ZAHRAH HAYATY 13/14

28 3 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *13/14*
Da dare around 7:30pm hayat yakoma kauyen kambazar fulani gun Zahrah.

Koda yaje saida gwaggo tai kaman tanayi harda duka da koke koke sannanfa akasamu zahrah tafito gun hayat a k'ofar gida, kad'an tad'an d'ago kanta domin taga shin wanene acikinsu tsakanin hayat da mutallab zai aureta, tana ganin fuskarsa batasake bud'e fuskartaba harta k'arisa gunsa tazauna.

Anan k'ofar gidane aka shimfid'amasa tabarma mai tsabta yazauna yanashan fura kasancewar hayat mutum ne maisan fura da kindirmo sosai, tinda tafito kallanta kawai yai yacigaba da shan furarsa, har saida yagamashan furarsa sannan yagyara zamansa yana fuskantarta yafara mata magana cikin nustuwa.

"Zahrah....!" yakirawo sunanta, bata d'agoba bare ta amsamasa saima faman sheshekar kuka take fuskarta a rufe da hijabinta, ganin haka yasa yacigaba da magana batareda yawani damuba da ganin kukanda take "Zahrah, meyasa kike kuka ne..?" nanma batace dashi komaiba kuma bata d'agoba, saiyacigaba da maganarsa "Shin bakyasona ne...?" yasake jefamata tambayar.

Jin abunda yafad'a yasa tad'ago ahankali sannan tagyad'amasa Kai alamar Eh.....zaro idanunsa yai yafito dasu waje taredayin murmushi kamin yace "bakyasona...?" tasake gyad'a masa kai alamar Eh....murmushi yasakeyi sannan yace "to wakikeso idan bakyasona".

Sadda kanta tai k'asa sannan tace "wanine, sunansa Ahmad amma anfi saninsa da jauro" murmushi hayat yai yace "to shi jauro din yashirya aurenki ne, ma'ana yanada abun aure ayanzu" ahankali tad'ago sannan tace "yatafi cirani sai wata shekarar zai dawo amma yace dayadawo za'amana aure, kuma suma su kawu sunsani".

Gyara zamansa yai sannan yace "nikuma kinga sonda nake maki yasa Ina ganinka nakasa hkr nad'auki tsawon lkc batareda namallakeki matsayin matata ba, sbd haka zahrah, inasan ki kwantarda hankalinki, namaki alk'awari zan baki kulawa sosai, ki kwantarda hankalinki kinji".

Kallonsa kawai tai saiga waensu zafafan kwallah nabin kuncenta saikuma ta sadda kanta k'asa takauce daga kallonsa, hijab d'inta tasaka tarufe fuskarta tanacigaba da kukanta, daganan bai iyasake cemata komaiba kawai yace "tashi kije cik....." tin baiko k'arisaba tamik'e dasauri dagudu takoma cikin gida.

Kallo kawai yabita dashi harta shige.

Bayan tashiga kawu yafito yana y'an kame kame, hayat baice dashi komaiba kawai yamasa sallama yafice.

Saikusan 10pm yakoma gida, koda yaje mutallab yana side din iyayensu, danhaka shima yai wanka yacanja kaya yafice can d'in.
    ..................

Washe gari takasance Friday kuma itace ranarda za'a d'aura auren kamar yanda hayat yafad'a.

Around 2:30pm dot bayan ansakko daga masjid aka d'aura auren HAYATUDEEN HASHIM MATAWALLE da ZAHRAH MUHAMMAD ARABI akan sadaki mafi tsoka naira dubu d'ari cif lakadan ba ajalan ba.

D'aurin aurenda yasamu halartar manyan mutanen kauyen kambazar fulani ciki harda shugaban k'auyen dakuma ard'on fulanin k'auyen tareda kuma waliyyan hayat guda hud'u, waenda kuma hayarsu yad'auka yabiyasu bawai ahalinsa bane ko mahaifansa na gaske.

Bayan angama d'aurin auren aka rarraba alawa da abinci kala kala sannan aka watse, bayan angama ne waliyyan hayat suka kirasa suka fad'amasa angama komai saura kawai yaje yad'auki amaryarsa.

Wani irin farincikine ya mamayesa har saida yai murmushinda ya bayyanarda fararan hak'oransa sannan yace "Alhmdllh, burina yana gab da cika"  saikuma yamik'e tsaye yafice daga office dinsa.
         ...................

