WANI GARIN YAFI GABAN KUNU....

284 19 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*🍚



HUMAIRAH B. MELODY





            17

Hmmm kanajin zanso ambil abokina? Abba ya juya ido yace ryt of course Mezai hana.
******
*bayan shekara uku*
Neehlah tayi candy tabar ambil a aji uku zata ss one ambil akwai kwazo da haxaka Don har wani abu aka kafa a makaranta wato kotu Don hukunta masu laifi ambil itace lawyer, ambil Tana ss one akayi mata double promotion zuwa ss 3 tuni aka biya mata komai NILE UNIVERSITY Tasa dake Abuja dayake neehlah Tana MAITAMA SULE UNIVERSITY,
Ambil tana gabda gama makaranta Kewan babarta da baffa malam ya tasata gaba taji duniya Tana bukatar ganinsu nan tasa tsama kullun kuka, haka aka dinga bata hkr.
Duk Wanda yaga ambil saiya kara kallonta saboda tsabar kyau wata rana ciwon ciki ya kamata a school kamar zata mutu tuni aka dubo file dinta king aka kira yana shika amma cikin miti goma sai gashi daukan ambil yayi cik sai mota kawai duba Jikinsa yayi yaga jini cikin tashin hankali ya juya yaga ambil bata motsi ga jini facha facha yace wat asibiti yakaita mafi kusa wato pal aka basu gado sannan yaje ya samo mata kaya shiyasan meke damunta hakan ya nuna cewa ambil taxama Mace mai lafya hajiya yakira ya sanar da ita abunda ke faruwa Amman yace anjima zasu dawo.

saida ambil tayi bacci sosai sannan ta farfado taji jikinta tsami koh ina ciwo yake mata king yace "maza ki tashi muje toilet in nuna miki wani abu tace toh ba musu riketa yayi maikaratu da king da ambil su ake cewa perfect match, suna shiga ya rabata da kayan jikinta yasa ruwan dumi yayi mata wanka ya goge mata jiki kannan tasa kayan daya siwo mata da panties harda always ya nuna mata yadda zatayi ta fito tsaf sannan aka basu nagani aka sallamesu sai gida hajiya ta zaunar da ita tace *ki kula ambil yanzu bada bane yanzu Kinkai munzilin da duk namijin daya kusanceki toh tabbas zaki dauki ciki kuma a wannan lokacin zakiga samari iri daban daban saiki kula sannan wajibci yahau kanki sallah akan Kari Duk lokacin da haila yazo miki zaki ajiye sallah har sai ranan da yadauke sai kiyi niyya kiyi wankan tsarki yadda xan sanar dake Kisamu ruwa mai tsafta bamai najasa ba sannan karki sake kifara wanka na sabulu sannan kiyi amfani dan wankan tsarki maka ruhi ne shi ana bukatan ruwa Mai tsafta saiki daura Niyya kiyi bisimillah ki wanke hannuwa tsaf sau uku,  saiki debo ruwa ki wanke daga cibiyanki zuwa kasa, saiki wanke barin dama sau uku hagu sau uku kina gama wannan saikiyi alwala shikenan kin tsaftace kanki kuma duk wanka iri dayane saidai niyya ta banbanta* Ambil tayi shuru tace chan kasan ranta "wato girma yaxo lokaci yayi dazan fara nunawa king cewa yanzu bada bane level Don change".
Hajiyace ta katseta tace kinjini koh tace eh naji, tashi tayi tashiga daki ta taradda neehlah tana karatu saboda an dawo daga yajin aiki zata koma  kano makaranta suna komawa sai exams nan suka kafa hiran duniya har ambil take sanar da ita cewa uncle dinsu yace yana sonta takuma aminche tanaso saboda gayene Iya gaye Don ya hadu bautar kasa yaxoyi Zaria Amman asalinsa dan kaduna ne Sunansa Muneer Washe gari ambil ta shirya cikin school uniform kirjinta yacika yayi fam saitaci karo da king yace ke sakko ina zuwa a haka yau ina hijab din? Ambil tayi Far da ido tace "King I just feel like going to school just as you see me so plz I'm late saina dawo," baki Isaba ambil kin mance matsayinki ne a wajena dole inkare martabarki a matsayinki na matar..........saiyayi shuru ambil tace "baka Burgeniba dabaka karasa ba kamar yadda ka gargadeni hk nake gargadinki nacewa ka kyaleni jiya ba yauba so mind your tonque idan kaki zan tona kowa yaji, magana ambil ta keyi kasa kasa ana bude gate taga muneer cikin motarsa tacema Direba ya sauketa ya koma motar muneer tashiga peogueot 307 sai school suna y
tafe suna zuba love zan iya cewa muneer shiya koyawa ambil so hartafara gane meye So.
direba yakoma fitowan king keda wuya yace uba harkayi meh? Yace ai wani ya rage mata hanya koma da alama sunsan juna kwarai.
ai tuni king ya figi mota sai  School dinsu ambil daidai tana sauka ai saida ta firgita muneer ya chakume yace "idan kana cin kasa kasan irin wacce zakaci saboda kar tayi maka illah kuma dole a tsaida ruwan miyan haka Don baxan jure ba" muneer ya fizge yace nikuma baxan lamunta ba ai tuni ambil tayi cikin school don tasaba dason muneer dukda tasan cewa da mijinta wato King, kuma da biyu takeyi don yagane banbanci aya da tsakuwa.

WANI GARIN.....yafi gaban kunuWhere stories live. Discover now