ZAHRAH HAYATY 23/24

27 1 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *23/24*
Cikin sallama ahankali yashigo cikin d'akinda amaryar tasa take a zaune, can yahangota tsakiyan gado a zaune fuskarta rufe da wani mayafi fari mai stones a jikinsa.

Wani irin farinciki ne yaji ya mamayesa sbd ganin yau burinsa yacika na mallakar abar k'aunarsa matsayin matar aure "Alhmdllh......" ya furta acikin zuciyarsa sannan  yak'arisa gunta.

Ahankali yake takonsa harya isa gunta sannan yazauna dan daita fuskarsa d'auke da yalwataccen murmushi.

D'an duk'o da kansa yai daidai fuskarta sannan yace "umm.....amaryata tasha kyau gashi sai k'amshi takeyi" murmushi tai amma batai maganaba, cigaba da magana hayat yai "umm......saidai badan wani abuba danace wannan amaryar marowaciya ce, sbd tahana angonta ganin wannan kyakkyawor fuskar tata mai haske tamkar farinwata a sararin samaniya" nanma murmushi kawai tai amma bata bude fuskarba.

Gyara zamansa yai cikin murmushi sannan yakai hannayensa yad'aga mayafin da aka rufe fuskarta dashi, yana bud'ewa saiya k'uramata fararan idanuwansa yana kallonta, itakuwa sassanyar murmushi ne a fuskar ta ahankali tad'ago dara daran idanuwanta takallesa saitaga ashe shima itad'in yake kallo.

Murmushi tai tana kallon yanda yake kallonta tamkar yaune yafara ganinta, ji tai yace "tubarakallah Masha Allah, tsalki ya tabbata ga mahaliccin wannan kyakkyawor halittar, Inak'ara godewa Allah daya bani ikon mallakar wannan halittar, inakuma rok'onsa daya bani ikon kula daita" ameeen......tafurta.

Murmushi yai sannan yakai bakinsa yasumbaci goshinta tareda furta "I love you with all my heart fatimah na" itakam murmushi kawai take har yanzu.

"Gsky fatima da ace narasaki ban aureki ba, to dana kasance acikin marasa sa'a a rayuwarsu, idan kuma hakan takasance dana kasance acikin dana sani na har abada, amma yanzukam Alhmdllh" dariya tai sannan tace "ai nafika zama mai sa'a, tinda kyakkyawan saurayi had'adde kuma tauraron duniya gaba daya yazamo mijina, Inafatar nacigaba da mallakarsa nikad'ai kuma yacigaba da zama mijina har abada, dan wlh darling broz banasan kishiya kokad'an, plss dan Allah karka k'ara aure har abada".

Wani irin yanayi yaji ya ziyarcesa jin abunda fatima tafad'a, shuru yai yakasa cemata komai yazubamata fararen idanuwansa yana kallonta kawai.

Ganin haka yasa ta tab'asa, saiyai murmushi sannan yajanyota jikinsa ya rungume kawai, murmushi tai taredayin lamo ajikinsa.

Ahankali yad'agota tareda fad'in "baby na, tashi muje muyo alwala muzo muyi sallah raka'a biyu domin nuna gdyrmu ga Allah daya nuna mana wannan ranar" toh.....tace sannan ta tashi suka fice toilet.

Atare sukayo alwalar sannan sukazo hayat yajasu sukai sallah raka'a biyun.

Bayan sungama sannan hayat yajuyo yana murmushi yace mata "baby na, bara namaka adduah a goshi, domin neman Allah yakareman ke" saitai murmushi kawai.

Nan yamatso ahankali yad'ora hanunsa na dama yamata adduarda manzon tsira yakoyar ga dik wani ango daya karantawa amaryarsa a daren tarewarsu, bayan yagama saiyace "to nagama, amma nima kiyiman ai, naki wayon"  dariya tai sannan tace "toni mezan karantama ne, bansaniba" saiyai murmushi shima.

Mik'ewa yai tsaye sannan yakai hanunsa itama yamik'arda ita tareda fadin "my baby, tashi muje parlor muci abinci koh" yamik'arda ita sannan yad'auki ledarda yazo daita saikuma yajanyo fatimar ajikinsa.

Parlor sukaje suka zauna saikuma yaje kitchen yad'akko plate da cups yazo yazubamasu kazar da fresh milk dinda yazo dasu, bayan yazubamasu saiyad'akko yazo kusa daita yazauna, nan sukafara ci ahankali suna yar fira, ganin shikadai kecin naman sosai yasa kawai yad'auketa cak yad'ora kan cinyoyinsa sannan yadinga d'aukan naman yana bata dakansa,cusa fuskarta tai a k'irjinsa alamar kunya, murmushi yai yacigaba da d'iban naman yana bata.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now