ZAHRAH HAYATY 15/16

27 1 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *15/16*
Kimanin kwanan yan uwan Zahrah biyu a gidanta suna d'ebe mata kewa, hayat kowa tinda suka dakko amarya rabonsa da gidan, saidai yakira d'aya daga cikin ma'aikatanda ke gidan waya abama zahrah suyi magana.

Ahaka har suka kwashe kwana hud'u sannan sukace zasu wuce, nan Lidia d'aya daga cikin ma'aikatan takirasa tafad'amasa sunce zasu wuce, yana office yabarosa yazo.

Alkhairi yamasu sosai wanda ya rikita tinaninsu, kowacce naira dubu hamsin tareda turmin atamfa super ta kimanin naira dubu hamsin.

Dik sun kid'ime da farinciki sai faman godiya suke suna sambarka, shikwa murmushi kawai yakemasu.

Bayan sungama had'a kayansu yasaka drivers dinsa biyu sumaidasu gida, dazasu wuce kowa dakyar yacire zahrah daga jikin gwaggo hajjo sbd sai kuka takeyi sosai wai saitabisu ankoma daita, dakyar yacireta suka wuce itama gwaggon kuka take, ahakadai suka wuce.

Bayan sun wuce yarik'a hanunta suka koma ciki, rarrashinta yashigayi cikin hikima da fara'a harya samu tayi shuru amma bisa wani alk'awari dayamata wanda shikansa yasan ba'iya cikasa zaiyiba, ahakadai yasamu tayi shuru harta kwanta tayi bacci, ganin tayi bacci yasa yarufemata d'aki yafito yakoma office.

Tindaga ranar baisake komawa gidanba hartakusan cika sati d'aya da tarewa, kawaidai yabarta tareda ma'aikatanda ke gidan, suma kuma ba'anan suke kwanaba kawai aiki suke around 8:00pm kuma sufice abunsu kamar yanda suka saba.

Haka take kwana itakad'ai acikin wannan k'atoton gidan a tsorace, kullum a tsorace take kwana, saitayita kuka dik lokacinda ma'aikatanda zasu fice amma haka suke ficewa subarta cike da tausayinta sbd bayanda zasuyi, kullum dakyar takeyin bacci sbd tsoro, saita tattakure a guri d'aya tarufe idanuwanta ta k'udundune gu d'aya, ahaka har bacci yad'auketa.

Acikin wannan yanayin harta cika sati biyu da zowa tafara da kad'aici, tintana kuka yanzu harta fara sabawa tarage kukan.
       ..................

A kwance yake around 5:30pm yana latse latsen wayarsa, hairan ne yashigo dasauri wato k'anen hayat dasauri yamik'amawa hayat waya yana fad'in "yaya hayat, gwoggo ce ke magana" wato k'anwar magaifinsu hayat mahaifiyarsu mutallab 'Hidayatu'.

Danhaka dasauri yakarb'i wayar yakara a kunnensa taredayin sallama, dagacan b'angaren akafara magana zai amsa saiga mutallab yashigo danhaka yatashi yafice parlor, ko kallonsa mutallab baiyiba yad'auki abunda zai d'auka yafice.

Baidawo d'akinba har saida yagama magana sannan yadawo yashiga bathroom yatsala tsalelen wankansa yafito, fuskarsa cike da tarin farinciki da annuri yashiga shiryawa, cikin sauri yashirya acikin wata dakakkiyar shadda gizna light blue mai shek'in kyau da tsada, saikuma hularsa k'ube da cover shue dinsa masu tsada da kyau, bayan yasaka hula kuma yad'akko watch dinsa yasanya a damtsen hanunsa, saikuma tirare yafeshe jikinsa, nantake d'akin yad'auki sassanyar k'amshi mai ratsa zuciya dakuma sanyawa gangar jiki kasala.

Bayan yagama shiryawa sannan yadauki phone dinsa da key car dinsa yafice.

Yau dakansa yai driving din kansa acikin wata galleliyar motarsa bak'a wulik sai shining take, abunda yad'auki tsawon lkc baiyiba indai har da motocinsa zai fita.

Kai tsaye gidan gwaggon tasa yafice, fuskarsa cike da fara'a zuciyarsa kuma fal da tarin farinciki, ahankali yake driving dinsa yanashan kira'ar alaramma Usman b/k, ahaka harya ya'isa gidan gwaggon tasa, nan yai horn get man yabud'e masa get yashiga.

Bayan yai parking yafito nan suka gaisa da baba maigadi dakuma security's dinda ke kula da gidan sannan yafice izowa cikin gida.

