EPISODE 1

684 43 12
                                    

Yankari national park

Kalban Hill

      Daga inda yake tsaye yana iya kallon kaf  park d'in sassanyar iskar dake busawa  yasa shi zaro sunglasses nashi ya toshe idanun sa, ya fi k'arfin mintina sha biyar a tsaye yana  kallon kyakkyawan scene d'in.

So many mamories....... Unforgettable ones!  zuwan sa wajen ya dawo masa da precious moments na rayuwar shi da bazasu gogu ba sam daga kwakwalwar sa kuma baya tunanin zai iya mancewa da su ko kad'an,  They are his most priced moments.....

Shekaru biyar da suka wuce(5yrs Ago)

Sunrise Hill Estate , Abj.

Alhaji Mahmoud Adams Residence;
_____________

      "What!!!?, Rayhaan baya gida? Kuna nufin kuce min kun kasa controlling yaro d'an shekaru ashirin da biyar? (25yrs) me kuke yi har ya fita daga d'akin shi ? Ba ma wannan ba How comes babu wanda yaga fitar shi?"
Alhj. Mahmoud Adams ya k'arashe maganar cike da b'acin rai har jikin shi na rawa tsabar ya hassala. Maza guda biyun dake tsaye gaban shi kuwa kansu a k'asa babu wanda kuma yayi yunk'urin d'agowa se shi Alhaji Mahmoud da yaci gaba da cewa

"48 hours!! Nan da 48hours ina so in ga Rayhaan a gabana and i will not entertain any sort of excuse from the both of you! Aikin banza! Don me na yi hiring din ku? You are his bodyguards in har wani abu ya samu d'ana even if it's just a scratch i will not spare you." Ya kammala maganar yana nuna su da yatsa kafin ya yi snapping yatsun sa yace
"Go..... Get out of my sight before i......"
Tsabar takaici ma bai k'arasa maganar ba ya bisu da kallo yayinda suka nufi k'ofar fita.

"Mahmoud Ya kamata ta kwantar da hankalin ka, Rayhaan is still young and...."

"Dakata Haleemah, kada kiyi k'ok'arin b'oye laifin d'anki! He's young but ai ya san ya kamata! Ya kuma san me yake yi! Kin kuwa san irin shirye shiryen da nayi? Nan da kwana biyu fa Haleemah! in two days he will be introduced into the business world, i'm making him the CEO of my company! Amma inaaa! Bayan irin kashedi da fad'a da nayi masa ya yi sneaking ya bar gidan, can you imagine?? In har ya dawo sai na koya mishi hankali! I'll teach him a lesson"
Kasa magana Haleemah tayi tana kallon yanda yake magana rai a b'ace, yayinda ya ja jakar sa na laptop ya fice daga gidan ita kuwa binshi kawai tayi da kallo har ya b'ace  sannan ta juya jiki a sanyaye ta nufi sashen ta .......

__________

     Alhaji Mahmoud Adams, a well known business tycoon and industrialist, Hamshak'in mai kud'i ne kuma Humanitarian, ya kasance yana da Mata biyu, Haleemah wanda ta kasance matar sa ta fari, da kuma Zainab,
Ya Auri Haleemah tun tana da shekaru sha bakwai, shekaru goma ta shafe kafin Allah ya azurta ta da d'a namiji  RAYHAAN,  ya auri matar sa ta biyu Zainab tun kafin a haifi Rayhaan kuma ta zo gidan da d'an ta guda d'aya Mu'azzam, wanda a yanzu haka ya baiwa Rayhaan shekaru biyu, bata samu haihuwa da Mahmoud ba sai bayan Rayhaan ya shekara goma, a tak'aice dai ta haifi y'a mace Ruqayyah.

Family ne mai cike da twists, drama na safe daban na dare daban musamman idan Rayhaan, Mu'azzam da Ruqayyah sun had'u domin ko kusa babu jituwa tsakanin su
  Mu'azzam ya kasance very cunning, ga munafurci, kullum fuskar sa d'auke take da shu'umin murmushi, bak'i ne da faffad'an k'irji ga huge biceps, kullum yana Gym a tak'aice dai he's the bodybuilder kind of a guy.
Rukayyah kuwa kaf gidan she's the most annoying person, ga gulma ga had'a guri, abunda taga dama shi take yi, kullum tana takun sak'a da Mahaifiyar Rayhaan ta takura mata sam Haleemah bata da sakat a gidan komai take yi suna kallon shi tamkar a madubi! Tun abun na damun Haleemah har ya daina d'aga mata hankali ita a yanzu babu abunda ta sa a gaba illa taga farin cikin d'anta guda d'aya Rayhaan, Alk'awari ne ta d'auka bazata bari d'anta ya wulak'anta saboda Zainab da yaranta ba.

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now