Episode 7

159 20 2
                                    

    "Hey! Wake up! Lokacin sallah yayi...."

Da kyar ta iya buɗe ido, idan ta ita ne barcin zata cigaba da yi amma dole tayi sallar asubahi, don haka ta miƙe a hankali ta fita daga d'akin. Kamar Rayhan itama kasa shiga bayin tayi saboda rashin tsaftar sa haka ta faki ido ta zagaya ta baya don yin ɗahara bayan tayi alwala ne ta koma domin gabatar da sallar asubahi, ta jima bisa darduman tana tuna abunda ya faru jiya, tamkar a duniyar mafarki haka take jin kanta, tana tuna yanda take tashi da jin Muryar Ummin ta da Ayeesha, it's funny how everything changed in just a day.

  Tayi nisa cikin tunanin ta bata ma san Rayhan na tsaye jikin ƙofar yana kallon ta ba, haka kawai yake ji he needs to stay by her side no matter what happens, to keep her happy. Da sauri ya kawar da tunanin da yake yace "idan kin gama ki shirya, if possible ki sauya waɗannan kayan naki coz in kika shiga cikin gari dasu maybe mutanen Dad naki will notice, don ina tabbata zaton they might be looking for you yanzun haka".

Kai ta jinjina kafin tace "ok."
Ficewa yayi ya bar ɗakin riƙe da jakar shi. Da sauri ta cire kayan jikinta ta sauya wani itama de doguwar rigar ne royal blue mai dogon hannu sai baƙin mayafi da tayi rolling da shi, feshe jikinta tayi da turare sosai Saboda batayi wanka ba, wannan shine karo na farko da ta kwanta ba wanka ta tashi ba tare da yin wanka ba, kayan da ta cire kuwa nan ta bar musu a cikin ɗakin ta fito, ƙarfe bakwai daidai motar ta iso cike da kayan lambu a bayanta, se bench guda biyu dake fuskantar juna,godiya sukayi wa mai gari sannan sukayi sallama,  gefe guda ma'aikatan guda huɗu ne suka zauna tare da Rayhan gefe guda kuma Benazir ce zaune ita kaɗai, yayinda mazan ke hirar su ita kam ido ta zuba musu kafin daga bisani ta ciro wayar ta tana danna wa, duk abunda take kallon ta yake yi ya fahimci she's uncomfortable don haka ya dawo gefen ta, kallon shi tayi da murmushi kafin a tare suka maida duban su ga kyakkyawan scenery da suke wucewa, garin a lumshe ga alamar hadari, da sauri ya zaro cameran shi ya fara ɗaukan hotuna bai damu da tafiyar motar ba kasancewar hanyar a shimfiɗe take babu gargada.
"Oh masha Allah! Camera!! Please teach me how to use it Mr Man".

Yanda tayi maganar tamkar yaron da yaga lollipop ko ice cream yasa shi dariya kafin ya miƙa mata yace "Sure why not?".
Haka suka dinga ɗaukar hotuna kamar mahaukata idan ka gansu zakayi tsammanin sun san juna da daɗewa that moment Rayhan yayi iyakar ƙoƙarin yaga bata fara tunanin gida ba, domin kukanta na jiya ya tsuma shi sosai. Da sauri ya maida cameran cikin jakar sa sanadiyyar ruwan sama da ya tsinko.
  "Wow Mr Man! It feels like I'm in a romantic movie running away from villains and all".
Wani guntun dariya ya saka kafin ya kalleta yace "Romantic movie?".
Dariya tayi ta juya kai ta cigaba da taran ruwan da hannunta tana wasa da shi, dukkanin su babu wanda ya damu da yanda sukayi sharkaf da ruwa surutun ta kawai ake ji apart from sautin ruwa dake sauƙa, shidai Rayhan nashi dariya ne kawai kallon ta baya isar sa, she's too cute.

_________

   "Sir...... actually..... Mun yi tracking motar Rayhan, the thing is motar tayi crashing, mun samu motar a gefen hanya cikin duhuwan bishiyoyi seems like Rayhan was involved in an accident and......."

Bai ƙarasa maganar ba Mahmoud ya miƙe daga zaunen da yake yace "WHAT?!!!...... And Rayhan? Me ya same shi? Ina yake? Is he alright? How's my SON??."
Har rawar jiki yake tsabar hankalin shi a tashe yake
"Ga dukkan alamu motan nan crashed since yesterday, babu mutane a wajen ballantana muyi tambaya but tunda garin dake gaba Bauchi ne maybe zamu samu wani labari akan Mr Rayhan soon, tunda accident ne zamu fara enquiring hospitals maybe a same shi a chan."

Wani zufa ne ya karyo masa babu shiri ya fice daga office nashi yana ƙoƙarin dialing wata numba "Hello.... Yaushe ne next flight to Bauchi? Ina son kayi min booking flight just check and let me know".
Motar sa ya shiga yace da driver "take me home".
Hanyar gida driver ya ɗauka bai tsaya ko ina ba sai daf entrance na gidan, ba kamar kullum ba yau ko jiran a buɗe masa ƙofa bai yi ba kawai ya fice zuwa cikin gida.
   Tun daga shigowar sa ta hango shi amma bata wani kulashi ba sai ma yamutsa fuska da tayi kafin tace
"Na tabbata yanzu akan wancan yaron ya shigo kamar mahaukaci, ai kaɗan ma ka gani ni da ma ɓacewa yayi har abada da sai nafi samun sukuni". Tayi tsaki ta cigaba da kallon da take yi.
"What happened? Ya na ganka haka? Wani abu ya faru ne, yau ka dawo da wuri i hope you are okay?".

