Episode 15

45 7 0
                                    


        "Ni fa ban ganewa tafiyar wannan matar da Mahmoud ba, dole akwai abunda suke shuka wa a Bauchi, kwanaki nawa amma babu wanda ya waiwaye mu? Saboda haka duk ku shirya muma muje Bauchin idan yaso koma me zai faru ya zama a kan idon mu ne domin hankali na sam ba a kwance yake ba" Zainab ta sake nanata maganar tana miƙewa tsaye tsabar baƙin cikin da ta sa a ranta.

Jinjina kai Mu'azzam yayi bayan ya gama sauraren maganar Mahaifiyar tasa sannan yace

"Nima nayi tunanin hakan, yanzu kuwa zan sa ayi mana booking flights zuwa Bauchin domin Rayhaan is not someone i would underestimate na tabbata akwai dalilin zamansu a chan kuma ko ma menene zan gano"

Cije leɓe Zainab tayi tana dariya ta fice daga falo ta bar Mu'azzam fuska a daƙile...........

*************.      **************

      "Rayhaan right now i don't have anything to tell you, all i know is that Mahaifin ka da Mahaifin Benazir were once friends....... A'a, Abokantakar su ta wuce haka, tamkar ƴan uwa haka suke, they grew up Orphans basu da kowa amma shaƙuwar su ta kasance tamkar na ƴan uwan da suka fito ciki ɗaya."

Cike da mamaki Rayhaan ya gyara zama yace

"But Oummi, in har kamar haka kika kwatanta Abokantakar su  why do i see raging anger and hatred for one another in their eyes? They couldn't even stand each other for a minute, I'm confused".

"Time and circumstances can make people do anything Rayhaan,"

Dad ya faɗa yana mai ƙarasowa cikin garden ɗin ya samu waje bisa darduman da suke zaune shima ya zauna.

Na san dukkanin ku mun saka ku a confusion, Benazir, Rayhaan, Saleem........ Today I'll tell you the reason Abdoulhameed Zayn couldn't stand seeing me let alone talking to me, despite being a brother and friend to me, zan sanar da ku dalilin da ya sa so da zumunci suka gushe tsakanin ni da shi....."

Benazir ta dubi Saleem sannan suka dubi Dad sun ƙagu su ji dalilin warware wa na Abokantakar su.

     "Ni da mahaifin ku Abdoulhameed  mun taso a tare tun muna yara, daga ni har shi mun tashi cikin maraici tamkar almajirai haka muke yawo cikin unguwa cike da rashin gata, a wannan lokacin da shekaru irin namu kamata yayi ace muna makaranta amma saboda rashin tsayayye haka muka zauna barkatai bamu da aiki se yawo da tsokana.... Though it's normal for kids our age those days. On weekdays we'd sneak into one of the classes na  Makarantar gwamnati dake unguwar mu saboda yanda muke tsananin son mu yi karatu, tun ana korar mu da baki har malaman suka fara using force amma sam hakan baya hana mu dawowa kashegari, duk lokacin da aka kora mu waje zamu koma ta window mu tsaya muna sauraren abunda ake koyarwa wani ikon Allah kuma sai ya zamana we're the only ones serious about learning.....

A taƙaice dai komai tare muke yi  sedai wajen kwana ke raba mu, domin Abdoulhameed yana tare ne da kakar sa ta ɓangaren uwa, ni kuwa ina tare da wan mahaifina da matarsa sedai babu wanda ya damu da yaya na tashi, na ci abinci? A ina nake, ko da kuwa zan kai tsakiyar dare ban dawo ba babu wanda zai damu, in har bani da lafiya haka zan yi ta yawo da jinya a jikina abunka da yaro har Allah yayi ikonsa na warke, bani da iko da komai na gidan se abunda yaran su ke so, haka na zama tamkar tsakuwa a tsakanin lu'ulu'u.

  Ku yanzu rayuwar ku a sauƙaƙe take, kun taso cikin  kulawar iyayen ku, ga ilimin addini da Western Education bugu da kari kun taso cikin daula rayuwar ku is an interesting one.....

     Wata  rana  lokacin mulkin Governor Alqasseem Garba, ya kawo ziyara garin da muke daidai lokacin malaman nan suna korar mu, mu kuma muka tirje dole sai mun yi karatu kamar dai kullum,  aka yi Sa'a komai ya faru ne a kan idonsa, daga nan ne ni da Abdoulhameed muka samu scholarship har na tsawon lokacin da zamu kammala karatun secondary school, sedai makarantar da muka samu  a Garin Kano take, hakan didn't come as a shock to us ni da shi mun yi murna sosai ganin yanda gwamnati ta ɗauki nayin komai har uniforms da takardu da kuma tufafi.

   Within those years of schooling and living in a different environment, we've learned the most important lessons in life. Bahaushe ya ce "Babu maraya sai rago"

Bayan mun tashi daga makaranta zamu shigo gari mu nemi aikin yi, ko mu shiga kasuwa muyi dako at that age we should be worried about what we'll become when we grew up but all we are worried about those days is "ina zan samu abinci?  Sabulun wanki da na wanka, etc"

Since abincin dining baya wani isar mu, abunka da makarantar maza.

  Life was hard but Alhamdulillah muna da ƙarfin mu kuma muna cikin tashen mu, Abdoulhameed ya kasance mutum ne wanda idan ya samu kuɗi kawai zai kashe su ne ya bi ta kansu babu wani plan though i don't blame him, yanayin rayuwar ce ta kawo haka, yayinda ni kuwa i believe in savings, bazan hana kaina ci ba sannan bazan cinye duk kuɗin ba har sai na ajiye wani abun domin gaba, wasa wasa muka gama secondary school, a wannan lokacin Abdoulhameed yayi niyyar tsayawa da karatu amma na tirje sai mun cigaba da karatu  saboda mu huce takaicin rayuwa, hakan kuwa akayi bayan result ɗin mu ya fito we've got good grades sunayen mu suna cikin jerin sunayen da suka samu scholarship zuwa England karatu, irin wannan luck ɗin ba kullum ake samu ba. A tare muka karanci Business Management a nan University of Birmingham."

    " We were the best of friends but then.........."

Rayhaan ya gyara zama cike da curiosity yace "But then what?"

Murmushi Dad yayi yace "let's pray Asr first...... In yaso sai in sanar da ku makasudin taɓarɓarewar zumunci da Abokantakar mu ni da Abdoulhameed."............

Ga wannan guntun page ɗin please manage with it. I'll update soon ( In sha Allah).
Pls don't forget to vote and I'll be waiting for your comments. ❤️

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now