ZAHRAH HAYATY....11/12

27 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *11/12*
Tin daga nesa kawu yahangosu suna tahowa izowa gunsa suna tinkarosa, abun mamaki, aikwa dasauri yamik'e daga duk'enda yake yana noma, tsananin mamaki bayyane k'arara a fuskarsa.

Ahankali har suka k'arisa gunsa, cikin sakin fuska hayat yace "sannu da aiki kawu"  kawu yawangare baki cikin fara'a sosai yace bakwariyar hausarsa "sannunku da zowa Alhj, meyasa baku tsaya acan gidaba a turo a kirane naje, amma kuzo har nan din dakanku" murmushi hayat yai yace "karka damu kawu"  nan kawu yai sauri yaje yad'akko yar wata yagaggiyar tabarmanda yake zowa daita dajin ya shimfid'a masu.

Hayat ne kawai yazauna mutallab kam kasa zama yai sbd tabarmar ma batada tsabta sannan batada girmanda zata daukesu sudika, danhaka hayat da kawu suka zauna.

Ganin mutallab yayi tsaye sai dasauri kawu yamike yana fadin "Alhj kazauna mana, kayi tsaye" dasauri mutallab yace "No...No....No karka damu kawu kazauna kawai"  sai kawu yazauna kamar yanda mutallab yace.

Bayan yazauna sannan akashiga gaisawa, kawu sai wasan hakora yake kamar gonar audiga gashi hakoran dik goro ne basuda tsabta bama dad'in kallo agaresu.

Cikin nutsuwa bayan sungama gaisawa hayat yadubi kawu yace "am...kawu, maganace babba ke tafe damu agunka" kawu yanutsu yana sauraran hayat, nan yacigaba da magana "kawu tin bayanda muka bige yarka wato zahrah, nasakata a idona nayi ido biyu daita Allah yasanyamin santa a zuciyata"  dasauri mutallab yakalli hayat sbd jin abunda yafad'a, shimad'in kallonsa yai yad'an masa murmushin gefen leb'e sannan yasake juyawa gun kawu yacigaba da magana.

"Kawu Allah yasanyamin san yarka Zahrah, wannan dalilin ne yasa nakasa hkr har naketa bibiyarta tsawon kwanakin nan, saboda haka nazo gunka domin nafad'ama nakuma nemi dama dakuma izinin magana daita agunka, Ina fatar bazaka hanani aurenta ba".

Wani irin farincikine ya bayyana k'arara a fuskar kawu, nantake yawage baki yana fadin "Masha Allah, wannan ai abun farinciki ne Alhj, karka damu Zahrah basida wani wanda yakeso kokum yakesansi, danhaka kawai kaje katuro magabatanka nabaka zahrah, dama idan yaro tagirma meya rage bayan a aurardasi, danhaka nabaka auren zahrah, kai ni ko yauma kakesan a d'aura auren za'a d'aura".

Gaba daya mamaki yagama cika mutallab, yayi tsaye kamar wani bodyguard.

Hayat kowa, murmushi ne mai k'arfi ya bayyana a fuskarsa har saida fararan hakoransa suka bayyana, cikin jin dad'i yace "to nagode sosai kawu, gobe ranace babba wato ranar juma'ah, danhaka magabatana zasuzo nemaman auren zahrah kuma zasuzo da sadaki sannan Inaso a daura auren dik a gobe" nan yasaka hanunsa acikin aljihunsa yaciro mak'udan kud'i yamik'awa kawu yana fadin "sannan ga waennan kud'in, naira dubu d'ari biyar ne saikuyi shiryen shiryen biki, nanda sati daya kuma zanzo nad'auki matata, bana buk'atar komai naku wanda yadanganci kayan d'aki ko gara kamar yanda aka saba a al'adance, kawai ni matata nake buk'ata".

Cikin fara'a sosai kawu yace "to yanda kace haka zaayi Alhj, mungode sosai da wannan arzikin, Allah yakaimu goben" hayat yace ameen....tareda mik'ewa tsaye.

Daganan sukayi sallama da kawu suka fice, kawu yamasu rakiya har gunda suka ajiye motansu, bayan sunshiga sun wuce sannan yakoma gonarsa.

Wani irin farincikine ya mamaye kawu ganin mak'udan kud'i ahanunsa kuma dika nasane, cikin yanayin mugunta irinta fulani yamurtuk'e fuskarsa yace "gwara nakarb'i kud'ina nabashi wannan banzar yarinyar mara asali da tushe konasamu na huta nima" saikuma yawashe fuskarsa yana dariyar mugunta.

Nan cikin sauri ya tattara kayansa bataredama yagama abunda yakawosaba gonar yafice gida.

Yana isa gida nan yakabartama gwaggon zahrah abunda ke faruwa, itama farincikine ya mamayeta hardayin gud'a wai yarsu zata auri mai kud'i, nantake tashiga mak'ota tadinga fad'amasu tana murna.

Nantake kankace kwabo kauyen KAMBAZAR FULANI yakauraye da lbrn zahrah tasamu miji mai kud'i za'amata aure gobe gobe.

Waensu dai susanya albarka waensu kuma suna tsegumi, kunsandai mutane baza'a hanasu aikinsuba na tsegumi bare kuma ance mai kud'i ne.

Waensu ma fadar suke, wai kilama hayat d'an yankan Kai ne ko dan kidmashin inji fulanin kauyen hhh Lol.

