Episode 11

145 23 2
                                    

     Isowar su gida Rayhan bai bar ɗakin da Benazir take ba saida ya tabbatar Nurse ɗin tana aikin ta yanda ya kamata, a gajiye ya fito inda ya iske su Dad zaune a lounge area suna hira, ƙarasa wa yayi inda suke da sallamar sa sannan ya zauna bayan sun amsa Dad yace
"Rayhan .... I was just talking about you, actually akwai wasu properties ɗina da ke nan garin wanda kusan zance daga ni sai Mom naka ne muka san da su, actually I didn't keep them for myself, da sunan ka bisa kowanne takarda, all you have to do is sign them.."

Zaro idanuwa Rayhan yayi yana kallon Dad dake maganar ba tare da kallon inda Rayhan yake ba, irin wannan yanayin na Dad shine ke tabbatar wa Rayhan cewa he's damn serious about it kuma ba wai shawara ce ba umarni ne na dole ya amshi ownership na properties ɗin don haka kawai ya amsa da "Ok Dad".
Yanda Rayhan ya amsa a taƙaice Dad fahimci cewa ba so yake ba amma ya dake kamar ma bai ji shi ba ya cigaba da al'amuran da yake bisa wayar sa.
A hankali Rayhan ya miƙe zai bar wajen Oummin shi ta dakatar da shi

"Ina kuma zaka je? It's been a while rabon da mu zauna muyi hira only the three of us over a cup of coffee....."
Murmushi yayi hannuwan sa cikin aljihu ya maƙe kafaɗa yace

"Well.... who's in for a cup of tea?".
Da sauri suka ɗaga  hannu sama in a playful way, Rayhan yayi snapping yatsun sa yace "ku ban mintina biyar! Just five minutes!!"

Yana faɗan haka ya nufi kitchen da sauri fuskar sa ɗauke da murmushi, su ma murmushin suke yi Haleemah ta ji daɗin yanda mood ɗin sa ya chanja nan take coz the Rayhan she knows won't  easily let go without a little bit of drama.

_________

     Cike da kasala ta buɗe idanuwa tana ƙare wa ɗakin kallo kafin a hankali ta tashi zaune tana juye juye, farin wallpaper ne a ɗakin da golden design sai kayan ƙawa dake ciki, sanyin Aircon na ratsa ta har tana kame jikin ta
"where am I?"
Ta tambayi kanta "I'm not dead am i?" Da sauri ta girgiza kai ta kawar da wannan tambayar

"No.... I can't be dead...  I'm alive! But where is this place?" Tambayar da babu mai amsa mata ta sake yi wa kanta, da idanuwan ta tabi ɗakin da kallo tana neman ƙofa tayi Sa'a kuwa ta hango ƙofar daga ɓangaren ta na dama da sauri ta sauƙe ƙafafun ta ƙasa tana ƙoƙarin tashi, nurse dake gyangyaɗi tayi saurin tasowa ta riƙe Benazir tace "You need more rest Ma'am please sit, zan je na sanar da su kin tashi."

"Su? Su waye? Where is this place and who are you?".

Please relax Ma'am bari na sanar da su kin tashi" Nurse ta mayar mata da martani kafin ta nufi ƙofa Benazir ta bita da kallo har ta turo ƙofar sannan ta ce "what if she's working for my Dad? I can't trust her".

Miƙe wa tayi ta nufi gefen ƙofan ta rakaɓe chan ta hango empty kwalban khumra ajiye nan da nan ta ruga ta ɗauko tana haki ta sake rakaɓe wa a bayan ƙofar....

   " Sir patient din ta farka."

