SANNU SANNU Bata hana zuwa..

939 27 1
                                    

[6/15, 11:34 PM] My S Nomba: 🚶‍♀️🚶🏻‍♂️ *SANNU SANNU*🚶🏻‍♂️🚶‍♀️
💎 _Bata hana zuwa..._💎

_WRITTING BY:_ *BILLY S FARI💎*

_DEDICATED TO:_ *BLOOD SISTER'S (AMZAHFAZ)*💋

_BESTOWED TO:_ *ZAINAB AL-AMIN (MOM NA'EEM)* AND *AMINA UBA AYUBA (OUM ASHFAQ)*💞

*DOMIN FARINCIKINKI SISTER SADIYA ZANGO (MIEMAH)*💖

*FATAN ALKHAIRI AGAREKU MOMMAH ME NANA HAFSAT (MISS XOXO) AND MAMANA HAFSAT RANO(OUM AFFAN)*❤️

Page___3💎

Murmushin da bai kai ciki ba shurahbil yayi masa yana kallon yaran da suka duqufa suna kallo abunsu hankali kwance, bud'e gambun motarsa yayi yafito tare da miqa masa hannu suka gaisa, fuskar shurahbil a d'aure yace "ammm.......kamar naso nawayi fuskarnan, waye kai? ya tambayeshi Kai tsaye batare da wani shayi ba.

"Ni ba kowa bane" shima ya bashi amsa atak'aice,

"Ok meya kai yarannan acikin motarka bawan ALLAH?" Yasake jefa masa wata tambayar batare daya dubi girman saba, Yana tunanin wane daliline zaisa daga ganin yara ya d'aukesu yatura cikin motarsa, ko dai so yakeyi ya sace sune, muryarsa yajiyo yana cewa,

"Ganin yanda kabar motarka abud'e sun fito batare da sanin inda zasu nufa ba shine dalilin da yasa nayi tunanin tsayawa na taimakeka ta hanyar tsaidasu har sai kadawo, yakamata kasan cewa wannan abun da kayi sakaci ne babba kuma kuskurene? qananan yarane su dake buqatar cikakkiyar kulawa, don haka yakamata akula dasu sosai" bai jira me zai ceba ya sake bud'e gambun motar yace dasu, "Yawwa yaran baba, kuzo ga baba nan yadawo kunji ko?." Maqale kafad'a sukayi sunaci gaba da kallonsa yayi murmushi tare da cewa, "yatafiyarsa kenan kun fasa zuwa wajen dady da ummie ko?"

"Laa..a'a nidai zanje." hassana tafad'a, hakan yasa itama hussaina ta taso tana fad'in, "nima zanje wajen dady da ummie." Fiddosu ya dingayi d'aya bayan d'aya daga cikin motar ya diresu qasa had'e da juyowa yana kallon shurahbil daya saki baki yana kallonsu yace, "ga yaranka nan, amma don ALLAH yakamata adinga kulawa" sannan ya shiga motarsa ya tayar yaran na d'aga masa hannu suna yimasa byebye, yana qoqarin barin wajen da sauri shurahbil ya iskosa tare da duqowa ta saiti jikin glass d'insa yace "afuwa alhaji, dama kasan yaran nan ne?"

Girgiza kai mutumen yayi don yafahimci gaba d'aya shurahbil qurciya na damunsa, girmane kawai ya rigayi hankali saboda yanayin yanda yake magana, abun nasa kamar rashin iya magana kamar kuma isa da jijji da kai a tattare dashi, kallonsa yayi sannan yace, "Ban sansu ba kuma ban san ko suwaye su ba, Amma abu d'aya nasani shine tun wajen da sukayi accident dana ganesu jikina yabani cewa kamar akwai wata alaqa tsakanin ni dasu kuma araina naji ina sonsu har acikin zuciyata hakan yasa nabiyo bayanku lokacin da kuka taho dasu, ina fatar jikin iyayen nasu da sauqi saboda tsaurin tambayoyinka d'azun sun kasa barina na tambayi hakan tun farko" sinne kai qasa yayi yana sosa qeyar kansa had'e da cewa "kayi hak'uri Alhaji naji tsorone araina saboda yanda duniyar tamu ta koma."

"Babu komai in sha ALLAH ka gaida iyayen nasu, in sha ALLAH gobe zanzo nadubasu saboda marece yayi yanzu."

"Shikenan Alhaji Amma shi mahaifin nasu ALLAH yayi masa cikawa, mahaifiyarsu kuma anyi nasarar yimata tiyata anciro wasu 'yan biyun" da motar na slow amma alhaji najin haka ya kashe motar yana sallallami kai kace wani shaqiqin sane, yajima yana jajanta abun aransa tare dayi masa addu'a sannan yabar wajen bayan ya bashi complement card d'insa.

Yana barin wajen yanufi inda twins d'in suke zaune agaban motar suna wasarsu hankali kwance yaje yaja hannuwansu ya nufi inda su Abba suke riqe dasu...

Suna isa Abba ya miqa masu hannuwa alamar suje wajensa, da gudu suka isa tamkar sun sanshi ya rungumesu yana kallonsu d'aya bayan d'aya yana jin wani irin sonsu da k'aunarsu nashiga zuciyarsa, kallo d'aya zakayi masu kasan kamarsu sak da mahifinsu tamkar an tsaga kara hasken fatar mahaifiyarsu ne kad'ai suka d'auko, hawaye ne suka zubo masa a idanuwa yagoge had'e da cewa.

SANNU SANNU Bata Hana zuwa..Where stories live. Discover now