Episode 4

182 24 0
                                    

    "Wai me kika ɗauki kan ki? Look at the condition of my car, duk saboda ke ne motana ta shiga wannan halin! Because of you! Haka ake a gidan ku baki san mutum ba kawai ki shiga motar sa, what if i sue you for trespassing?"
"Oohh please! Dakata Mr man, kada ka d'aga min Murya saboda wannan akwalar motar taka, in ba don ƙaddara ba wa ma zai shiga wannan motar? (Ta bugi motar da k'afar ta) consider yourself lucky that Benazir ta shiga motar ka. Tell me nawa ne motar naka? Ni Benazir Zayn zan biya ka for the damages, fad'i ina jin ka kafin na sauya ra'ayi".

Rayhan bai san lokacin da dariya ta kufce masa ba harda kama ciki yana nuna ta da yatsa.

"Ke d'in ne zaki biya ni kud'in  motar nan? Ta yaya? Ina nufin da kina da kuɗin biyana da baki shiga motar ba in the first place, da taki motar zaki tuk'a, besides this car is priceless."

Ya k'arasa daf da ita yace "by the way...... Me ma zai sa in damu tunda ga kinan? Dalilin ki ne muke nan wajen saboda haka kece zaki gyara min motar, you will fix my car this minute!"
Cike da fargaba ta jinjina kai tace
"Sorry...... I'm sorry, zan iya siya maka irinta sak amma ni ban iya gyaran mota ba gaskiya, ban san ta ina zan fara ba"
Chan k'asan  mak'oshin ta kuwa cewa tayi "sai kace wata mechanic wai in gyara mota."

"I heard that!".
Ya fad'a mata ba tare da kallon inda take ba hankalin shi na kan wayar shi, da sauri ta cije harshen ta tana mai rufe bakin da tafin hannun ta. Daga nan babu wanda ya sake wa ɗan uwansa magana. Rayhan yana ta yawo neman network amma sam babu, daga bisani ma emergency ya koma ita kuwa bata da aiki sai bin shi take da kallo tana dariya.

"Zai fi maka kyau ka hak'ura, daji fa muke; ko dai mu tsaida wata motar da zata k'arasa da mu ƙauye na gaba ko kuma mu kwana a nan coz babu wani network da zaka samu a nan".
Ko kallo bata ishe shi ba ya cigaba da harkokinsa yayinda itama ta mak'e kafad'a  ta nemi wani dutse ta zauna a kai ta cigaba da kallon sa, Rayhan yana haɗa ido da ita harara yake watsa mata ita kuwa sai ta maida martani ta hanyar yin murmushi, abunda yafi k'ular da Rayhan kenan.

     "I don't even know her but she has caused me enough trouble already, she's a witch." Ya fad'a a ranshi idanuwan shi a kanta. Sai lokacin ya  lura da kayan jikin ta  ga lalle ta sha ga makeup duk da ma dai tayi gumi hakan bai hana shi fahimtar lamarin ta ba.
"Amarya ce ke? Ya tambaya da gira ɗaya a d'age

"Wait a minute!...... Did you perhaps run away from your wedding venue?coz kin yi kama da amaryar da ta gudu ranar auren ta is that why you hide in my car?? I hope I'm not in trouble".

Tafa hannu tayi sannan ta nuna shi da  yatsa "Wow! You are a genius!! Ka chanka daidai kuwa, gaskiya kai na musamman ne alaji! Ƙwaƙwalwar ka tana ja."

"Me yasa kika Gudu? Girl you are crazy i swear!"
Mak'e kafad'a tayi kafin tace "it was an arranged marriage, saboda business na Dad, shine zai aurar ni ga tsohon bijimi ɗan shekaru hamsin da biyu can you imagine? I'm only 18yrs old that man is just like a grandpa to me, anyways why do you care?"
Ta kawar da kanta gefe tana wasa da yatsun ta cikin ƙasa, girgiza kai kawai yayi, ya cigaba da duba wayar shi ko zai samu signal .

    Bayan wasu mintina ya hak'ura ya mayar da wayan cikin aljihun shi ya nufi inda motar take ya shiga, abubuwan da yake buƙata kaf ya kwashe ya zuba su cikin jakar sa ya goya a baya, rufe motar yayi ya fara tafiya, ba shiri ta miƙe da gudu ta bi bayan shi  tana ƙoƙarin goya nata jakan.
"Hey! Mr Man!..... Ina kuma zaka? You can't leave me alone a wannan wajen."
Ko kulata bai yi ba ya cigaba da tafiya saida ya ɓullo titi sannan ya tsaya ya kama kunkumi yana dube dube. Ganin cewa bai ji motsin ta ba yasa shi juyawa. Hango ta yayi ta durk'ushe tana ta fama da k'arangiya duk ta kwaso su a jikin rigar sai yarfe hannu take kamar zata yi kuka.
Dariya ta bashi da bai san dalilin yi ba, a zuciya yace
"How cute!!"
K'arasowa yayi inda take ya durk'usa ya kama riga yana cire mata k'ayoyin ........

