10

84 4 3
                                    

Bismillahil Rahmar Raheem!

Wannan labarin ni na kirkira shi da kaina dan na fadakar.Ban rubuta dan na tozarta kowa ba. Idan ya zo daidai da labarinka/ki kusani is just a coincidence😀. Ina fatan zaku ban hadin kai wajen yin comment da latsa wannan tauraron 😁. Ku bini a sannu zaku fahimci darasin da yake cikin wannan labarin nawa wanda nasan zai kayatar da masu karatu in kunyi hakurin bibiyar Labarina.

Not edited🚫
💞KOMAI DAGA ALLAH NE☝️💞
(MBA)

Da isansu aka wuce da ita dakin haihuwa.
Tasha wahala sosai. Da har anso yi mata CS saboda bata da karfi, cikin ikon Allah ana kan shirin fita da ita dakin theatre ta haifo yarta katotuwa fara sol sosai kamarta.
Haka aka kintsa ta da babyn ta akakai su dakin hutu.
Murna wajen Alhaji Buba da Mama hanne ba'a magana.
Mama Hanne sosai ta nuna murnarta tsakani da Allah har da hawayen farinciki tayi.
Bayan Hanne ta Farka daga bacci. Likita ya shigo ya sake dubata da yarta. Yaga babu wata matsala sai ya sallamesu.
Suna zuwa gidan Hanne da yahansu suka hura babban murhu aka daura katuwar tukunyar ruwan zafi.
Alhaji Buba yasa aka fiddo rago daya daga cikin gidan gwonan sa aka yanka. Aka mata pepper sun kai da kafa wanda yasha kayan kamshi da kunun kanwa.
Haka Mama hanne tama yarinya wanka. Sannan aka kai ma Goggo marka nata ruwan wankan jego.
Sosai Mama Hanne ke kula da su.
A bangaren baratu kuwa ciki ya sake rikicewa Duk abun da akeyi babu ita aciki tana can kwance a asibiti ana kan bata magunguna ana kara mata ruwa sai washe gari da safe aka sallamo ta.
Tana shigowa gidan ta hadu da yahanasu a kofar gida zata kasuwa. Kallon sama da kasa suka ma juna.Babu wanda yace wa Dan uwansa ci kanka. Haka ta wuce daki wajen yayarta cike da tsanan yahanasu da alkawari daukan fansa.
Ranar suna ta zagayo aka radama yarinya Sunan Babbar yayar Alhaji Buba "ABIDA" kasancewa ita ta raineshi tun yana da shekara uku a duniya mahaifiyarsu ta rasu.
Ayinin sunan kam Mama Hanne tasha gori, habaici da zagi a wajen dangin Goggo Marka.
Haka suka ringa mata gorin haihuwa. Suna cewa haihuwa yanzu aka fara a gidan nan. Babu daga kafa sai sun cike gidan nan da yara fal. Maza da mata. Haihuwa gaba kuwa magajin Alhaji Buba Goggo Marka zata haiho.
Wannan abu yama yan' uwan Mama hanne da wasu daga dangin Alhaji Buba ciwo. Inda wasu kuwa kararara suka nuna suna gowon bayan Goggo Marka.
Anso a danyi rikici wannan ranar Amma sai suka hakura suka zuba musu  ido. Suna ala wadai da jahilci irin nasu. Toh in ba jahilci ba Ina mutum mai ilimin addini da ilimin zaman duniya zai goran tama wani haihuwa ?
Dan Allah bai bawa mutum haihuwa ba sai akama goranta masa.?
Sun manta Annabi Ibrahim bai samu haihuwa da wuri ba? Haka shima Annabi zakariya sai da ya manyanta kafun Allah ya azurta shi da haihuwa?
Sannan ai rayuwa kanta jarabawa ce. Babu wanda yafi wani wajen Allah sai wanda ya fi tsoronsa da kiyaye dokokinsa. Dan baka haihu ba bayana nufin Allah baya sonka ba ko ya manta da kai ko kuma wani laifi kayi masa ya hanaka ba. Itama wanda Allah ya bata bawai yafi sonta bane. Ko wani dabaran ta bane yasa ya bata. Allah ne yaso bata kuma ya bata.
Dan haka idan Muna da wata ni'ima wanda Allah ya azurta mu dashi to kar muyi tunanin isar mu ne yasa muka samu. Rashin haihuwar jarabawace a wajensu haka zalika mu da aka azurtamu da haihuwar jarabawace a garemu. Don abaka rikon mutum guda mai rai daga cinsa, shansa, tarbiyarsa, iliminsa wallahi ba karamin abu bane musamman a wannan zamanin.
Allah ya shirya mana zuri'a. Allah ya taimake mu akan tarbiyar yaranmu. Ameeeeen .
Haka har akayi suna aka watse.

Rayuwa taci gaba da tafiya a gidan Alhaji Buba. Mama Hanne na shan habaici da gori a wajen Goggo Marka da Baraka. Dan ma yahanasu na taka musu biriki in sun fara tsiyarsu. Haka har ABIDA ta cika wata tara a duniya inda a lokacin Goggo Marka ta fuskanci tana da shigan ciki. Murna da jida kai, gori habaici da salon iskanci sai kara gaba yake a gidan Alhaji Buba. Dan fa yanzu Mama Hanne bata iya zama tsakar gida sai an bita da gori. Haka ko cikin biki tashiga dangin Alhaji Buba sun ringa binta da bakakken maganganu. Tun tana iya danne wa har yakai bata iya rike zubar hawayenta a gaban mutane. Yahanasu ce take Dan kwantar mata hankali ta tsawatar wa mutane. Amma kuma sauran sun girme mata babu yadda ta iya sai de ta bawa Mama Hanne hakuri kawai.

A kwana a tashi babu wuya gurin Allah har cikin Goggo Marka ya cika lokacin haihuwa . Inda ta haihu Yarta mace aka saka mata suna SHAMSIYA. Ta so ace namiji ta haifa. Amma tunda haihuwa yanzu ta fara na gaba yara maza zata haifa ta cika gidan fal. Sai an ringa kwatacen gidansu da gidan Maza (hmmm sai kace ita take bawa kanta ).
Wannan karan ma Mama Hanne tasha gori amma haka aka yini aka watse ko cikanku Mama Hanne da danginta basu miyar musu ba.

SHAMSIYA nada wata biyar Goggo Marka ta kuma samun ciki. Iskanci da ji dakai sai abunda ya karu. Ta zama matar so acikin dangi. Komai yanzu da ita akeyi. Acewarsu itace tasu tunda tana haifa musu. Ba Kamar Mama Hanne ba da babu abunda take musu sai de taci Tasha tayi kashi. Ko abun biki yatashi sai de azo wajen Goggo Marka. Taron manyan mata ma ita take zuwa. Komai an ware Mama Hanne a ciki.
Duniya hmmm Dan Adam abun tsoro. Mutane ba'a iya musu da sunga ba kada abunda suke so ko su amfana daga gare ka shikenen sai su manta da kai. Yanzu duniya ta lalalace da wuya kasamu mutum da zai zauna da kai tsakani da Allah badan wani abu naka ba.

KOMAI DAGA  ALLAH NE!!!( ARZIKI & ILIMI)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon