Episode 3

214 19 2
                                    


    Abdoul_Hameed Zain  ya kasance  hamshaqin mai kud'i kuma ɗan kasuwa, burin kowanne ɗan kasuwa ne yaga a koda yaushe dukiyar sa na hab'aka, wasu sukan samu hakan ta halattacciyar hanya wasu kuwa ta qazantacciya, amma b'angaren Abdoul Hameed lamarin ba haka yake ba, he is the kind of man who is ready to ruin his daughters happiness for his business's sake. Bai damu kuwa da shekarun abokin harkar sa ba da kuma k'ank'antar y'ar sa ba a wajen sa it's all a game a ticket to get him more money!!

  Aminatou ta kasance mahaifiyar Su Benazir kuma mata d'aya tilo ga Abdoul Hameed, kamar de yanda ake ƙoƙarin yiwa Benazir auren dole haka ita ma ta shigo gidan shi, ba ƙaramin gwagwarmaya aka sha ba kafin ta miƙa wuya ta hak'ura, yau shekaru ashirin da shida da auren su, ɗan ta na fari Saleem d'an shekara ashirin da huɗu yanzu haka baya ƙasar yana karatu a Uk sai Hafeez wanda kwata kwata shekarun sa ashirin ne, Benazir itace ta uku shekarunta sha takwas ne kachal sannan  Wanda ke da shekaru sha shida, Hanan is fifteen years old Ayeesha kuma shekarun ta takwas.

  Benazir ta kasance yarinya ce mai surutu, ga tsokana, she's very carefree and a trouble maker, saidai tana son freedom d'in ta she loves adventures, shiyasa yawancin kawayen ta suke ganin she's crazy, amma ita ko a jikin ta. Domin a ganin ta idan zamanta crazy zai sa wasu Happiness toh zata kasance a haka har ƙarshen rayuwar ta!".

    Yau shekaru takwas kenan da jituwa ta ƙare tsakanin Aminatou da mijinta Abdoul Hameed, tun lokacin da ta fahimci cewa yana tarayya da wata matar a waje wanda ba matarsa ta sunna ba, Daga ita se shi suka san wannan Magana tuni ya gama fita daga ranta tana zama ne kawai saboda yaranta, tunda abun ya faru kuwa yau shekaru takwas ko d'akinta ba samu zarrar takawa ba saboda bashi da courage na fuskantar ta ga kuma  kunyarta da yake ji, they are only hunsband and wife a idon jama'a da kuma yaran su. Aminatou tayi.
  Abunda ya k'ara angiza wutar k'iyayyar da ke tsakaninsu ma saida Ya kawo Ayeesha gidan tun tana y'ar jinjira kwanan ta d'aya a duniya, a nan ma saida aka buga drama kafin ta Amince a bar Ayeesha a gidan, shima dai domin ta san babu Laifin baby Ayeesha a cikin abunda ya faru, infact she's also a victim, ta amshe ta da hannu bibbiyu kuma ta bata k'auna da kulawa kamar yanda ta bawa nata yaran, ko yaran basu san gaskiyar asalin wacece Ayeesha ba a wajen su adopting d'in ta aka yi kuma sosai suke nuna mata k'auna......
Kamar yanda kuka sani ko wanne ahali na da nasu sirrikan, masu iya magana sukace *"all that glitters is not gold"*

______________

     Sultan Road

Waje ya samu yayi parking motar shi sannan ya fito  yana k'arewa wajen kallo.
  Da sauri ya tsallaka titin ya shiga Hadiza wani plaza dake tsallaken, daidai lokacin ne Hafeez yayi parking motar sa daf ga da na Rayhaan zai siyo ma Benazir ruwa, fitowar sa kenan ya hango motar yaran Dad d'in shi sun danno kai ta yanda baya tsammani, jikin sa ya d'au b'ari ya lek'o cikin motar da sauri
"Benazir!!! Gasu nan zuwa get out! Hide somewhere!!!"
Da sauri ta fito rungume da jakar ta har zufa ya fara gangaro mata, tayi imagining yanda mahaifinta ya zai yi da ita in dai har ta shiga hannu shima Hafeez yasan in dai aka fahimci shi ya tseratar da ita toh lallai kashin sa ya bushe.
A lokacin tunani ɗaya ne kawai yazo kanshi, da gudu ya fisgo hannun ta ya hankad'a ta jikin motar da ke ajiye a gaban nashi. Ita kuma sai ta gwada Sa'ar ta ta hanyar ƙoƙarin buɗe K'ofar ga, mamakin ta  sai k'ofar ta bude batayi wata_wata ba ta faɗa cikin motar ta rufe k'ofar sannan ta kwanta tsakanin kujerun, sa'ar ta guda Motar tinted windows ne da ita.

    Yanayin parking d'in da sukayi ma kaɗai ya isa nuna suna zargin Hafeez amma duk da irin tsoron da yake ji bai wani bari ya bayyana ba ya tsaya kallon su kafin yace "what? What's all this? Wani abu ya faru ne? What are you guys doing here?"
Yayi tambayoyin ne ɗaya bayan ɗaya ba tare da ya nuna damuwa ba ko girgiza.

"Miss Benazir ita muke nema....... Perhaps kana da masaniyar inda take, ko ma dai kuna tare ne?"
Ɗaya daga cikin su ya jefo tambayar fuskar sa babu annuri ko kaɗan.

"What? Me kuke nufi? Benazir ta b'ata? How? I mean wasn't she locked up in her  her room, wanne hanya tabi we've got to hurry!!! My sister might be in trouble! Let's go and look for her!!"

