ZAHRAH HAYATY 31/32

39 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *31/32*

Hayat ne zaune kan kujera acikin k'ayataccen office d'insa, aiki take tuk'uru domin yaukam sunada aiki sosai a kamfanin, gawaensu baki dasukayi daga Canada, danhaka yaudaikam aiki suke harma yamasu yawa.

Around 11:00am suka shiga meeting da bak'inda sukayi.

Acan gidansa kowa, bayan minti biyar dafitar fatimah ma'aikatanta masu mata hidima suka fahimci bata gidan, danhaka suka sanarda security's din gidan, nanfa aka shiga nemanta acikin k'aton gidan dama wajensa gaba d'aya.

Saidai harkusan 12pm baagantaba babu ita ba amonta, hankalin security's din yatashi matuk'a sbd hayat yamasu alk'awarin kora matuk'ar suka bari fatimah tasake fita, danhaka suka bazama nemanta acikin unguwar gaba d'aya.

Haka suka karad'e unguwar ta G.R.A gaba d'aya har wajenta amma basugantaba, ganin haka yasa suka kira jami'an tsaro suka fad'amasu abunda ke faruwa, badawani jimawaba police suka iso unguwar, nantake unguwar tarikice tako'ina neman fatima akeyi amma shuru kakeji.

Ganin haka yasa dole badan sunsoba aka kira hayat domin sanardashi halinda ake ciki.

Wajen 10miss calls akamasa amma baid'agaba sakamakon idan suka shiga meeting d'in kowa kashe phone d'insa yake, danhaka dai basusami yin magana da hayat d'inba, ganin haka yasa police sukaje suka Kai report a station d'inda ke kusa da unguwar.

Saikusan 2pm sannan hayat yafito daga meeting d'in, masjid yafara zowa yagabatarda sallah sannan yadawo office, koda yadawo domin yaci abinci sai akafad'amasa ai yau ba'akawo abincinba kamar yanda aka saba, mamakine yakamasa sbd tin bayan aurensu fatima bata tab'a fashin turo masa da abinciba daga gida, gabansa ne ya yanke yafad'i har saida yakaranto "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, hazbiyallahu wani'imal wakiiil...." wayarsace tafad'o masa arai danhaka yakira wayar telephone yace akawomasa wayarsa yana office.

Bayan mintina uku saiga d'aya daga cikin ma'aikatansa  yashigo, cikin girmamawa yadurk'usa yagaidashi sannan yamik'a masa wayar ya karb'a taredayin godiya.

Kowa yakunna wayar abun mamaki kusan 30miss calls, 20 din daga security's d'in gidansa ne 10 d'in kuma bak'uwar number ce.

Layin security's d'insa yafara kira aikwa bugu daya ana biyu aka d'aga, baiko jira komaiba yajefamasa tambaya "Incedai lafiya haroon" cikin murya mara dad'i yaron yafad'amasa dik abunda yafaru.

"Ohh sheeeet.....!" hayat yafurta dak'arfi, nantake ransa yab'aci matuk'a zuciyarsa tashiga bugawa kamar zata faso k'irjinsa tafito "haroon kuna aikinme harta fita baku ganiba...?" haroon yarasa mezaicemawa hayat kawai yashiga nashi hkr.

Baiko tsaya saurarensaba yakatse kiran, key car dinsa yad'auki kawai yafice.

Dasauri yasauka k'asa yafice gunda ake aje motoci yashiga d'aya yafice, yana hawa kan titi aka kirasa, koda yad'auka yaduba wannan number d'in ce da'aka kirasa daita d'azun, dasauri yad'aga, sallama aka masa farko ya amsa sannan aka cigaba da magana "Muna fatan muna maganane da Hayatudeen Hashim matawalle" hayat yace "eh...shine lafiya dai..?" cigaba da magana akayi "kazo police station dake aliero estate, munkama matarka fatima da hannu dumu dumu wajen kisan wata budurwa, takashe yarinyar sakamakon shan jininta datayi, sbd haka yanzu tana hanunmu kazo".

Wani irin abu hayat yaji yazo yatokaremasa k'irji wanda yahana masa cewa uffan har saida aka katse layin.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...." shine kawai abunda yaiya furtawa sannan ya'ajiye wayar.

Dasauri yabankama motar wuta nantake kowa saigashi unguwar ta aliero estate sannan ya'isa station d'in.

Dasauri yai parking yafito yashiga station d'in.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now