Hakadai maganganu keta yawo a kauyen, ita gogar Zahrah batamasan me akeba.

Sai gab da magrib sannan tadawo tasami lbrn abunda ke faruwa,abun mamaki zahrah tashige d'aki tayita kuka wanda ni kaina nakasa gane dalilinsa, shin ko son auren ne batayi kokuma hayat d'in ne bataso oho, dikda batamasan ainahin wanne daga cikinsu ne zai auretaba sbd kullum atare take ganinsu.

Gashi batasan sunansu ba barema taiya banbantasu kawai ganinsu takeyi,banbancinsu kad'an ne mutallab yafi hayat hasken fata sosai, shikuma hayat yafi kyau sosai kuma yafi kama da shuwa arab, tsayinsu d'aya hakama yanayin girman jikinsu.

Hayat yanada saje shikuma mutallab gemene kawai yakeda amma bashida saje, dikansu kuma sunada cikar suma irinta fulani, ammadai dikanninsu kyawawane matuk'a.

Danhaka batasan wanene daga cikinsuba ahalin yanzu saidai nangaba.
    .................
A b'angaren su hayat kowa, hayat yacika mutallab da tsananin mamakin abunda ya aikata yau, cikin tsintsar mamaki da b'acin rai yafara masa magana "hayat meka aikatane haka,kana cikin hayyacinka kowa, kayi aure batareda sanin iyayenmu ba, shin wai mekake nufine da wannan auren, wace irin manuface kakeda akan wannan yarinyar, wlh kabi ahankali domin dik ranarda MATAWALLE yagano abunda ka aikata ranka saiyafi na kuturu baci, haba wannan wane irin abune, karka mantafa kaine a matsayin magaji a wannan family namu na MATAWALLE, kamata yai ka auri yarinya wacca take yar babban gida, amaku aure irin na yayan gata bawai irin wannan auren ba wanda nama rasa da wanne suna zan kirashi, ba'ako gama rigimar wancan yarinyarba fatimah yanzu kuma zaka sake rakutumo wannan din, to wlh kasani dik ranarda asiri yatoni karka nemoni kuma karka sakoni aciki domin bana iyawa da rigimar maigirma MATAWALLE".

Kallonsa kawai hayat keyi harya gama sannan yace "Cool down my broz, ka kwantarda hankalinka mana, insha Allah babu wani abunda zai faru sai alkhairi, sbd alkhairi na aikata ba sharri ba, sunnar manzo na rayafa, itakuma sunnar manzo idan za'a rayata babu batun wai y'ar dangi ko yar masu kud'i ko yar sarauta kokuma yar talakawa, kamar yanda manzon tsira yafada yace, zaku iya aurar mace dan kyanta, iliminta, nasabarta, kokuma dan arzikinta, saikuma yace amma ku auri wacca takeda ilimi.

Sbd haka babu dalilinda zaisa ace wai dole sai yar manya zan aura sbd inad'an babban gida kuma inada tarin dukiya, ku kuje kunemi yayan masu kudin da mulkin ku aura mana".

Wani kallo mutallab yamasa kamin yace "to ai dama ace dan Allah ne ka aureta dayafi, amma wlh natabbata domin badan Allah ne yasa kayi wannan auren ba, domin kasamu damar kasancewa da Fatima ne" hayat yai murmushi yace "to miye matsala aciki, kai kafi kowa sanin irin tsananin Sonda nakewa yarinyar nan fatima, akanta ba abunda bazan aikataba, sbd haka kawai kazuba ido kayi kallo".

Hmm.......mutallab yasauke numfashi sannan yace "nazuba idon,amma kasani idan MATAWALLE kokuma su dady sukaji wannan lbrn baruwana, kuma karka sakoni aciki" yak'arisa tareda hararansa.

Dariya hayat yakwashe daita sannan yace "aikwa kaine akan gaba, kuma kana ciki tsumb'ul, sbd bawani wanda yasan sirrina saikai" dukan wasa mutallab yakaimasa yana hararansa shikuma yakauce yana dariya.

Ahaka suka isa gida mutallab sai faman gallamasa harara yake shikwa yana tsokanarsa yana dariya.

Daren ranar haka hayat yakwana cikin tsintsar farinciki, yakira Fatimarsa sukasha firarsu har tsakiyan dare sannan suka kwanta, shidai mutallab kallansa kawai yake yana tab'e baki.

     Washe gari tinda sassafe office kawai yaje yai signing yawuce kauyensu Zahrah.

Tarin abinci kala kala yakaimasu buhuhunan shinkafa dana taliya, kwalayen kajin turawa goma, dikdai wani abunda yadanganci nau'in abinci yakaisa, drivers dinsa guda uku da dank'ara dankaran motocinsa ne sukazo suka sauke abincin suka wuce, kawu sai faman gdy yake, bakinsa yaki rufuwa.

Yan kauyen kowa saizowa kallo suke suna ganemawa idonsu, Zahrah kowa har yanzu d'aki take tin jiya saidai tafito alwala takoma abincinta ma sai gwaggoce take kaimata a d'akin.

Nantake gwaggo tashiga gyaran Zahrah gyara irin na amaren fulani.

Hayat yawuce bayan sunyi sallama da kawu, amma yace zai dawo da dare gun zahrah.


#/Aufana for life❤️

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now