Hakan da yayi ne yasa suka gamsu bai san da maganar ba, motar su ya shiga ya bar nashi a wajen saboda idan sun bar wajen Benazir zata fito, har suka bar wajen idanuwan shi na kan motar da Benazir ta shiga, idanuwan sa cike da kwalla.

    Tana d'agowa kenan taji an buɗe motar da take ciki hakan yasa tayi saurin komawa tayi lamo a ciki yayinda ya shigo ya zauna, shopping bags d'in hannun shi ya jefo bayan motar ba tare da juyowa ba ya kunna motar shi ya fara tuk'i........

*****.      *******.    *****

    A yini ɗaya kachal na ga rayuwata a gaban idona tamkar wani mafarki, labarun da nake gani a TV da social media  today the same thing is happening to me! I'm a runaway Bride, today I'm running away to save myself from my very own father....... Leaving my home, my family, everything that I've ever loved sannan ban san irin trouble d'in da zan jefa Yan uwana ba indai aka gano cewa  da hannun su a taimaka min. I'm not even sure where to go, ina zan nufa? Yanzu na tsira cikin motar nan, gaba kuma ina zan shiga? Motar wa na faɗa? Idan kuma ya ganni fa??
  Waɗannan tunanunnuka su suka dabaibaye min ƙwaƙwalwa nayi zurfi cikin tunani ban ankara ba naji ƙarar buɗe k'ofa, hakan ya dawo dani daga duniyar tunanin da na shiga......

Farar T-shirt nashi kawai nake iya gani sai kuma gefen hannunshi da lokaci lokaci yake sauk'e wa daga stiring wheel d'in, i realized the car was moving, ban san inda muka nufa ba , abunda na sani kawai shine ba ƙaramin tafiya muka yi ba, sanyin Air_con  ne ya ratsa ni ga soft romantic song dake tashi ban san lokacin da na fara barci ba........
   Tsananin yunwa ne ya sa ta bud'e ido cikin ta yana ƙara sai ware idanuwa take gashi ɓangaren da ta kwanta duk yayi tsami ga matsi, tashi tayi a hankali zata sauya b'arin da take kwanciya  kwatsam sai Rayhaan ya ɗago ya kalli mirror  dukkanin su suka sa ihu a tsorace bai san lokacin da yayi loosing control na  motar ba bai ankara ba sai ji yayi motar ta bar kan titin ta shiga daji inda ta haɗu da wata Bishiya, tuni komai yayi tsit a wajen sai hayak'i da ya turnuk'e na wasu mintina kafin ya washe.

   Buɗe K'ofar yayi ya fita daga motar yana murza goshin sa, yayinda itama ta fito sai fama take da uwar dogon riga ga wata abaya da ta d'aura a saman, hannunta ɗaya kuma ta dafe kanta.
  

"Kayi hauka ne?..... Haka ake tuk'i a garin ku??"

Kalmar da ta fara furta wa kenan idanuwan ta cikin nashi. Rayhaan da tuni mamaki ya cika shi yace

"What?..... Wait! Who the heck are you? Me ma kike yi a mota na sannan ta yaya kika shiga? I mean were you inside all this while? Are you even human?".
Tab'e baki tayi ta sake rigar nata data riƙe kafin tace
"It doesn't matter ko ni wacece...... Ka bar motar ka a buɗe, saboda haka kar ka wani ga laifi na, Yunwa nake ji baka da wani abun ci ne haka??".

Gaba-daya tayi confusing nashi ya ma rasa me zai ce mata kawai ya nad'e hannu a k'irji yana ganin ikon Allah. Kai ta kutsa cikin motar ta ɓangare driver ta janyo wata leda cike da snacks ta fito, buɗe wa tayi tana kallon abubuwan dake ciki kafin tace

"Unbelievable! Baka sayo chocolate chip cookies ba, too bad that's my favorite! Hahahah! Kai kam na musamman ne gaskiya, who would eat samosas bayan ga meat pie??" Bud'e ledar tayi ta d'auko meat pie guda ɗaya ta cire foil paper d'in ta fara ci har da lumshe ido, Hakan ba ƙaramin k'ular da Rayhaan yayi ba yana kuma mamakin boldness d'in ta.

"Wai me yake faruwa ne a nan? Wacece ke?.... Are you crazy?...…. Dalilin ki dubi halin da mota na yake ciki, but ke ta cikin ki ma kike, How did you even end up in my car? Shin ke mutum ce ma kuwa???...."

Hannu ta d'aga mishi alamar (ya dakata) tana ƙoƙarin had'iye pie d'in dake bakin ta. Da kyar ta buɗe baki  tace
"Ruwa!.... I need water."
Sakar baki yayi yana kallon ta daga bisani ya tura mata aniyar ta ya kutsa kai cikin motar ya d'auko roban ruwa ya miƙa mata, domin shi buƙatar shi kawai ta bashi amsoshin tambayoyin da yayi mata, karb'a tayi ta sha iya shan ta sannan ta ajiye roban a saman motar ta juyo tana k'are masa kallo kafin tace

"You are such a gentleman.... Fine yanzu zaka iya tambaya na koma wanne irin question kake da shi just ask."

"Kaji wani Rainin wayo!!"
Rayhaan bai san lokacin da waɗannan kalaman suka fito daga bakin shi ba  tsabar takaici. "wato ma duk tambayoyin da nayi mata bata ji ba take so tace?  Lallai wannan yarinyar akwai rainin hankali! What does she think of herself? "

Pls vote vote vote
Luv u all😘😘

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now