Episode 10

195 18 3
                                    

Da sauri suka nufi reception inda sukayi tambayan patient mai suna Rayhan tuni aka musu kwatancen ɗakin da yake Haleemah ko ta kan su bata bi ba ta fara nufar inda aka yi musu kwatancen Mahmoud na biye da ita.

   "Rayhan!!"
Cike da damuwa ta ƙira sunansa yayinda take ƙaraso wa cikin ɗakin, idanuwan ta cikin nashi tana sauƙe sigh of relief ganin cewa ba ɗan ta ne kwance bisa gadon ba, fuskar shi ta riƙe cikin tafukan hannayen ta tana ƙoƙarin magana.

"Did you know how scared i was? I taught wani abu ne ya faru da kai, Rayhan i taught I've lost you."

"Mom......Mom....Moooom..... Please calm down, ga waje ki zauna I'll tell you everything. First of all relax."
Hannun ta ya kama ya zaunar bisa kujerar dake gefen sa, ba tare da sakar hannun ba ya ɗago yana kallon ta
"I'm sorry Oummi.... I didn't mean to trouble you like this, But why are you here?".

Juyawa tayi ta dubi Mahmoud da tun shigowar sa ya ƙura musu ido yana jira Rayhan yayi noticing ɗin shi, tace
"Kaji abunda yake cewa..... He's asking why we are here!" Ta maida dubanta ga Rayhan kafin ta ce
"Ka kuwa san irin halin da na shiga? Wayar ka bata shiga bayan haka kuma motar ka an sameta tayi crashing into a tree, i was tensed and worried saboda ban san halin da kake ciki ba kai kuma kana nan ko a jikin ka. Thank goodness mun samu labarin kana asibitin nan if not i might even die of ........".

Kunnuwan sa ya toshe da yatsun sa yace "Mom! Why bring about death? Please I'm here now so please..."
Bai gama magana ba ta sa hannuwan ta cike da kula ta janye yatsun da ya toshe kunnen da su sannan tace "mutuwa ai ta zama dole, duk mai rai se ya ɗanɗana ta there's no escape".

Kawar da kai yayi gefe yana kallon Benazir dake kwance kafin yace

"Dad..... We can't let them know about her whereabouts, idan suka gano inda take ban san irin matakin da Dad nata zai ɗauka a kanta ba please she needs help".
Sai lokacin duk suka maida duban su ga Benazir dake kwance bisa gadon.
"Who is this girl and why are you here with her? Me yasa kace Dad ɗin ta zai ɗauki mataki a kanta? Rayhan are we safe? Are you in any kind of trouble?"

Kai ya girgiza alamar 'A'a' yana kallon Dad nashi da ya watso masa tambayoyi kai tsaye haɗiye miyau yayi da ƙyar sannan ya ce

"Dad...... Can we talk about it outside? Tunda nan akwai patient who needs a lot of rest".
Kai Dad ya jinjina sannan ya fice daga ɗakin Oummi na biye da shi jiki a sanyaye ya fita inda ya iske su tsaye suna jiran fitowar sa.
Nan ya kwashe labarin dauka abunda ya faru ya faɗa musu har yanda akayi ya sake haɗuwa da Benazir bayan rabuwar su.
"Dad she has nobody here, bata san kowa ba and she has nowhere to go idan na barta ita kaɗai......"
Bai ƙarashe maganar ba Dad ya dafa kafaɗar shi yace

"And who said you are going to leave her all alone? She's also like a daughter to me! I will not let anything bad happen to her son! Amma sai kayi min alƙawarin abu guda, kamin alƙawarin nan gaba zaka yi abunda na saka, you will take your place as the new Chairman of the company...."

Shiru Rayhan yayi na ɗan wani lokaci kafin ya jinjina kai yace "Dad..... You know that I have no experience with business world, how can i handle such a big  responsibility?".

Murmushi Dad yayi yace "Don nace ka karɓa ragamar shugabancin Company ba wai ina nufin zan barka da iyawar ka bane Rayhan, idan akwai wani al'amari da ya shige maka duhu you can ask me, KABEER yana nan ya kasance tare da ni tun lokacin da na buɗe Company ɗin, ya san almost everything he's my P.A and the only person i can trust after your mom, zai kula da kai sosai bani da tantama, Rayhan i just....."

"Fine Dad..... I'll do it, I'll become the chairman of the company i promise, i won't let you down again, I'm sorry".

Wani murmushi Dad ya sakar kafin ya yi hugging Rayhan yace "that's my Son! Yanzu zan yi magana da hospital management zamu  tafi tare da Benazir in dai maganar da ka faɗa gaskiya ne, zaman ta a Bauchi ba zai yiwu ba I'll arrange for an emergency flight". Kai Rayhan ya jinjina in agreement with maganar Dad kafin ya  koma cikin ɗakin da Benazir take.

Zama yayi gefen gadon yana kallonta kafin yace "don't worry Drama Queen.... You are safe, i won't let anyone hurt you again".

*******

  "Mahmoud na san yarinyar nan tana buƙatar taimako but i hope in the process of helping her we are not getting ourselves into trouble, ka fa ji abunda Rayhan yace "yaran mahaifin ta ke neman ta" idan kuma suka gano Rayhan is involved with the girl suka nemi su cutar min da ɗa na fa?".
Haleemah ta ƙarashe maganar idanuwan ta cikin nashi fuskar ta ɗauke da damuwa.
Murmushi Dad yayi sannan yace " I know it's not easy but we have to help her as a daughter, we might not know her but she's here because of Rayhan, iya sani na da Rayhan I've never seen him soooo concerned about someone he met for just a day, in such a way that he instantly agreed to become the chairman for her sake, Allah kaɗai yasan dalilin haɗuwar su so let it be, whether or not our decision is right time will prove it, but for now let's do this for Rayhan."

Murmushi Haleemah tayi sannan tace "in that case let's talk to the hospital management about her transfer". Jinjina kai Dad yayi suka bar wajen cikin sauri.

   Bayan mintina ashirin suka dawo tare da doctor, saida ya sake examining Benazir sannan ya dube su yace "nan da half an hour za'a yi arranging for ambulance one of our Nurses will go with you"

"Thank you doctor, this really means a lot". Dad ya faɗa da murmushi a fuskar sa yayinda suka koma ɗakin da Benazir take.
Miƙewa yayi ganin sun shigo yace "Dad...... Did you talked to the management?  Sun amince mu tafi da ita gida? Coz na tabbata waɗanchan thugs ɗin bazasu huta ba har sai sun maida Benazir wajen mahaifin ta, they might find her here".
Oummi tayi dariya tace "kwantar da hankalin ka Rayhaan......we are taking Benazir home so relaax".
Wani sanyi yaji a zuciyar sa nan take yaji hankalin shi ya kwanta ya furta "Alhamdulillah" cikin ransa sannan ya zauna yayinda Dad da doctorn suke tattaunawa.....

#vote!!🙏🙏

NUR_AL_HAYATحيث تعيش القصص. اكتشف الآن