Episode 17

46 8 0
                                    

      Cikin gaggawa ya shiga wanka ya fito bai wani tsaya ɓata lokaci ba ya shirya tsaf cikin ƙananan kaya,  ya ɗauka wayar shi ya fice daga ɗakin bai ko damu da rufe ƙofar ba, da sauri ya nufi ɗakin Mahmoud inda ya tarar shima ya shirya riƙe da briefcase yana waya. Ganin Rayhaan yasa shi katse wayar yace

"Yawwa ka shirya ko? Let's go".
Briefcase ɗin Rayhaan ya karɓa yana biye da Dad har suka fita zuwa living room inda Haleema ke zaune tana karatu, ajiye littafin  tayi a  gefe ta bi su da kallo har suka ƙaraso

"Har kun fito? That was fast.?"

Murmushi Mahmoud yayi sannan yace
"Is that so? Well, in that case se ki tashi muje tare this way you wouldn't miss me nor Rayhaan."
Nan ta bushe da dariya tace "and who will stay with my daughter Benazir? Kuje abinku, Allah ya bada Sa'a just don't be late for dinner and take care. Rayhaan...."

Ta ƙira sunansa ya amsa

"Na'am Hayaaty".

"Behave, coz I Know you, da fara'ar nan nake son ganin kun dawo min gida is that clear?".
Daga Rayhaan har Mahmoud suka haɗa baki wajen faɗin "Yes Ma!!".

     Motar Rayhaan na fita daga gida sukayi clear da motar su Mu'azzam, Mahmoud ya gansu amma sai ya girgiza kai da murmushin takaici ya dubi wayarsa sannan ya maida dubansa ga Rayhaan wanda shi yake driving yace  "Drive faster Rayhaan coz ina so mu dawo gida da wuri."

Inda suka tsaya farmhouse ne mai girman gaske ga ƙayatuwa, sassanyar iskar dake busawa yasa Rayhaan ya ƙanƙame jikinsa yana ƙarewa wajen kallo,  Duk ma'aikatan gidan gonan suka taho da sauri inda Rayhaan ya tsaya da motarsa, nan suka kwashi gaisuwa cike da girmamawa da kuma fara'a, wani dattijo daga cikinsu yace "Ranka shi daɗe halan wannan Rayhaan ne?"

Murmushi Mahmoud yayi sannan ya amsa da "Na'am, yau dai na kawo maka Rayhaan har inda kake".
"Allahu Akbar, dubi yanda ya zama saurayi, rabona da shi tun bai fi shekara biyu ba, sannu da zuwa ɗana".
Shidai Rayhaan bai ce qala ba sai murmushi tunda babu wanda ya sani daga cikinsu, "yawwa Baba". Ya amsa a takaice.

"Ranka shi daɗe barrister ya zo tuntuni yana chan palour yana jiran ka."
Kai Mahmoud ya jinjina yace "Nagode Baba Adamu, Allah ya sa dai yau ka dafa shayi?"
Baba Adamu ya washe baki yace "Ah... Shayi kam akwai yanzu kuwa zan kawo muku".
Mahmoud yayi murmushi ya ja hannun Rayhaan yace "mu shiga gida Barrister yana jiran mu.
Rayhaan yace

"Dad.... Haka kake da kusanci da wadancan bayin Allah n? You seem relaxed".
"Yes Son, these people are my second family, mutane ne masu riƙon amana and  Baba Adamu...... He's one of a kind."
Rayhaan ya jinjina kai yace "i see."

Bungalow ɗin dake gidan gonar suka nufa inda suka iske Barrister zaune yana ta dube duben takardu daga lokaci zuwa lokaci yakan kurɓa shayi.
Miƙe wa yayi ganin su Mahmoud sun shigo nan suka gaisa cike da fara'a

"So finally I've got to meet Mr Rayhaan Mahmoud Adams?".

Mahmoud ya yi dariya yace "yes finally! And sorry na san ka daɗe kana jiran mu, tafiyar ce da nisa."
"No, not at all nima ban daɗe da shigowa ba, kamar yanda ka bukata ga takardun na kawo sannan kuma ga yarona shine zai recording wannan moment ɗin yayinda Rayhaan zai sa hannu ga takardun saboda sha'anin rayuwa and also stand as witness." Kai Mahmoud ya jinjina in acceptance sannan ya juya ga Rayhaan wanda tuntuni ya kasa gane komai da suke yi, he's confused bai ma san ana miƙa masa takardun ba har saida Mahmoud ya dafa kafaɗar sa yace

"Sign these papers Rayhaan my son".

"Dad .... If i sign all these papers, what about my brother Mu'azzam? What about Ruqaiya? I'm not the only son you have".
Murmushi Mahmoud yayi yace
"Son you won't understand why I'm doing this now, but nan gaba kaɗan zaka fahimci dalilina na yin hakan. Wannan takardun da kake gani kuma tun da aka haifeka na sayesu da sunanka, ni kawai juya maka su nayi amma sunan ka ne a jiki, now that you are of age, i thought it's high time you take what belongs to you. Wannan kadarorin duk ba nawa bane naka ne, ina tsoron in faɗi in mutu ba tare da na damƙa maka kayan ka ba Rayhaan coz hakan zai iya jawo tashin hankali tsakanin ka da Su Mu'azzam bana fatan hakan, duk da haka ma ban yarda wannan maganar ta fita ba, bazaka fahimci abunda nake ƙoƙarin sanar da kai ba but with time you'll understand In sha Allah".

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now