ZAHRAH HAYATY 27/28

34 2 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *27/28*
Dakyar tasamu wani lungu ta b'uya tarufe bakinta da hancinta ta toshesu sbd kar aji numfashinta, sai shesheka take boyewa, ahaka harta d'auki kusan 30mnts acikin wannan yanayin.

Gudu sosai mutallab keyi hakama hayat, acikin wani matsiyacin gudu mutallab yaiso unguwar, yana isowa yakira habiba yafad'amata yaiso, kamin tak'ariso gunsa saiga hayat shima yaiso.

Nan suka dunguma atare suka shiga unguwar domin neman zahrah d'in.

Suna cikin tafiyane hayat kefad'in "waishin mema yafito da wannan yarinyar a wannan lkcn, meya fito daita ne" kokallonsa mutallab baiyiba barema ya amsa masa.

Gudu gudu sauri sauri suka dinga tafiya, suna isowa wata hanya saisukaga tarabu gida uku danhaka suka rabu kowa yakama d'aya.

Tafiya suke a kid'ime cikin tsintsar tashin hankali, sai faman kiran sunanta suke "Zahrah....Zahrah....!" amma shuru kakeji ba zahrah ba amonta.

Almost 30mnts suka d'auka ahaka, yayinda itakuma zahrah takecan tasamu wani lungu tab'uya.

Anacikin haka kwatsam saiga mutallab daidai fuskarta tahangosa yana kiran sunanta alamar ita yake nema "Zahrah...Zahrah....kina inane kifito gani"  harta d'aga zata amsa da Na am....kwatsam saita hango d'aya daga cikin samarinda suka biyota a bayan mutallab, hanunsa rik'e da wuk'a.

Zaro idanuwanta tai cikin tsintsar tashin hankali, nan tai saurin k'ara rufe bakinta tana wani irin kuka mai tsananin tashin hankali daban tausayi.

Haka tana gani mutallab yawuce amma batada halin d'agawa tamasa mgn.

Yana wucewa shima yaron yafice batareda sunmaga junaba.

Yana wucewa tasake fashewa da kukan bak'in ciki, tana cikin yin kukan tamanta tabud'e bakinta kwatsam ashe wannan yaron baiyi nisaba yana kusa daita, yanajin sautin kukanta kowa yadawo baya, yana zowa kowa saigata durk'ushe ak'asa.

Dasauri yace "Keh...!" aikwa tanaji dasauri cikin kid'imewa tad'ago, tana ganinsa jikinta yad'auki rawa tamkar yar dambe.

Dak'arfi yafizgota yadamk'o Sumarta yajata da hanu d'aya yafice yabar wannan wurin dasuke ciki.

Wani irin azababbe kuma masifaffen zafi takeji, wani irin ihu takurma sbd azabarda takeji, ihunda tai yasa mutallab dayake kusa da layin yajiyo, hakama hayat yaji saidai shi yana nesa da lungun, nanfa aka fara yar tsere domin zowa inda sukaji ihun nata.

Suna fitowa lungun dak'arfin tsiwa yawurgarda ita tafad'i k'asa kanta yabugi dutse goshinta yafashe sai jini, ihu tasake bugawa sbd azabarda taji, waensu marika yawanketa dasu har hud'u tas....tas...tatas tas....kakeji.

Nan tasake fad'uwa k'asa, jiri yafara d'aukanta tadafe kanta, Sumarta yasake damk'owa yad'agata, hanunsa tarik'e tana wani irin kuka mai tsananin ban tausayi, murya a disashe tafara magana cikin wani irin yanayi mai cike da tsananin ban tausayi "menamaku ne kuke cutardani, menamaku ne dan Allah karku cutardani banmaku komaiba, kuyi hkr dan Allah, narok'eku" wani marin yasake wanketa dashi sannan yafara magana cikin rashin imani da rashin tausayi.

"Wato tambaya ma kike mekika mana koh..kenan harkin manta da aika aikanda kikayi koh"  tace "ni bansan mena makuba kuke cutardani, dan Allah kuyi hkr" baiko sauraretaba yasake wanketa da kyawawan marika tas...tas...tattas tas....daidai lokacin kuma mutallab yaiso wurin.

Akan idonsa waennan marikan dika suka sauka fuskar zahrah.

Jikinta yayi sanyi tagalabaita sosai ihunda takeyima takasayi sbd azaba.

Dasauri cikin izza mutallab yazo dagudu tareda kiran sunan zahrah "Zahrahhh.....!" nan shikuma yaron yawaiga, yana gadin mutallab yazaro idanuwansa ganin tabbas yasan mutallab kuma yasan wayeshi, sannan shi yaron bashine asalin wanda fatima takashewa y'ar yar uwa ba,gashi shikadaina mutallab ko kashesa zai iyayi awurin.

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now