ZAHRAH HAYATY 25/26

28 2 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *25/26*
Koda suka isa kowa abunda suke tinani shinedai yafaru, a tsorace kuma a kid'ime cikin tsintsar tashin hankali hayat yaja da baya cikin firgici da tsintsar tashin hankali.

Fatima ce a tsaye idanuwanta sun firfito waje suncanja kala izowa blue, bakinta yai kaca kaca da jini hakama hannayenta dik jinine, a gefenta kuma wani yarone kwance cikin jini, a cikinsa bakomai sai jini dake fitowa da'alama dikta yashe kayan cikin yaron ta cinye.

Mutane dik sun zagayeta suna kallo.

Mutallab ma firfito da idanuwansa yai woje tareda ja da baya dasauri cikin kid'imewa, hayat yafurta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" mutallab ma hakan yafurta tareda fadin "mezan gani haka, Fatima...! wai dama baki daina aikata wannan mummunar d'abiar ba, ya Subhanallah".

Dasauri suka k'arisa wajen hayat yafincikota yadamk'ota tareda watsa mata mari nagaske, wani irin yunk'uri tai tadamk'o hanunsa zatakai baki yai saurin damk'e bakin nata yarufe da hanunsa.

Sake yunk'uri tai tacire hanun nasa tana wani irin gurnani kamar mahaukacin zaki idanuwanta suka kara firfitowa gaba daya suka koma blue.

Dasauri mutallab yazo yataimaka masa yafinciko kafafuwanta shikuma hayat yarik'e hannayenta sannan suka samu suka d'auketa suka fice cikin gida.

Nanma dasuka shiga cikin gidan a wani d'akin suka sakata suka rufe da key, koda suka rufeta haka tadinga bugun k'ofar da iya k'arfinta kamar zata fasa k'ofar haka kakejin kofar na kuka.

Hayaniyar mutanenda ke waje harma sunkusa shigowa cikin gida dan sai rigima suka da security's sai sunshigo sun d'auki fansa sunkashe fatimah.

Hakan yasa dole suka rufe fatimar acikin gidan sannan suka fito.

Nanfa akaita fafatawa tsakanin mutanen unguwa dasu hayat da security's din hayat, sufa mutanen unguwar sunce dole saisun d'auki fansa sunkashe fatima, shikuma hayat sai faman basu hkr yake.

Dakyar da sud'an goshi hayat yasamu suka daidaita da mutanen unguwar amma bisa yarjejeniyar saiya biya diyyar wannan yaron, nantake ya amince yashiga cikin gida yad'akko masu kud'i naira million biyar yabasu akaima malamin wannan yaron sbd yaron almajiri ne.

Sun nemi aje kotu gun alk'ali bayanda hayat yaiya sbd sunfishi karfi ya amince da hakan, amma daakaje gun malamin su wannan almajirin saiyace kawai akawo diyyar basai anjeba shys hayat yabada diyyar kawai.

Bayan yabada ne mutanen unguwar sukamasa kashedi akan idan tasake wlh saisunkoreshi daga unguwar kuma saisun kashe fatima, nan yamasu alk'awarin hakan bazata sake faruwaba.

Bayan komai ya daidaita sannan su hayat suka koma cikin gidan.

Yana shiga ya harhad'o dikkannin security's din gidan, rai a bace yashiga masu masifa kamar zai dakesu yana fadin "miye amfaninku kudika, a k'alla security's shida ke gidannan, to dik kuna inane harta fita batareda kunsaniba"  d'aya daga cikinsu yace "am very sorry Sir. But.....Sir wlh tasama tabi, zanje toilet ne naji motsi asama koda naduba sainahangota, harzanyi yunk'urin kiran sauran ma'aikatan kawai sainaji tawatsomin wani abun a ido, daganan bansake sanin inda nakeba har sai bayanda wannan abun yafaru".

Wani irin tsaki hayat yayi sannan yafice cikin gida batareda yasake cemasu komaiba.

Mutallab ne yacemasu "am....Is Okay.....but....dan Allah ku kula sosai kucigaba da bama gidan tsaro sosai" nan suka amsa da "Okay Sir....."  nan shima mutallab yafice ciki.

Kankaceme tini wannan lbrn yakarad'e garin birnin kebbi, gidajen radio dana talabijin dik sun d'auka sai yayatawa ake, amma anrufe sunan hayat dana fatima ba'afad'aba, kawai sai akace wai wata mayyace tazo taci yaron wacca ba'asan daga ina tazo ba.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now