PROLOGUE

3.6K 319 130
                                    

BISMILLAHIR-RAHMANIR-RAHEEM

✍ZABI NA✍

☆☆☆☆☆☆

Babban abin da yake janyo wa wasu ‘yan matan rashin samun mazajen aure shine ruwan ido. Da yawan ‘yan mata yayinda suka kai wani mataki na girma, tauraruwar su na haskawa a wannan lokacin.. Hakan yana sanyawa samari su dinga tururruwar zuwa wajen yarinya don zama masoyinta na aure da wanda ba na aure ba....

A wannan mataki ne ita budurwar take ganin ta zama tauraruwa wanda hakan ya kan sa ta ruwan ido wajen zabar masoyi na qwarai kuma na gaskiya wanda yake sonta tsakani da Allah.

‘Yan matan su kan zabi masoyi, Idan kuma suka samu wanda ya fi shi sai su canza... haka zasu yi ta canzawa har su rasa wanda za su zaba.

Rudin duniya ya kan saka idanuwansu rufewa su rasa gane ina suka dosa.

Ba wani abu bane yake janyo hakan...

illar KWADAYI da kuma SON ABIN DUNIYA shi yake kawo hakan

Wani lokacin ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.

Da yawa a yanzu sukan dauki buri mai girma su dorawa kansu wanda hakan ko kusa ba zai samu ba idan kuwa ya samu, toh sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauqi qarshe a sha wahala.

Wasu sukan sakawa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan saurayi mai hanci dogo, shi ma dogo fari kamar zubin fulani irin saurayin cikin littafin Hausa.

Sai mace ta saka wa zuciyarta ita lallai sai irin wannan namijin za ta aura wanda yake ba shi da makusa kamar shi ya yi kansa.. ko kusa bazan ce ba za'a samu ba, amma kafin a samu za'a dade a ce an samu irin wanda ya hada komai ba shi da wani makusa kamar yanda na cikin littafin Hausa yake.

Wasu su kan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so saboda sun riga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin.

Ko kuma mace ta kudurta cewa lallai sai mai KUDI, saboda mijin qawarta ko saurayin qawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko wanda sana’arsa ba mai girma bace irin wanda duniya za ta san da zaman sa...

Ire-iren wadannan da ma wasu ra’ayoyin nasu wadanda ban fado su ba... toh su kan sa wasu matan ruwan ido, domin ba duka ne aka taru aka zama daya ba, sai an amince wa saurayi amma da zaran wanda ya fi shi ya zo sai zance ya lalace.

Ki sani cewa yayinda kika tsaya ruwan ido za a kai ki a baro komai kyanki. Mata su kan rasa na zaba har lokacin da samarin za su daina zuwa, lokacin mace ta wuce wannan matakin da tauraruwarta take haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da ta yi tana da na sani tun a wancen lokacin ta zabi daya da ya fi mata, amma yanzu ga shi tana zaune ana aurar da qannanta tana gani.

A cikin ruwan idon wasu su kan qudurta cewa su ba za su auri mai mata ba, wani lokacin ma har iyayen su kan ba wa yaran nasu gudummowa wajen haifar da ruwan idon, yayinda aka rasa sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo ko da mai mata uku ne, saboda burinsu a lokacin a yi auren domin kar ‘yan unguwa su rinqa cigaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar.

A cewar wasu ‘yan matan zama da saurayi daya tsautsayi ne, gwara su raba qafa har Allah yasa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne za ku ga wasu mazan na arziki wadanda suke da niyyar yin aure kuma sun je wajen yarinya da zuciya daya, amma ita sai ta qi amincewa da soyayyarsa ko da kuwa bashi da wani makusa a tare da shi, sai su dinga biye wa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin.

ZABI NA | ✔Where stories live. Discover now