Jin kalaman nurse yasa Rayhaan saurin ajiye tray ɗin tea dake hannun shi sannan ya nufi hanyar ɗakin da sauri yayinda su Dad ke biye da shi,  a bude ya riske ƙofar don haka ya kutsa kai bai yi aune ba yaji an rafka masa duka a baya da abuda bazai iya tantance itace ne ko dutse ba nan take ya saki ƙara ya zube ƙasa yana riƙe da wajen 

Shi ya fara kutsa kai cikin ɗakin ba tare da sanin irin tanadin da Benazir tayi ba bai ankara ba yaji an rafka masa kwalba a kai, nan take ya zube bisa ƙafafuwan sa yayi saurin riƙe ƙeyar sa, da kyar ya juyo a hankali ya dubeta tsaye riƙe da kwalban a tare suka zaro idanuwa nan da nan tayi wurgi da kwalban daidai lokacin su Dad suka ƙarasa cikin ɗakin

"RAYHAN!!" Suka haɗa baki wajen ƙiran sunan sa.

"Rayhaan!!  Oh what have i done?? I'm sorry i taught that lady is working for my Dad....... "
Benazir ta faɗa cike da firgici

"And so you blindly smacked my head with that big thing of a bottle  you could have used a pillow instead or a shoe or something light!  You wicked dummy! "

Rayhaan ya bata amsa cikin tsawa muryar sa gauraye da alamun jin ciwo,  ya kasa daina kallon ta hannun sa dafe da ƙeyar sa yayinda Oummin shi ke ƙoƙarin janye hannun sa daga wajen ciwon

"Rayhan ɗauke hannun ka please,  we have to stop the bleeding".  Sai lokacin ya kawar da idanuwansa daga kan Benazir dake karkarwa ya bawa Haleemah (rayhaan's Mom)  daman treating ciwon,  tana gama naɗa masa bandage ya miƙe da kyar ya nufi ƙofar fita

"Ina kuma zaka je?  You need to sit and relax yanzu zan ƙira doctor coz you have to get checked up" Dad ya ƙarashe maganar yana buɗe contact list na wayan shi.

"I'm going to my room Dad, my shirt is stained i've got to change" ya ƙarashe maganar haɗe da watsa wa Benazir harara ita kuwa da sauri ta gimtse idanuwan ta cike da tsoro.

Kamar babu kowa cikin ɗakin haka wajen yayi tsit se shesheqar kukan Benazir Oummi tayi sauri gimtse shirun ta hanyar rungumar Benazir tana patting bayan ta,  kamar wanda aka ƙara fuel Benazir ta ƙara fashewa da kuka har numfashin ta yana yankewa.

"Ya isa haka my dear, it's okay,  bar kukan kaka ya isa, your health will deteriorate  even more, kin san baki da lafiya ko?".

"Aunty please  ba da niyya nayi ba, i taught she's working with my Dad and i only hit him because i wanted to escape please forgive me i didn't do it on purpose"

"Shhhhh..... I know dear,  i understand na san ba da niyya kika yi ba now stop crying,  listen  Rayhan yana da temper at times but you'll see he won't be angry for long besides  it's just a minor injury."

Janye jikin ta Benazir tayi a hankali tana kallon Oummin Rayhan da confusion kafin tace "Rayhan is your son right?  Then why  are you not mad at me even after hurting him,  i mean you are such a nice person Aunt,  and you are beautiful too".  Ta ƙarashe maganar with a spark in her eyes  da wide murmushi a fuskar ta.  Kai Oummi ta girgiza tana dariya kafin ta sa hannu ta shafe guntun hawayen dake reto a fuskar Benazir tace

"Yanzu nan ɗakin ki ne,  feel free kamar kina gidan ku ne nan ni zan sauƙa downstairs idan kina buƙatar wani abu do not hesitate to let me know kuma kar ki damu da Rayhan i will handle him" da murmushi Benazir ta jinjina kai kafin ta bi Oummi da kallo har ta fice daga ɗakin.

Dad ma bai ce komai ba ya bi bayan Haleema suka tafi.

,Hey there,❤️ beautiful people it's been so long! I can't believe it! So far I've managed to do an update today, you can share with me what you think about this episode on the comments section I'll be waiting!
I can't promise you another update soon but I'll try shaa. Thanks for your patience.
Don't forget to Vote 🤗🤗

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now