ZAHRAH HAYATY.....17/18

32 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *17/18*
Washe gari bayan sundawo daga masjid mutallab yake cewa hayat  "dan uwa...dama inaso namaka wata magana"  hayat dake kwance kan kujera 2seater batareda yad'agoba yace "inajinka" nan mutallab yacigaba da magana.

"am.....dama bawata magana bace, magana ce akan matarka daka d'aura aure kuma kawofantarda ita kamar ba matarka ta sunnah bace, dikda baayi auren kamar yanda addini ya tanadarba yakamata ka kula da'ita kamar yanda kowanne miji yake kula da matarsa, ahalin yanzu dikkannin wani nauyi nata yarataya a wuyanka sbd haka nake maka tini dakaji tsoron Allah kasauke nauyinta dayake rataye a wuyanka".

Ahankali hayat yatashi zaune cikin yanayin bacci yakalli mutallab yace "tokai wane nauyine kake ganin bansauke nataba, bayan bata rasa ci ba batakuma rasa sha ba, haka kuma ana kula daita sosai fiye da kularda take samu acan gidan iyayenta data baro, so ni bayan wannan bansan kuma wata kulawa dakake so nabata ba".

Wani gwauron murmushi mutallab yai tareda gyara tsayuwansa sannan yace  "idan kana bata ci kana bata sha, to itakuma mu'amalar aure fa, sannan tinda yarinyar nan ta tare koda sau d'aya baka tab'a kwana a gunta ba, kullum kana nan anan kake kwana, hayat kaima abunda kasanine, bafa ci da sha ne kad'ai rayuwar aure ba, itama mutum ce sbd haka tana buk'atar mijinta a kusa daita, sannan hak'kinta na mu'amalar aure baka tab'a saukeshi ba kuma akansa kad'ai Allah zai iya kamaka yamaka hukunc........i"

Tin baiko k'arisaba hayat yadakamasa wata iriyar tsawa mai karfin gaske har saida yarazana, sannan yataso yazo gab dashi cikin tsananin b'acin rai yanunasa da yatsa idanuwansa sunyi zajir yace.

"Mutallab......nakula kafara rainani a yan kwanakin nan, Inaso kasani har gobe agabanka nake, nine agaba dakaiiiii........" yak'arisa da k'arfi cikin masifa, sannan yacigaba da fad'in.

"Mind you're language mutallab.....am not ur mate, ni ba sa'arka bane, sbd haka kadaina sakamin ido a ayyukana karka sake sakamin wannan kazamin bakin naka idan har bazaka iya kalloba to karufe idanuwanka"  yak'arisa maganar idanuwansa cikin na mutallab tamkar zasu fad'o k'asa.

Mutallab bai iyacemasa komaiba harya gama yafice fuuu yabar d'akin.

Kallo kawai yarakasa dashi harya fita sannan yazauna kan gado tareda janyo filo yakwanta yana fad'in "Allah ishiryaka hayat, idan dasabo ai nasaba da halinka, fatana kawai kagano gsky kadawo kan hanya sbd kokad'an banasan Allah yakamaka da laifin wannan yarinyar" nan yai kwanciyarsa.

Tin around 8:00am driver din hayat yasaukesa a airport, 10am dot jirginsu yad'aga izowa kasar Dubai, a yayinda gwaggo hidaya itama tad'aga izowa garin habuja, to Allah yatsare hanya ameen.
      ...................

A b'angaren zahrah kowa, harta fara sabawa dasu Lidia saisuyita shan firarsu atare, a ranarda tacika sati uku da tarewa, Lidia tatsefe mata kai tawankesa tas sannan tamata kitso mara yawa sosai Amma kuma mai kyau.

Idan dasabo yanzu tafara sabawa da zaman kad'aici idansu Lidia suka fice, saidai dik sanda tatina da gida saitayita kuka mai ban tausayi tanaji aranta inama zata iya data gudu daga gidan, saidai bahalin guduwar sbd katangar gidan tanada tsayi sosai k'ofar gidan kuma ga get man, saidai tak'udiri aniyar dik sadda tasamu dama saitabar wannan gidan.
       .................

Kimanin kwana biyu hayat yai a Dubai sannan yadawo, abunka da d'an uwa yana sauka mutallab yakira yace yazo yad'aukesa airport, nan mutallab yashirya tareda drivers dinsa biyu sukaje suka d'aukosa suka dawo gida.

Bayan yai wanka yaci abinci yai sallah, nan yake bama mutallab hak'uri kan abunda yafaru tsakaninsu, murmushi kawai mutallab yai sannan yace "karka damu d'an uwa, idan dasabo ai nasaba da halinka" sai hayat yai murmushi tareda rungumesa.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now