Cikin sallama yashiga babban parlon gidan, dagudu munira k'aramar kanwarsu mutallab tazo tanamasa "oyoyo yayana" shima cikin farinciki yad'auketa yad'agata sama yana fadin "oyoyo my Lil sis"  gwaggo dake zaune cikin parlon tareda muwad'd'a kanwar mutallab dake binsa fara'a ta bayyana a fuskarsu da ganin d'aya tamkar ya dubu wato hayat, kamar yanda suke masa kirari.

Cikin girmamawa yazo yadurk'usa yakwashi gaisuwa gun gwaggon tasa nana tadafa kansa cikin farinciki tareda fad'in "Allah ya albarkaceka yarona" yace "ameen" tareda mik'ewa yazauna, itama muwadda cikin girmamawa da fara'a tagaidashi "Ina wuni big broz"  cikin fara'a yace "how are you my Sister"  tace "am fine yaya".

Gyara zamansa yai yana cigaba da wasa da munira.

Wasu files gwaggo ke aiki kansu, danhaka saida yajirata tagama yasha ruwa da muwadda takawomasa, bayan tagama tace yabiyota izowa parlonta.

Bayan sunshiga sun zauna saita dubesa ahankali, cikin nustuwa tafara masa magana "Hayatudeen......" takira sunansa, nan yadubeta ahankali tareda amsawa da "Na am gwaggo...".  saitacigaba da magana "hayat bazan b'oyemaka ba, kamar yanda kasani yanzinma hakane, wlh dik acikin MATAWALLE'S family babu mutum d'aya dayakesan aurenka da wannan yarinyar, Inaso kasani, bawai yarinyar ce ba'asoba illa wata d'abiace datakeda wacca kowa yasani kuma kaima kasani, wacca kuma tasamo asali tin a ainahin tsatsonta wato mahaifin kakanta, kaga kowa tinda ita datake jikar jikarsa tasamu dole itakuma acikin y'ayanta ko jikokinta su samu.

Wannan dalilin ne yasa kowa bayasan wannan had'in naku" nannauyan numfashi hayat yasauke "Hmmm.......!" sannan yadago da kansa yace "to gwaggona miye mafita a yanzu" gyara zamanta tai sannan tacigaba da magana "karka damu yarona, Insha Allah zanyi iya k'okarina domin ganin ka auri wacca zuciyarka ke So, saidai inafata kuma Ina addu'ar kar abunda mutane ke tinani akan wannan yarinyar ya tabbata har karshen zuri'arku baki d'aya"  dafe kansa hayat yai sannan yafurta "ameen ya Allah".

Numfashi yasake saukewa "Hmm......! sannan yace "dan Allah gwaggo kiyi dik yanda zakiyi kishawo kan Matawalle domin nasan shikad'ai ne babbar matsalata a yanzu" dan murmushi gwaggo tayi tace "ka kwantarda hankalinka, banasan ka d'aga hankalinka sosai kan wannan matsalar, ranar Friday insha Allah zanhad'a family meeting wanda ya kunshi harda shi matawallen kansa, and kuma dik abunda zamu tattauna acikin zaman is all about wannan issue din, kuma am very sure zanshawo kan matsalar insha Allah, sbd haka ka kwantarda hankalinka, Inaso ne ahad'e bikin naku gaba daya, naka dana d'an uwanka mutallab dakuma kanwarku humaira" wato kanwar hayat ta biyu.

Sbd haka ka kwantarda hankalinka".

Wani d'an farinciki yaji ya mamaye zuciyarsa harsaida yai murmushi, gwaggo tacigaba da fadin "gobe insha Allah zanje habuja gun matawalle zamuyi magana kamin jibi muhad'u meeting d'in".

Cikin jin dad'i hayat yace "Ok my lovely aunt, thank you soo much, I really appreciate to you, Ina sonki sosai gwaggo na" cikin k'aunar yaron nata gwaggo tace "love you too my sweetheart, karka damu farincikinku shine namu ai" yai murmushi sannan yamik'e tsaye yana fadin.

"Ok.....bara nawuce office har jibi idan kin dawo, kokuma mayi waya sbd inada nima zanje dubai gobe" gwaggo tace "ohk, Allah yakiyaye ya tsare" yace ameen.....sannan yafita.

Koda yafito su muwadda sunfita, danhaka yafice kawai.

Koda yafita office yafice, baikoma gidaba Sai kusan 12:30am, koda yakoma mutallab baidawoba danhaka yai wanka yacanja kaya kawai yakwanta abunsa.

Mutallab bai dawo gidaba Sai kusan 2:00am, koda yashigo hayat sai sharan baccin sa yake, shima wanka yai yadauro alwala yai raka'ah biyu sannan yakwanta.

Washe gari bayan sundawo daga masjid mutallab yake cewa hayat...........

Wasa farin girki......💃🤸🏻‍♀️🤩


#/Aufana for life❤️

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now