ZAHRAH HAYATY 29/30

40 4 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *29/30*
Sannu ahankali hayat ke driving lokaci bayan lokaci kuma yana kallon zahrah datasha kyau take zaune agaban motar kusa dashi, kusandai zaman kurame akayi acikin motar, zahrah dama batasaba da fira da hayat ba wanda shi hayat kuma dama miskili ne bashida hayaniya bare surutu.

Time to time sukan had'a ido wurin kallon juna, idan suka kallo juna kuma sai kowa yad'auke nasa idon, ahaka harsuka isa katafaren gidansu hayat wanda tindaga tamfatsetsen get d'in shiga gidan zakasan gidane na manyan mutane kuma babban gida, asaman get din gidan antubuta "Welcome to Matawalle's house" suna isowa security's d'inda ke kula da kofar shigar suka taso dasauri suna kwasar gaisuwa gun hayat ya amsa cikin sakin fuska sannan suka bud'e masa get d'in sukashige.

Tin a k'ofar shiga zahrah taware daran daran fararen idanuwanta tana kallon ikon ubangiji, zata iya cewa tinda take a rayuwarta bata taba gani kokuma shiga irin wannan shahararren gidanba, kai batama taba tinani ko mafarkin zata taba ganin irinsaba koda a mafalkine kowa, sbd ita yauwarta a iya k'auyensu ne tatsaya daga kauye sai kasuwa shkn.

Amma yau cikin ikon ubangiji saigata tsumbul harcikinsa.

Bayan yagama parking acikin katon parking lots kuma a tsakiyan dank'ara dank'aran motocin gidan saisuka fito atare, bayan sunfito saishi yashiga gaba tareda cemata "zomuje ciki, amma kiyi hattara sannan kiyi hkr dadik abunda zaki gani ko zakijima kunnayenki"  mamakine ya bayyana a fuskarta sbd jin abunda yafad'a wanda takasa gane abunda yake nufi, hartatsaya tana tinani can kuma saitabi bayansa ahankali.

Ahankali suna tafiya harsuka isa side d'in mahaifansa inda sukaci karo da hairan da hunaiz wato k'annen hayat maza guda biyu, dasauri cikin girmamawa suka gaishe da hayat cikin fara'a da farincikin ganin d'an uwan nasu, nan shima ya amsa cikin sakin fuska.

Bayan sungaisa saisuka kalli zahrah sannan suka gaidata cikin sakin fuska "Ina wuni yaya fatima"  mamakine ya k'ara bayyana a fuskar zahrah jin sunanda suka kirata, badanda itakad'aice mace a wurinba todatace bada'ita sukeba dikda kowa tasan cikekken sunan nata shina fatima zahrah, to amma bakowa kekiranta da fatima ba.

Danhaka saita amsa masu itama cikin fara'a, bayan sungaisa sai hayat yafice tabi bayansa.

A parlon ummi suka fara shiga cikin sa'a kowa bakowa acikinsa danhaka hayat yace tazauna yana zowa, bedroom din ummi yafice, yad'auki mintina kamin yafito, candai yafito tareda wata mata kyakkyawa wacca daka ganta kasan mahaifiyar hayat ce sbd akwai kama sosai.

Dasauri Zahrah tamik'e tadurk'usa tana gaida ummi "Barka da rana" fuskar ummi ba walwala sosai hakadai ta amsa mata sannan tazauna nan shima hayat ya zauna.

Sai shuru yaratsa parlon aka rasa wanda zaiyi magana acikinsu, fuskar ummi gaba daya babu walwala ko fara'a a tattare daita koma kallon zahrah batasanyi, abunkam yabama zahrah matuk'ar mamaki.

Hayat yakatse shurun da fad'in "fatima tashi muje mugaishe dasu gwaggo" jin sunanda yakirata dashine yak'ara sakata acikin mamaki dakuma rud'ani, fuskarta d'auke da tsintsar mamaki tamik'e tsaye kawai tanamasa kallon mamaki, baiko kalletaba haka yajuya yana fad'in "Ummi zamushiga gun mai girma matawalle" uffan ummi batace dashiba tai sauri tashige bedroom d'inta kawai.

Abun yak'ara rud'arda zahrah, ganin hayat yafice yasa itama tabi bayansa.

Kai tsaye side d'in mai girma matawalle da uwar gidansa suka wuce, tin a k'ofar shiga sukafara cin karo da muwadda tana d'auke da ahlan d'an aunty mamu, cikin fara'a da sakin fuska tagaishe da hayat sannan tajuya tagaishe da zahrah, nan zahrah ta amsa fuskarta ba yabo ba fallasa.

Nansuka dunguma suka shiga ciki atare.

A babban parlon mai girma matawalle suka tarardasu dika harda aunty mamu da gwaggo da abban hayat dika, mai girma matawalle narik'e da glass cup a hanunsa yana dariya akeelah ce kan cinyarsa tana wasa da teddy d'inta.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now