan fadawa yaya Buba kuma tsab zaku bar gidan nan. Marka kina cemin bazawara ko? Yau zaki kuma dandanon zawarci Kuma da ciki. Tana fada ta juya zata fice a dakin.
Ai da sittin suka rikota. Sai ga Goggo Marka durkushe da katon ciki tana rokan Yahanasu Allah da Annabi ta rufa musu asiri. Wallahi sharrin zuciyace da ta shaidan.
Murmushi tayi tace. Zan hakura na rufa muku Amma da sharadi biyu. In kun kiyaye wannan sharadi Toh babu mai jin wannan iskancin naku.
Wallahi Duk abunda kika ce . Duk zamuyi in de zaki rufa manah asiri.
Kun tabbata?
Eh .
Toh ! Na farko yau ya zama rana na karshe da zaku sake maimaita kalar wannan gangancin a cikin gidan nan.
Wallahi har duniya ta nade bazamu karaba. Goggo Marka tace.
Na biyu sai tayi murmushin😊😊Ku cinye wancan abincin yanzu Ina kallonku.
Kallon juna sukayi cikin tsoro .
Haba Yahanasu kema fa kinsan ko kare bazai iya cin wannan abincin ba. Taya zaki ce muci? Baraka ta fada tana fura hanci.
Oh ashe da saninku ko kare bazai iya ci ba? Shine kuke so yaya Buba yaci ko?
Toh Wallahi idan baku ci wannan abincin ba na rantse da Allah yau sai kun bar gidan nan kuma yanzu ba gobe ba. Zan fada yaya kaf iskancin da Duk wata kullin da kuke a cikin gidan nan . Kuma sai na fada masa wancan agogon da aka sace kwanakin baya Baraka ke kika sace kika siyar.
Wani zaro ido😳 Baraka tayi ta daura hannu akanta 🙆🏻‍♀️tace na shiga uku ni Barakatu😭 sai ta fashe da kuka.
Tace yaya Marka ki cece ni.
Murmushi tayi tace  ta cece ki? Ta ceceki fa kika ce. Hmmm lalle Toh ke kuma Marka zan fadawa yaya Buba kece nan kika dauke Sabon Radion da ya manta a kofar gida kika bawa idi mai shago ya ajiye miki. Kaninki yazo ya karba ya siyar ya aiko miki kudi. Ko Duk ba'ayi haka ba? Ta fada tana sake shu'umin murmushi😊😁.
Kai !!kuma wasa dani baku San wacece Yahanasu ba har yanzu. Babu abunda ban sani ba. Kukai wasa sai na tona Duk wata sirrin ku a cikin gidan nan.
Shiru sukayi Dan kunya Duk sun sunkuyar da kai sun kasa cewa komai.
Toh nide yanzu na wuce wajen yaya Buba bada rahoto 📣📣📣🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️🚶🏻‍♀️😁 ta fada tana kokarin fita daga dakin.
Ai da gudu suka bita suna rokanta ta rufa musu asiri.
Na fada muku in de kuna son na rufe zancen nan to ku koma dakin nan ku cinye tsiyarku.
Da gudu suka zauna gaban abincin wanda yake tuwoce da miyar yauki da nama manya Amma barkono da kalanzir Duk ta chanza mata dandano.
Gutsirawa baraka tayi tana kai loma bakinta taji barkono da kalanzir . Ta bude baki da niyar tofar dashi taji Yahanasu tace Wallahi ki ka kuskura ki ka tofar ko ki ammar. sai na saki cin wanda kika tofar kuma ki lashe wanda kika amar. Ehee 🤷🏻‍♀️😏😏.
Babu yadda ta iya haka ta Hadiye abincin kut hawaye na zuba daga idonta.😭
A bangaren Marka ma gumi take share wa. Ga yunwa, ga ciwon da maranta ke mata, ga nauyin jiki ga kuma abincin me shegen barkono da kalanzir. Ci take tana share hawaye😭😭😭😭😭 da majina 🤧🤧.
Nadama iya nadamar wannan shawaran lalata abincin Alhaji buba sukayi ba kadan ba.  Ga wata tsana da tsoron Yahanasu da ta cika musu zuciya.
Sun mata Allah ya isa ya fiso million cikin zuciyarsu.
Baraka kam addua take Allah yasa Yahanasu ta mutu.
Kuma Wallahi sai ta rama wannan bakar azabar da Yahanasu ta dandana mata yau ko bayan shekara dari ce.
Haka suka cinye abincin tas.
Amma Duk sun fita a hayyacinsu. Domin Yahanasu ta hanasu shan ruwa.
Haka tace ma Baraka ta dauke kwanon taje ta wanke ta ajiye ta dawo.
Mikewa baraka tayi kanta Duk yana juyawa ta fice da kwanon , ta wanke ta dawo.
Goggo Marka kam Dan azaban da take ci ko Magana ta kasa. Hannu ta daura akan kugunta tana kallon kasa hawaye 😭😭😭yana ambaliya a fuskarta. Azaba iya azaba ta shashi.

Kadan kuka gani daga aikin Yahanasu! Ina nan da nidaku a cikin gidan nan shege ka fasa. Ta fada tana ficewa daga dakin.

Muguwa!
Yar iska!
Shegiya!
Mai bakar zuciya!
Mayya!
Wallahi yaya Marka dagaske yau na yadda yahanasu mayya ce babu Allah a cikin zuciyar ta.
Ta fada tana share hawaye 😭da suka zubo mata .

Dago kai Marka tayi tace Baraka kawo mun ruwa. Ina ga mutuwa zanyi.
Haka baraka ta fita kawo ma yayarta Marka ruwa.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now