__________
Wannan wanne irin al'amari ne? Awa biyar kenan har yanzu babu wani labari. Are they trying to tell me yarinya k'arama kamar Benazir ta ɓace musu?
"Hello.... Wai ya naji shiru ne? It's been five hours babu labari, na tabbata tana nan cikin gari, ina take da wani wayon b'oye kanta na tsawon lokaci haka? Look...... Duk wani check point na saka an yi enquiring bata wuce ba, basu ma ga mai kamar ta ba! Wannan yana nufin tana nan cikin garin, you have to find her or else I will loose a lot of money! Millions!!"

  Yana cikin wayan ta fito, hannun ta cikin na Ayeesha, tana murmushi yayinda Ayeesha ke mata hira.  Kallo ya bita da shi cike da mamaki har suka fice daga ganinsa sannan ya dawo hayyacin sa

   "Oh yes! Ta yaya akai sai yanzu na fahimci hakan? Me yasa ban lura da hakan ba? Aminatou looks relaxed even after her darling daughter left home, while ina nan ina ta d'aga jijiyoyin wuya, ita kuwa she looks as if ba abunda ya faru, this must only mean one thing! Ta san inda Benazir take, she knows everything, ko kuma ince they planned to disgrace me!. Jefar da wayar sa yayi bisa kujera ya fice zuwa hanyar da Aminatou suka bi nan ya iske su suna hira.

     "So duk abunda ya faru was your doing right?, Kece kika taimaki Benazir ta gudu!". Cikin tsawa yayi maganar hakan yasa Ayeesha ta manne mata a jiki tana rawar jiki
"Ayeesha my dear, tashi ki tafi wurin y'an uwan ki zan yi magana da Dad naki"
Kai ta jinjina ta bar wajen da gudu kafin nan Aminatou ta miƙe tsaye

"Eh.... Ni na sa ta gudu, me zaka iya yi a kai? Ko kana tsammanin yanda aka lalata min rayuwa ni zan bari na y'ata ya salwanta? Irin rad'ad'in da naji dalilin Auren ka bazan bari Benazir ta ɗanɗana shi ba, ina laifin ɗan Alhaji ilyas? Amma fa shi da kanshi ilyas ɗin kake shirin haɗa auren shi da y'ata, yanzu kai baka ji kunya ba? You choose money over your very own family and you are here to brag. Kar ma ka fara sannan kada kayi amfani da wannan incident d'in kayi ƙoƙarin shiga rayuwa ta because abunda ya faru 8yrs da suka wuce har yanzu ban manta da shi ba don haka ina maka gargadi kar na ƙara ganin fuskar ka a gabana , ko kuma a sashe na, yau na kyale ka domin na san zafin asarar kuɗaɗen ka da zaka yi kake ji, but this should be the last time da zaka shigo kana d'aga min Murya". Tana kai nan ta d'auki wayarta  ta barshi a wajen yana bin ta da kallo cike da mamakin ƙarfin halin ta. Kai ya jinjina kafin ya fice daga wajen rai a dugunzume...

*****.        ******    *******

   Duk motocin Rayhan akwai tracking devices a jiki, wannan batu ne da shi kanshi Rayhan bai sani ba cewa duk tafiye tafiyen shi ana tracking, saboda yanayin rayuwar yanzu duniya babu tsaro, kuma Mahmoud na samun report akai akai na whereabouts d'in ɗan sa, kasancewar ko ina akwai business rivals wanda babu abunda baza su iya yi ba domin kuɗi daga ciki kuwa harda cutar da ahalin su.

   " ina so kuyi tracking down motar shi, his mom  is worried sick, wayar shi ma bata shiga. Idan wani abu ya samu Rayhan i will hold you responsible!".
Yana kai nan ya katse wayar yana kallon Haleemah da ta kasa zaune ta kasa tsaye
"Look! Babu abunda ya faru, maybe inda yake babu network coverage ne don't be hard on yourself".

"Kasan dole ne in damu, Rayhan is my only child. I can't bear to loose him, Allah kad'ai ya san Halin da yake ciki"

Murmushi Mahmoud yayi sannan yace "dubeta, lokacin da na hana shi fita kece ta farko to break the rules and you helped him escape, yanzu duk kin shiga damuwa, kar ki damu... Duk inda yake i'm sure he's safe and sound In Shaa Allah"

"I hope so" ta faɗa murya a sanyaye....

#####

thanks for your patience ❤️❤️

NUR_AL_HAYATWhere stories live. Discover now