ZAHRAH HAYATY 21/22

25 2 0
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *21/22*
Bayan sungama aikin, hayat yakoma cikin gida sbd gaba d'aya yau a gajiye yake, mutallab kowa gaba d'aya wannan yarinyar zahrah tazo tatsayamasa a rai, sai tinaninta yake yana kuma matuk'ar tausaya mata, sai faman sak'a da warwara yake akanta, can kawai yatada mota yabar gidan.

Kai tsaye gidan na hayat yafice inda zahrah take, yana driving yana zuciyarsa cike da mamakin halaye da d'abiu irin na hayat, a wani b'angaren kuma tsintsar tausayin zahrah ne yaketa cikasa.

Ahaka harya isa gidan kusan 9:00pm, tini har mai gadi yarufe get sbd yasaba bamai zowa gidan, da masu aiki sunfice saiya rufe gida yai kwanciyarsa, idan hayat yazoma shine yake tashinsa kokuma yafad'amasa zaizo sai karyai saurin rufe gida, dayagama abunda yake kuma saiyafice shikuma yarufe get d'in.

Bayan yaiso yai horn sannan mai gadin yataso yabud'e masa get yashiga da motar sannan yarufe.

Ahankali jiki a sanyaye yafito nan suka gaisa da rabi'u mai gadi sannan yafice cike.

Abun mamaki, a palor yataddata kwance akan carpet dikta k'udundune gu d'aya kamar mara lfy, ahankali yai sallama saiyaga bata amsaba, danhaka yak'arisa gunta ahankali, karkarwar sanyi yaga tanayi hannayenta dika biyu tarungume cikinta tana fitarda sautin kuka kad'an kad'an.

Ganin haka yasa dasauri yadurk'usa kusa da kanta tareda kiran sunanta "Zahrah....." bata iya amsawaba sai bud'e daran daran idanuwanta kawai tai waenda suka kad'a suka canja launi daga fari zowa zajir "meke damunki, bakida lfy ne...?" yajefa mata tambayar, kai kawai tagyada masa alamar eh "Subhanallah....." yafurta sannan yace "meke damunki..?" nanma bata iyamasa maganaba sai murk'ususu data farayi.

Shuru yai yana kallonta cike da tausayi yarasa mezaimata, wani irin kuka datafashe dashi tareda fad'in "wayyo Allah na...." hakan yasashi dasauri yatallafo kanta cike da tausayi yana fad'in "Subhanallah......wai meke damunki ne zahrah..." ganin abun yana cigaba da tsananta yasa yai saurin d'aukanta sannan yakwantarda ita kan gujera, abun mamaki koda yaduba saiyaga jini dikya b'ata sket d'inda take sanye dashi, wannan ya tabbatar masa da period d'inta yazo.

Danhaka nantake yad'auki key car dinsa yafita, bayan kamar minti talatin yadawo d'auke da ledar magunguna.

Sunanta yashiga kira yana fadin "zahrah tashi ga magani kisha kinji.."  saidai takasa samun sukuni akan rad'adin zafin ciwo dakuma azabarda takeji, hakan yasa takasa amsamasa.

Shuru yai yana kallonta yanda taketa juyi tana kuka kwallah nazubar mata, wani irin tausayinta yamamaye zuciyarsa, dakyar tasamu ciwon yatsaya tai shuu tana zubda kwallah idanuwanta a rufe, ahankali yasake kiran sunanta "Zahrah....." saita bud'e idanun ta dubesa, murmushi yamata sannan yace "sannu.....tashi kisha magani zakiji sauk'i insha Allah, kinjiko sannu" ba musu kowa ta tashi a zaune ahankali, saiyaje yabud'e wani k'aramin fridge yadakko ruwa sannan yaballe magungunan yabata, nan tasha sannan tasake kwanciya.

Bayan dakamar minti uku kuma ciwon yasake dawowa tadinga murk'ususu tana juyi cikin yanayin wahala tana kuka maiban tausayi, hannayenta dafe da mararta, gaba daya tausayinta ya mamaye mutallab yarasa yanda zaiyi gashi kuma kayan jikinta diksun b'aci.

Ganin yanda kayan jikinta dik yab'aci kuma yakamata yataimaka mata tagyara jikinta sbd jikin nata ba kwari, to saidai yarasa yanda zaiyi.

Tsaye yai gaba d'aya yarasa abunyi, sbd dolene yasaka hanunsa ajikinta domin taimaka mata, amma kuma idan yatina da itafa matar aurece saikuma hakan yasakamasa tsoro da fargaba a zuci.

Bashida yanda zaiyi, iya tinaninsa yarasa dabara, danhaka kawai bayanda yaiya yarufe idanunsa sannan yad'auketa yafice toilet.

Bayan sunje toilet nan yahad'a mata ruwa masu d'umi yace "kiyi wanka idan kingama ga towel kid'aura, inazowa" saiya fice.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now