ZAHRAH HAYATY.....9/10

40 4 1
                                    

_*ZAHRAH HAYATY_*

*By~AUFANA*

   *9/10*
Yaukam hayat dakansa ke driving danhaka sai tsala gudu yake san ransa, dama hayat shi mutum ne mai kazar kazar bayasan sanyin jiki kokad'an.

Mutallab dai kasa jurewa yai har saida yai magana "haba d'an uwa katafi ahankali mana kana driving kamar wanda zai tashi sama" murmushi yai tareda kallon mutallab yace "haba dan uwana,me kake tsoro ne hala" mutallab ya harerasa yace "acikin waye yakeda wanda yabari amatsayin magaji wanda yakeda yak'inin zai masa addu'ah bayan mutuwarsa, babu....sannan zakace bazan tsorata ba".

Murmushi hayat yai har saida fararan hakoransa suka bayyana yace "kwantarda hankalinka dan uwana, very soon zamuyi aurenmu atare insha Allah" mutallab ma yai murmushi yace "Allah yanunamana wannan ranar" hayat yace ameen.

Mutallab yasake yin murmushi tareda kallon hayat yace "to amma...idan mukai aure atare waye zai raka wani gun amaryarsa...?" yak'arisa zancen cikin yanayin fara'a sosai.

Hayat ma fara'arce ta bayyana a fuskarsa k'arara dariya mara sauti mai bayyanarda fararan hak'oransa kyawawa waenda suke a jere ta bayyana a fuskarsa yace "aikwa idan haka takasance, saidai ni nafara rakaka sannan Kai kuma ka rakani tinda kaine k'ane" dariya sosai sukai harda tafawa, sunajin dad'in firarsu.

Ahaka har suka isa kauyen su zahrah, kasancewar yanayine na damina anyi ruwa and'auke kowa yafito sai harkan gabansa yake, makiyaya sai kiwonsu suke manoma kuma suna nasu aikin na noma.

A gefen titi kuma y'ammata ne fulani da tsofaffi suna tafiya ak'asa d'auke da kwaryayan nono zasuje kasuwa sukai waensu kuma zasujene talla a gidaje.

Titi d'aya ne a k'auyen wanda shine babban titinda zai sadaka da argungu yakuma gifta izowa sokoto da dai sauransu.

Atacan gefen titin cikin y'ammata mutallab yahango zahrah tana tafiya d'auke da kwaryaye biyu akanta, kuma kamar yanda suka ganta awancan lkcn tana sanye da hijab d'inta mai girma tarufe jikinta, idanma kaganta batareda kwaryan nono akantaba bazakace ita bafulatana bace, sbd yanayinta sam baiyi kama da fulanin daji ba saidai na gida.

Dasauri mutallab yacemawa hayat "dan uwa ga zahran can zasuje tallah" nan shima hayat yaduba saikwa yahangota, murmushine ya bayyana a fuskarsa nan yataka motar yamatsa izowa kusa dasu.

Zahrah suna cikin tafiya ita da k'awayenta saisukaga galleliyar mota natinkarosu, saidai itakam tana ganin motar tagane ko suwaye, sab'anin sauran k'awayenta dasukaji tsoro suka fice dasauri sukabarta.

Itakam tsayawa tai kyam tana jiran motar tagama tsayuwa mamallakan motar sufito, saidai kuma tayi mamakin zowansu kauyen a wannan lkcn.

Dab daita motar tatsaya suka fito, mutallab ne yafara fitowa tareda fadin "sannunki yammata" tai murmushi kawai batareda ta amsaba, hayat ma yazagoya yatsaya kusa da mutallab sannan cikin murmushi yace mata "yar fillo, ajamo..." dan murmushi tai sannan tace "jam pelem...".

Hayat yasake cemata "talla zakuje ne..?" gyada masa Kai kawai tayi alamar eh, saiyace "to munhutardake da wahalan tallah, zamu siye nonon gaba daya" murmushi kawai tasakeyi batace komaiba.

Ganin haka saiya ciro kud'i a aljihunsa yak'irga naira dubu biyar yamik'a mata, ahankali tasauke nonon sannan takarb'i kud'in takirga.

Bayan takirga saita cire naira dubu biyu kacal tamik'o masa sauran dubu ukun batareda tacemasa komaiba.

Kallonta sukai sai hayat yace "kudin nonon ne, ko sunyi yawa ne?" girgiza kanta tayi alamar aa sannan ahankali cikin sassanyar murya mara rigima tace "kud'in sunyi yawa ne, dika nonon da kindirmo bazasu wuce naira dubu biyu ba" hayat da mutallab kallon juna sukai sannan hayat yace "to kid'auka kawai nabaki" girgiza masa Kai tai alamar aa sannan tace "ni bana buk'ata".