Kai ya jinjina yace "Yes I'm okay, ina so zan ɗan yi tafiya zuwa Bauchi, it's urgent, haɗa min kaya na...... No go get me a glass of water".
"Toh" kawai tace sannan ta fice domin kawo mishi ruwan.

"Sir Flight zai tashi in two hours time"
"Ok thank you sai na zo"
Rayhan i hope nothing happened to you my son? Ya ilahy keep  him safe."

Zame wa glass ɗin ruwan yayi daga hannun ta nan take ya fashe, ƙarar ne yasa yayi saurin juyowa yana kallon ta "Haleemah?".
Ya ƙira sunan ta sannan ya dubi sasassun glass ɗin da take ƙoƙarin bi ta kai da sauri ya dakatar da ita yana faɗin "hankali......  Zaki taka glasses ɗin nan"
"I don't care about the galsses Abban Rayhan just tell me my son is alright? Are you going to Bauchi because of him? What happened to him? Take me with you please, ko da baka tafi da ni ba zan je da kaina but you can't stop me!".
Kai ya jinjina yace "ok! Relaax, zan tafi dake but right now i can't answer all your question, go and pack your bag nan da awa biyu jirgin zai tashi." Ji tayi two hours ɗin ma yayi yawa domin ko kurɓan ruwa ta kasa yi.....

____________

Bauchi state.

      A bakin titi aka sauƙe su suka yi godiya motar ta tafi, Benazir goye da jakarta ta sauƙe ajiyar zuci tace " Sooo.... This is it? Ina ka nufa?" Ta ƙarashe tambayar zuciyar ta na bugu da ƙarfi don tasan bata da wajen zuwa Allah Allah take yace baida wajen zuwa at least zai kasance tare da ita. Kai ya girgiza yace
"Yeah. That's it! We're here in Bauchi, actually muna da gida a nan garin so I'm heading over there, na gaji sosai, thanks to you".
Murmushi tayi kawai ta ɗauke dubanta daga kanshi tace "thank you for helping me out duk da troubles ɗin da nayi causing maka, i am really grateful". Kai ya jinjina kawai yayinda wani guntun murmushi ya bayyana bisa laɓɓan sa.

Wata baƙar mota Mercedes ce tayi parking a gaban shi, don cike da fara'a ya fito yana kallon Rayhan
"Sir...... Barka da zuwa! Ya kake tsaye a nan? Ina motar taka?".
"Dawood..... Barka dai, motar ta lalace ne a hanya, ya kake ya kwana biyu? Ina ka nufa?"
"Sir dama motar na kai gyara duk sun kwana biyu a zaune babu mai hawan su, gida na nufa yanzu muje in kai ka, na tabbata ka gaji sosai".
Kallon Benazir Rayhan yayi kafin yace "You can come with us, sai in yi dropping naki a masauƙin ki. Kai ta girgiza tace "a'a Nagode I'll manage"

"Are you sure?" Ya tambaye ta.
Kai ta jinjina da murmushi tace "yes"
Har zai shiga mota ta ce
"Hey Mr Man! At least give me your number in bazaka faɗa min sunan ka ba. Dariya yayi ya dawo daf da ita ya amshi wayar ta ya yi dalilin numbar shi sannan ya juya zuwa motar saida ya shiga ya rufe ƙofa ita ma ta juya zata bar wajen taji muryar sa
"Rayhan...... My name is Rayhan".

Dariya tayi kafin ta juyo suka haɗa ido ta ɗaga masa hannu shima yayi waving back sannan ya mayar da kansa cikin motar yana ajiyar numfashi....

    "Mashaa Allah Dawood! Gidan nan ko kaɗan bai sauya ba kayi ƙoƙari wajen managing gidan I can't believe it's been two years rabona da Bauchi state and nothing has changed since then."
Dariya Dawood yayi yana sosa ƙeya da alama yana jin daɗin yabon da Rayhan ke yi masa.
"Ni zan shiga ciki in ɗan huta anjima kaɗan zan shiga gari coz i have a lot of things to do".
"Ok Sir sai ka fito ɗin". Dawood ya bashi amsa kafin ya miƙa masa jakar sa ya tafi.

******.   ******  ******

    Phone nata ta ciro daga jakar sannan ta fara browsing hotels in Bauchi, nan da nan search engine ya bazo mata sunayen hotels har ma da location a  Google map hakan yasa ta zaɓi mafi kusa da inda take don ita buƙatar ta kawai ta samu inda zata huta daga baya se ta san abun yi. Taxi ta tare ya kaita har Bakin hotel ɗin kai tsaye ta ƙarasa reception inda tayi booking ɗaki, sunanta da akayi entering a computer yasa receptionist ɗin ɗago kai tana  kallon ta, ita dai Benazir signing tayi ta ƙara gaba yayinda ɗaya daga cikin ma'aikatan ke biye da ita riƙe da jakar ta da kuma key ɗin ɗakin.

"Ma'am this is your room and here's the key, if you need anything just call enjoy your stay at our hotel".

Murmushi tayi ta karɓi key ɗin ita kuma ta ajiye jakar ta fita, Benazir kwata kwata hankalin ta bai wani kwanta ba ta daɗe tana bin ɗakin da kallo babu abunda babu a ciki ga tafkeken window wanda daga nan zaka iya ganin harabar Hotel ɗin. Langaɓar da kai tayi ta nufi gado ta ɗan kwanta, cikin ta ya fara ruri don haka ta tashi zaune tana shafar cikin nata tana haɗe rai.
Waya ta ɗauka tayi ordan abinci sannan ta shiga yin wanka.......

   

#vote 🙏

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now