ZAHRAH HAYATY.....5/6

40 2 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*🌷

*By~AUFANA*

    *5/6*
#Washe gari
Washe gari tinda sassafe suka shirya suka fita aiki,amma yaukam driver ne yakai hayat office, mutallab kowa shiyai driving kansa izowa hospital dinsa.

Tindaga kantamemen kofar get d'in shiga company din zakaga tsintsar yanda ake bama hayat girma cikin matuk'ar girmamawa yana amsawa ta hanyar d'aga hanu kawai, waensu kuma yakan karb'a da baki amma cikin izza da k'asaita sbd hayat akwai masifaffen miskilanci wanda dayawan mutane keganin kamar yanada girmankai ne wanda bahaka bane.

Dik wanda yazauna dashi zaifahimci cewa hayat mutum ne mai sauk'in kai bashida rigima sosai kuma bayasan hayaniya sosai, haka kuma idan yanajin fara'arsa da nishad'i dakansa zai fita gun ma'aikatansa yayita fira dasu cikin nishad'i, sannan yanamasu alkhairi sosai, shiyasa suke matuk'ar jin dad'in aikinsu.

Bayan ya'isa office dinsa dake hawa na k'arshe wato hawa na ashirin ta hanyar tallafin shiga lifta.

Yatararda aiki sosai danhaka baisamu lokacin kansaba sai kusan 1:30pm shima din lokacin sallah ne yayi shiyasa yasauka kasa, suna gama sallar kuma yasake komawa, baisamu lokaci ba dakyau dai saukusan 6:00pm sannan yasamu yazauna.

Yanacikin hutawa kwatsam tinanin yarinyar yadawomasa arai, nantake yadakko wayarsa yashiga kiran lambar mutallab, saida hartakatse amma baid'agaba, nanyasake kira har uku still dai bai d'agaba.

Baigajiyaba yasake kira cikin sa'a kuwa aka d'aga, dasauri yace "dan uwa kana inane?" ahankali mutallab yace "Ina hospital dan uwa, yah akayine" dasauri hayat yace "plss ganinan zowa karakani rigarsu yarinyar nan" Ohk.....mutallab yafada kamin yasake cewa.

"But......seriously inada wani aiki babba, operation zamu shiga yanzu, saidai bazamu dadeba for 2hrs ne kawai idan zaka iya hkr" numfashi hayat yasauke sannan yace "Ok....badamuwa ganin zowa" mutallab yace "Ok..." sannan yakashe wayar.

Bayan yakatse kiran nan ya had'a kayansa yad'auki jakarsa da wayarsa yafita.

Daganan Kai tsaye asibitin mutallab yafice, koda yaisa kowa tini haryashiga operation din danhaka yashiga office dinsa yajirasa.

Koda mutallab yafito dare yafarayi danhaka cikin sauri yashirya suka fice.

Acikin mota ne mutallab yadubi hayat yace "dan uwa....wai menene manufarka akan yarinyar nan ne?" dan murmushi hayat yai sannan ahankali yadubi mutallab yace "dan uwa so nake najefi tsuntsu biyu da dutse d'aya ne tsakanin FATIMAH da ZAHRAH, amma kamin nan inaso nasan wacece ZAHRAH sannan babu wata alak'a tsakaninsu, idan har na tabbatarda hakan to inamai tabbatar maka matsalata da fatimah tazo k'arshe".

Murmushi sosai mutallab yai sannan yace "bansan wane irin SO kakema yarinyar nanba dan uwa, nidai kawai shawarata agareta itace, kada ka cutarda yarinyar mutane ka ruguzamata rayuwa wajen gyara taku rayuwar, kada kayi amfani daita ka ruguzamata rayuwa, kasani Allah bazai tab'a barinkaba sannan kuma bazai yafema hakkinta ba".

Shuruu hayat yai nawasu mintina kamin yasauke nannauyan numfashi sannan yace "mutallab.....kasani wlh akan fatimah zan iya aikata komai, zan iya aikata koma menene matuk'ar zan samu damar mallakarta matsayin matata, sbd haka kadaina yiman wa'azi domin bad'auka zanyiba".

Murmushi kawai mutallab yai daganan baisake cewa komaiba.

Kai tsaye rigar tasu yarinyar wato ZAHRAH suka fice, dugu suke sosai danhaka nantake suka isa rigar.
Bayan sun isa sannan suka fice Kai tsaye izowa gidansu, bayan sun isa sannan suka saka yaro yamasu sallama da mahaifinta.

Cikin masifa kawun Zahrah yafito azatonsa waenda ke zowa gunsa aron kud'ine sukazo shiyasa tinda yaron yafadamasa ana sallama dashi yaketa faman masifa harya fito, saidai yana fitowa yai tozali dasu hayat sai yanayin fuskarsa yacanja izowa fara'a.

Dasauri yakariso cikin bagwariyar hausarshi yana masu barka da zowa harda kai hanunsa gun hayat danufin sugaisa, d'an murmushi hayat yai tareda d'aga masa hanu danhaka yajanye hanun nasa cikin yanayin jin kunya, mutallab yai murmushi kawai.

Gaisawa sukayi sannan hayat yace "am....munzone muduba jikin zahrah dafatar dai tasamu sauk'i sosai" cikin murmushi yawangare baki yana bagwariyar hausarshi yace "ayyooo.....zahrah kam ai abun baasewa komi,wollahi ziya dakyar mukayi bacci sai sambatu yake, sannan kafanshi yau dasafe saida mukaze gun masu d'auri ashe yasamu targad'e ne a kafa, jikin nasi babucau wollah ga zazzab'i, munkasi kudi sosai kamin musamu agano kanshi" tsananin mamakine yakamasu sudika sbd ganin jiya koda suka barta bawani alamar jin ciwo datayi tana tafiyarta kalau amma ace wai harda targad'e.

Basudai nunamasaba hayat yace "yaasalam, assha Allah yabata lfy yak'ara tsarewa" kawu yace ameen....

Nanyasake cewa "toko zamu iya ganinta domin mudubata" dasauri kawu yace "eyyah....ai yayi bassi yanzu, dakyar muka samu yayi bassin ma" hayat da mutallab suka kalli juna.

Mutallab yace "Eyyah, to badamuwa agaida ita da jiki Allah yabata lfy, madawo gobe idan ta tashi" kawu yace "toh..." yana sosa kansa kamar mak'aryaci ko marar gaskiya, kud'i hayat yaciro masu yawa daga aljihunsa yabama kawun, aikwa dasauri kaman zai cabe hanun hayat ya karb'a yanata gaman murmushi da gdy.

Hayat yasake kallon mutallab, nan sukamashi sallama suka fice.

Cike da mamakin kawu sukabar rugar, mutallab yace "nifa a fahimtarda namawa kawun nan nata makwad'aici ne maisan abun duniya, nayi mamaki matuk'a ace yarinyarda muka rabu daita jiya lafiya kalau acewai yau harda gyaran targad'e akamata harma dakyar aka kwana daita" hayat dai murmushi kawai yai.

#/Aufana for life.🥰

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now