Episode 14

54 6 0
                                    


"Yaya Saleem can't we just forget about Dad coming today? These people are so kind I'm afraid kar Dad ya musu wulaƙanci duk a dalili na." Benazir ta gama rufe baki kenan Haleema ta shigo da sallama
"Wa alaykumus_salaam" Saleem da Benazir suka amsa a tare.
"Benazir i know it's hard for you, still kada ki damu da ni ko mahaifin Rayhaan duk wulaƙanci zamu shanye indai har hakan zai sa Dad ɗin ki ya saduda, we'll be alright "
Shiru kawai Benazir tayi saboda ita kaɗai ta san halin mahaifin nata.
"Aha...... You guys should get realdy and join us for breakfast" ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin fita nan suka ci karo da Rayhaan

"Good Morning Hayaaty!"

Muryar Rayhaan ya riski kunnuwanta ita ma tayi murmushi tace
"Morning dear. So tell me son..... Have you figured it out yet or do you need help figuring it out?"
"Mommmm, not yet." Ya amsa mata murya ciki_ciki yana dariya, kai ta girgiza ta ja hannunsa tace
"Let's go to your Dad tun ɗazu yake jiran ka".
A tare suka nufi hanyar ɗakin Dad suna hirar su gwanin ban sha'awa.

           *******.           *******.       *******

    Da sauri ya miƙe tsaye ganin content ɗin cikin rubutacciyar gayyatar da aka aiko masa. "If this has something to do with my daughter Benazir then i can't wait to meet whoever this is, he might have a clue where she is right now."
  Key ɗin motar sa ya ɗauka cikin hanzari kwarai ya fita yana ƙiran driver
"Wannan address ɗin nan zaka kai ni maza maza tada mota!"
Babu shiri driver ya shiga ya tada mota suka fita......

15 minutes later....

     "This Place...... This mansion..... It looks familiar i feel like I've been here before"
A cikin zuciyarsa yake wannan magana yayinda ya fito daga motar yana mai ƙare wa gidan kallo, kawar da tunanin da ya zo masa yayi da gaggawa ya bi bayan mai aikin wanda tuni ta fito tarbar sa. Fuska babu yabo ba fallasa ya shigo da sallama sannan ya nemi waje ya zauna yayinda Maid ɗin ta ce dashi "Zan sanar da su cewar ka iso". Kai kawai ya jinjina ya cigaba da ƙarewa falon kallo, daga gani ya san ba gidan ƙaramin mutum bane ganin irin ƙayatuwar gidan.
    Cikin sauri yake sauƙa daga bene yana waya, turus yayi da ya iso tsakiyar falon ya kafa wa Abdoulhameed Zayn ido shi ma baki buɗe ya miƙe yana kallon Rayhaan kamar dama chan sun san juna bakin sa na ƙoƙarin furta magana amma ya kasa.
"Hello Uncle, you must be Benazirs Father, I'm Rayhaan, actually my Dad invited you over, I'll let him know you are here. "
Kai ya jinjina in acceptance saidai ya kasa komawa ya zauna jikinsa har ɓari yake "I hope wannan ba abunda nake tunani bane........" Ya faɗa a ƙasa ƙasa kafin ya maida dubansa ga Maid ɗin da ta kawo masa refreshments yace "take it away, it's not like I'm here to party!" Kai a sunkuye ta kwashe drinks and snacks ɗin ta juya zata tafi sai tayi turus ganin Mahmoud daf da ita, ta sake sunkuyar da kai tace "he asked me to take it away."
Idanuwan Mahmoud da suka cicciko suna cikin na Abdoulhameed Zayn, ba tare da ya ɗauke dubansa ba yace "ajiye ki tafi.... Masu iya magana sun ce 'Baƙon ka Annabin ka'."

Smirking Abdoulhameed Zayn yayi ya kawar da jajayen idanuwansa daga kallon Mahmoud ba tare da yace komai ba.
Ita dai mai aiki haka ta ajiye tray ɗin hannunta ta fice daga falon daidai lokacin Su Saleem suka shigo falon suma yanda suka ga iyayen nasu a tsaye hakan suka yi turus babu wanda ya motsa sai Benazir dake ɓoyewa a bayan yayan nata har zufa ya karyo mata. Gashi kuma daga Mahmoud har Abdoulhameed Zayn babu wanda ya furta koda kalma ɗaya ce.
Da murmushi Haleema ta fito amma ganin mutumin da suke ta jiran zuwansa yasa tayi turus itama baki na karkarwa tace "Abdoulhameed?"
"Ƙwarai! Abdoulhameed! Wait wai kuna nufin ku ne zaku bani shawara a kan yanda zan yi dealing da rayuwar ƴa ta? You! Mahmoud? Toh ai zai fi min in tari mahaukaci bisa juji in nemi Shawarar sa da dai in tsaya kai ka min lectures akan rayuwar family na! Benazir is my daughter, you have no right to question duk wani decision da na yanke a kanta maci amana kawai."