Hayat yadubeta hakama mutallab, mutallab ne yasake cewa "meyasa bakyaso, kud'i nefa"  kallon mutallab tai sannan tace "idan nakarb'a kawuna zai dakeni, kubarshi kawai dan Allah ngd sosai" tab'e baki hayat yai tareda fadar "shikenan tinda bakyaso" yamayarda abunsa aljihu.

Kallonsu tai tace "a ina zan juye maku nonon sbd Inaso nawuce gida ne" hayat yace "anan gsky bamuda inda zaki jiyemana, amma mezai hana mujecan gidanku sai asakamana a leda, dama can gidanku d'in zamuje" jin abunda yafad'a na karshe saitai saurin d'agowa ta dubesa cikin yanayin firgici da razana hade da tsoro.

Suma sunga hakan dasauri tace "mezakuyi a gidanmu" hayat yace "bakomai, kawaidai zamud'anyi wata magana ne da kawun ki" gaba d'aya maganar hayat tahargitsata ta rikitata, tsoro dikya mamayeta.

Batasake cewa komaiba amma gaba daya hankalinta baya akanta, suma kuma sun fahimci hakan sai suka kalli juna kawai.

Hayat yace "kishiga mota muwuce" dasauri tazaro dara daran fararen idanuwanta masu kama da madara tace cikin yanayin tsoro "Ehh...! aa ni zan tafi akafa" tai saurin d'aukan nononta tadora aka tawuce, ganin haka yasa suka shiga sukabi bayanta.

Tafiya suke ahankali saikuma sukaga tabi wata yar k'aramar hanya wacca mota bazata iyabinta ba, danhaka sukabi ainahin wacca suka sani.

Mutallab yadubi hayat yace "dan uwa, nifa har yanzu acikin duhu nake, kaine a daure yake, dan Allah kataimaka ka warwaremin zare da abawa, shin wace irin manufa ce kakeda akan wannan yarinyar..?" murmushi hayat yai sannan yace "dasannu ahankali zaka fahimci manufata akan Zahrah, amma a yanzu koda na fahimtarda Kai bazaka ganeba sbd kaima bakasan aurena da Fatimah".

Wani irin kallo mutallab yamawa hayat na rashin fahimta da mamaki "hmm.....! Shkn tinda bazaka fad'amin ba, nidai a kullum abunda zan kara fadama shine, karka cutarda rayuwar yarinyar mutane domin gyara taku rayuwar, wlh Allah bazai taba barinkuba matuk'ar kuka zalinceta" murmushi kawai hayat yai baisake cewa komaiba, har suka isa gidansu zahrah.

Bayan sun isa saisukayi parking suna jiranta, bayan yan mintina tafito d'auke da nonon nasu da kindirmo a leda, nan takariso ahankali cikin sallama cikin girmamawa tamik'awa hayat ya karba cikin sakin fuska.

Bayan ya karba saitacemasa "kawuna baya nan, yanacan daji yaje nema" hayat yace "Ok.....to meyasa bazaki kaimu can gunsaba" dasauri tace "zansake komawa talla ne sbd Inada sauran nono a gida, kuma gwaggona bazata bari naje koina ba har saina siyarda sauran"  hayat yace "to bawani wanda zaki saka yakaimu can din" dan shuru tai, can sannan tadago tace "bakomai, bara nayi sauri nakaiku kawai, amma bazan shiga motonku ba" gyada mata Kai hayat yai alamar Ok....nan tashiga gaba sukuma suka shiga motarsu sukabi bayanta.

Ahankali take tafiyarta cikin nutsuwa tamkar ba bafulatanar daji  ba sukuma sunabin bayanta da motarsu, saida suka Kai inda mota bazata shigaba sannan suka fito sukaci gaba da binta, ahaka har suka isa gonar ta kawunta.

Da hanu ta masu nuna da wurin sannan tace masu "dan Allah karkufadamawa kawuna nice nakawoku gunsa" hayat yai murmushi yace mata "karki damu bazai san hakanba insha Allah" nan tajuya tafice abunta, dakallo hayat yabita hartab'acema ganinsa.

Shidai mutallab d'an kallo yakoma, bayan tawuce nan suka shiga acikin gonar izowa gun kawun zahrah.

Am very sorry fam👏dajina shuru 2days, abubuwane sukadan sha gabana wlh, am sorry, ga sabon post nan yau🥰

#/Aufana for life❤️

ZAHRAH HAYATY Where stories live. Discover now