ZAHRAH HAYATY 19/20

29 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *19/20*
Ranar Tuesday around 6:00pm dot jirginsu yasauka a katafaren filin jirgin na birnin kebbi l/gvmnt acikin ambursawa mai suna "Ahmadu bello International airport".

Hayat,mutallab dakuma abban su ne tareda hairan k'anen hayat wanda ke binsa ne sukaje taryosu, jirgin na sauka sukafito, cikin wani irin farinciki Chief justice MATAWALLE yatinkaro iyalan nasa fuskarsa cike da tsananin farinciki.

Hayat ne yaje dasauri yarungume kakan nasa cike da farincikin ganin nasa, shima matawalle cike da tsintsar k'aunar jikan nasa yarungumesa tareda sumbatarsa a goshi.

Hayat yace "ur highly Wlcm my grandpa" shikuma yace "thank you my sweet apoky" dan haka yake kiran dika jikokinsa maza, hayat yai murmushi tareda fadin "I really miss you my apoky"  mai girma matawalle yai dariya yace "bawani, ni banyarda kayi kewata ba, tinda bazakaje ka ganni ba, nanda habuja bai wuce 40mnts ba a flyt amma saika kwashe kusan wata hud'u biyar bakaje kaganni ba, saidai ni nazo, wannan abokantakar yatake"  yak'arisa tareda shafa kan hayat d'in.

Hayat yai murmushi sannan yace "karka damu my apoky, ayyukane sukaman yawa a Company, amma very soon zankaimaka ziyara har saika gaji dani"  mai girma matawalle yai dariya yace "inajiran wannan ranar tazo".

Abba dasu mutallab ne suka k'ariso suka katse masu maganar, mutallab da hairan suna fadin "oyoyo oyoyo kakus" nan sukaje suka rungumesa shima yana rungumesu tareda sumbatarsu a goshi.

Mutallab yace "sannu da zowa mai girma alk'alin alk'alai, nasara maka" nan suka kwashe da dariya, nan shima abba yaje ya rungumesa tareda masa barka da zowa ya amsa.

Abban ra'uf ne yak'ariso "wato hisham k'anen mahaifin hayat" tareda security's din mai girma matawalle d'auke da kaya.

Cikin farinciki abba yaje suka rungume juna cike da farincikin ganin d'an uwan nasa.

Nan akashiga gaggaisawa sannan suka rankaya izowa gun dalla dallan motocinsu.

Cikin sauri aka bankama motocin wuta sukabar wurin.

Nantake suka iso birnin kebbi acikin GRA, koda suka iso tini ummi tagama shirya komai, masu aikin gidan sai hidima suke sungama gyara side d'insu tini ankuma jere dining room da kalolin abinci irin wanda mai girma matawalle keso.

Danhaka suna isowa aka gama gaisawa nan suka wuce side d'insu aka Kai masu kayansu acan.

Bayan sunyi wanka sannan suka fito, atare gaba d'aya yau sukayi dinner anatashan fira cike tsintsar farinciki, ahlan da akeelah sunmak'ale ajikin mai girma matawalle sai k'iriniya sukemasa shikwa yana dariya cike da farinciki, bayan sungama sannan aka koma babban parlor aka cigaba da shan fira.

Gaba d'aya yaudai tinda mai girma matawalle yaiso hayat da mutallab basusake fitaba, sai can kusan 9pm mutallab yafita sakamakon kiranda yasamu daga asibiti urgently.

Washe tin around 10am gida yafara cika da bak'in, gwaggo hidaya da iyalanta su muwadda dik sunzo hakama iyalan abba abubakar sunbaro side d'insu sunzo sundawo side d'in iyayen hayat dayake suma acikin gidan suke, kamar yanda nafad'a maku gidansu hayat family house ne, dakazoma tin a k'ofar get din shigowa zakagane lallai gidan babban gida ne, abban ra'uf wato hisham shine kad'ai gidansa daban, amma abba abubakar da hashim dakuma shi mai girma matawalle dik acikin gidan suke da iyalansu.

Gida yacika Masha Allah, ga y'aya kuma ga jikiki harda tattab'a kunne.

Matawalle Sai farinciki yake yaga zuriyarsa Masha Allah.
       ................

Around 3:00pm dot aka hallara babban parlon mai girma matawalle, kowa yaiso jira kawai yake a fara, abba hashim mahaifin hayat, abba hisham, mai girma matawalle dakuma gwaggo hidaya.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now