A b'angaren Zahrah kowa, gidansu a cike yake da mutane masoya yan uwa dakuma abokanan arziki, sai ci ake anakuma sha yayinda gwaggo taketa faman gyaran y'ar tata gyara irin na fulani, anmata lalle ja da sabon kitso bayanda aka wanke sumar da man shanu dakuma sauran mayuka, tayi kyau daidai gwargwado dikda itad'in dama kyakkyawace koda ba kwalliya.

Saidaifa har yanzu tak'i tabar kuka.
   ................

Hayat kowa ranar wani tsalelen wanka yad'auka yatafi gun fatimarsa sukasha fira tareda fara tsarin yanda bikinsu zai kasance sbd yafad'amata nanda k'ank'anen lokaci za'asha bikinsu, danhaka ranar fira mai dad'in gaske sukasha sannan suka rabu cike da mararin juna.

Bayan yadawo ne kuma yafara tsara yanda zai tsara komai akan aurensa da Fatimah, nantake yatsara komai har koda mutallab yashigo around 11pm yataddashi da biro da takarda yana rubuce rubuce akan lamarin, saidai harya gama abunda yake yafita baifad'amawa mutallab d'in ba abunda yake shiryawa ba.

Ahaka yagama abunsa ya tattara yasake fita, sai kusan 12:45pm yadawo, ananma bayan yadawo yacanja kaya laptop dinsa yaciro yafara aikin office, sai kusan 2am sannan yakashe laptop din yakwanta.

Sai a washe garine yake fad'amawa mutallab and'aura aurensa da zahrah a jiya, amma bazata tareba sai next week, murmushi kawai mutallab yamasa sannan yace "Allah sanya alkhairi" yace ameen......daganan baisake cewa komaiba akan zancen.
      .................

Ahaka gwaggo da kawu suka cigaba da kula da Zahrah har sati yacika kamar yanda hayat yafad'a.

Ranar juma'ah around 8:00pm drivers din hayat tareda shi hayat dakuma mutallab suka isa kauyen nasu zahrah acikin dank'ara dankaran motocinsa guda uku.

Sai kusan 9:00pm sannan suka d'akko amaryar tareda yan uwanta guda takwas na b'angaren uwa da uba, dakuma k'awayenta biyu, itadai amarya motar angonta aka sakata yayinda sauran aka sakasu a sauran motocin.

Bayan angama kwashesu sannan suka kamo hanyar garin birnin kebbi, amarya sai kuka take, shikwa angon kallonta kawai yake yana latse latsen wayarsa.

Ahaka har suka iso birnin kebbi din acikin wata kyakkyawor unguwa mara hayaniya dakuma rigima wato GRA bayan government house, nantake suka isa gidan na amarya.

Suna isowa akai horn get man yazo yabud'e get din aka shiga ciki da amarya da angonta dakuma yan uwan amaryar.

Bayan motoci suntsaya nan aka fito da amarya, yan uwan amarya kowa baki da hanci da ido suka wangare suna kallon aljannar duniya.

Nikaina dake rubutawa wangare baki nai da ido ina kallon wannan kyayataccen gidan mai masifar kyau, tin a wajen gida ma bare kuma da'alama cikin gidan yafi wajen kyau, gsky wannan gidan yahad'u matuk'a, flowers ne kala kala a shuke a cikin gidan gakuma greens carpet shimfid'e ak'asan gidan kana takawa wani ni'imtaccen sanyi naratsa cikin tafin k'afarka.

Aikwa fullo anzo burni sai zuba kauyanci ake waensu harda tab'a flowers din suke, ga flowers din angyarasu sosai sai shek'i suke suna kad'awa.

Daganan aka shiga da amarya ciki tareda sauran mutane, koda suka shiga ashe akwai masu aiki aciki mata har uku dikansu y'ammata ne.

Cikin izza hayat yamasu umarni dasushiga da amarya dakuma sauran yan uwanta aciki sannan sukula dasu, nan suka amsa da "Ok Sir" sannan sukai abinda ya umarcesu.

Sukuma drivers din suma yamasu nasu umarnin suka juya.

Nan shikuma da mutallab suka shiga motar mutallab suka fice izowa gida.

Shidai mutallab kallonsa kawai yake yama rasa mezaicemasa sbd gaba d'aya yacikasa da mamaki, ahaka har suka isa gida.

Hmm......wasan yanzufa aka fara, kawai kucigaba da bibiyata fan's🤩💃

#/Aufana for life❤️

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now