13

81 3 0
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Haka rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Alhaji Buba har Goggo Marka ta kuma samun ciki tsammaninta dukka da namiji zata haifa sai Allah cikin ikonsa ya kuma azurta ta da haihuwar ya mace ran suna aka saka mata suna FAIZA. Wannan abun ya kuma damunta tayi kuka sosai haka Mama Hanne da yan uwanta suka ringa rarrashinta suna tuna mata ta godewa Allah da azurtata da haihuwar 'ya'ya mata domin wasu hakan ma basu samu ba. Kuma 'ya'ya mata ai rahama ce . Akwai tarin baiwa da ni'ima tare da haihuwarsu. Tayi fatan Allah ya raya mata su yasa albarka cikin rayuwarsu sai taga sunfi yara mazan ma. Da haka ta samu saukin wannan lamarin duk da bata cire rai a haihuwan namijin ba.
Inna indo ma ta kuma haihuwa ta haifi'yan biyu wannan karan dukka mata aka saka musu SAFIYYA da SURRAYYA.
Daga wannan haihuwar kuma sai haihuwa ya tsaye a cikin gidan gaba daya . Babu wanda takuma daukan ciki a cikinsu. Wannan ya sake saka Goggo Marka cikin tashin hankali ya sake sakata nadama Duk abun da tayi a da. Takan zauna ta tuna lokacin da take cewa zata haihu ta cika gida da yara mata har da maza. Sai an ringa cewa gidan mazan. Yau gashi ta haihun kuma duk yaranta sunfi yawa ta cika gidan amma kuma itace bata haifi namiji ko daya ba acikin matan gidan. Yaranta goma shadaya dukka mata. So dayawa sai ta zauna ta sasu a gaba tayi ta kallonsu.
Dan Allah ina son jan hankali mu gaba daya anan. Yara wata baiwa ce da Allah yake bayarwa ga wanda yake so kuma ya hanawa wanda yake so. Sannan Yara jarabawace a gare mu abun da nake nufi da jarabawa itace Allah zai iya baka yaro mai lafiya ko mara lafiya, mara ji ko mai ladabi Duk dan ya gwada yaga karfin imaninmu. Yaro ko mace ko namji dukka dai yara ne. Babu wata bambanci. So daya ma sai kaga mace ma tafi jin tausayin iyayenta akan da namiji. Kuma yanzu a zamanin yanzu duk abunda namiji zai iya mace ma tana iyawa. Kawai muyi fatan Allah ya bamu masu albarka shine kawai. Wanda basu samu ba Allah ya azurtasu ya basu masu albaraka komai lokaci ne kuma daga Allah ne. Mu roke shi zai bamu idan lokacin yayi in sha Allahu.
Ba dabaran mu bane ba wayon mu ne yasa Allah ya bamu su ba amana ce a gare mu Allah zai tambaye mu akan tarbiyar da muka daurasu, ilimin da muka basu, cinsu, shansu komai da ya shafi rayuwarsu.
Wannan duniyar yanzu ba kaman da bane komai ya chanza kuma yana kan chanzawa.
Mu kasance masu yawan yiwa yaranmu addua sosai da fatan alkheri In dan yaranki sun bata miki rai karki jefesu da mugayen kalamai ko zagi. Ki daure ki danne zuciyarki kimusu ce musu Allah ya shirya mun kai ya maka albarka da addua masu kyau. Sai kiga Sun natsu
Shi bakin uwa kaifi gareshi sosai. Duniyar yanzu baka bi danka da mugun kalamai da zagi bama sai kaga yara sun lalace bare kuma da bakin uwa akansu.
Yawanci yanzu wallahi yara bakin iyaye ne yake bibiyarsu. Duk wannan kalaman shegu, yan iska, munafuki, matsiyaci , mara kunya da dai sauransu dukka shine yake bin yara akasa gane kansu.
Akwai wani imam masallacin haram a masallacin Makkah sunansa Sheikh Adil Kalbani bakin mutum ne ya kasance wannan imamin lokacin da yake karami mara ji Magana sosai kullum idan yayi karambaninsa da rashin jinsa ya bata ran mahaifiyarsa  sai tace masa Allah ya shirya mun kai yasa kazama imami a masallacin ka'aba. Allah cikin ikonsa ya amsa mata adduarta ya shirya mata shi kuma yasa yazama daya daga cikin imam ka'aba. Toh yan uwa kunga misali kenen daga karfin baki uwa da adduar uwa.
Dan Allah mu ringa bin yaranmu da kalamai nagari.
Allah ya shirya mana su ya albarkaci rayuwarsu.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Where stories live. Discover now