Kalaman Abdoulhameed Zayn sun yi matukar ƙona zuciyar Rayhaan amma sai yayi ƙoƙarin danne zuciyar sa yace " With all due respect sir, my parents are only trying to help your daughter why so much hate and......."

"Rufa min baki Rayhaan! Bana son raini"

Mahmoud ya dakatar da Rayhaan tun bai amayar da Maganar da yayi niyyar faɗa ba nan take Rayhaan ya ja bakinsa yayi shiru yana kallon mahaifin nashi dake watsa masa harara.

"I'm sorry Dad i didn't mean to interfere it just happened."

"In dai a kan wannan yarinyar ne there's nothing left to between us, daga ranar da ta sa ƙafa ta tsallake iyakar gidana ta kuma tsallake sharruɗan dana gindaya mata a wannan ranar ne ta sa wuƙa ta datse duk wani dangantaka tsakanina da ita"
Cikin matsanancin kuka Benazir ta ce "But how can you say this Dad? I've never been against any decision you make on my behalf but getting married to a man old enough to be my grandpa, mutumin da babu wani yarinta ta da bai sani ba sannan i doubt he'll even keep me happy, i do not have an ounce of love for that man Dad. I'm sorry i know i shouldn't have ran away but that's the only Choice i have in kuma na tsaya tabbas da na yanki ticket na shiga ƙuncin rayuwa."

Wani dariyan takaici Abdoulhameed Zayn yayi sannan yace "Wow! Mahmoud Wow! Now even my daughter has started acting up like you? Zama da maɗaukin kanwa. Now she even has the audacity to look into my eyes and voice out her feelings and opinions about a decision i made in her life. Or did you brainwashed her like you did Haleema many years back?."
Rai a daƙile Mahmoud ya ce

"Enough! Abdoulhameed i can take all the insults you threw up at me but i won't tolerate you taking my wife's name to the mud don't even go there! And yes! I think I've had enough now get out of my face; and as for Benazir nan ma gidansu ne, zan riƙe ta tamkar ƴar da na haifa a cikina and I don't give a damn what you think about me now get lost!."
A fusace Abdoulhameed Zayn ya juya ko second ɗaya ba ƙara ba ya fice daga gidan yana huci.

Daga Mahmoud har Haleema watsewa sukayi daga wajen ya rage daga Rayhaan sai Saleem da Benazir waɗanda a wannan gaɓar sun kasa fahimtar komai daga al'amarin da sukayi witnessing a wajen. An barsu ne tsaye a wajen without a clue, and with minds full of questions waɗanda basu da amsar su.

"Okay....... What just happened? Can anyone explain to me abunda ya faru few moments ago?"
Rayhaan ya tambaya idanuwansa na duban su Saleem da Benazir yayinda su ma suka maƙe kafaɗa alamar basu sani ba. A tare suka nufi upstairs sai saƙe_saƙe suke yi

"Daman sun san juna ne? Were they enemies? What was all that attitude? Tabbas akwai dalilin da ya sa suke takun saƙa amma to what could that be??."

"Guys zan je in tambayi Oummi na I'm sure she knows something! "
Bai saurari amsar su ba ya juya ya nufi ƙofa bai tsaya ko ina ba sai ƙofar da zata sada shi da ɗakin Oummin sa, ya ɗaga hannu zai kwanƙwasa ƙofar sai yaga an buɗe ƙofa, kallon juna sukayi na wasu seconds kafin tace

"I know what's on your mind right now....... Rayhaan i have nothing to say to you about what happened moments ago, at least not now" tana kai nan ta wuce ta barshi tsaye a wajen baki a sake yana bin ta da kallo.......

********.        ********.       *******
Abuja....

   "Dole akwai wani abun! Idan ba haka ba babu abunda zai sa Mahmoud ya tsallake tarin ayyukan da ke kansa ya bar gari, ni bai ce min komai ba haka ma wancan koɗaɗɗiyar matar tasa..... Gaskiya ni ban yarda da wannan tafiyar tasu ba dole akwai wani abun da suke kitsa wa bayan ido na"
Shu'umin murmushi Mu'azzam yayi kafin ya dubi uwar tasa yace "yaushe aka fara sa ki a sahun mutane da har zai fara sanar da ke inda yaje ko kuma abunda zai yi?".
Harara ta watsa masa sannan ta miƙe tsaye ta dubi Mu'azzam tace  "ko ma dai menene zan gano, dukkannin mu yau ɗinnan ku shirya mu tafi Bauchin...........

XO 😘

NUR_AL_HAYATDonde viven las historias. Descúbrelo ahora