WANI GARIN YAFI GABAN..... 18

281 18 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*🍚



HUMAIRAH B. MELODY





            18

Ka kyaleta Don akan ambil zan iya shatawa kowa layi wallahi koda abba jumare ne babban abokina inko kaki saina rabaka da rabin duniya.
Muneer yayi banza dashi ya wuce dukda mutane basu ankare dameke faruwa ba, King ya juya baije office ba yakoma tun daga bakin gate yake kwadawa hajiya kira itada neehlah suka fito Sukace lafya kuwa king cewar hajiya, "hajiya dole ambil ta daina fita saboda har yakaiga a dauketa a mota wannan ai iskancine yau danida ambil ne a gidannan"
Hajiya tace kaga saikace wata matarka koh neehlah baka samata ido yadda kasawa ambil ba kasakar mata Mara tayi fitsari pls taya wani zai aureta idan babu so? Koh ka Mance naka zamanin,?  Ai fuuuuuu..... Ya fice sai office saboda haushi yakasa attending dubban matan dasukazo dominsa.
*********
Ambil wai waye wannan mutumin koh kinsanshi ne?  Ambil tace my love you don't have to worry about mugune haka yake koh a gida mance dashi so yake ya gutsure halakata dakai kuma bazaiyuwu ba, nan ambil ta shigarda muneer abun tausayi muneer ya mutu akan ambil koya zata kasance Allah kadai yasan daidai.
Komawar ambil gida Don bata samu hajiya ba neehlah tagayawa ambil maima Kwan ta tsorata ai sai cire kaya takeyi tana wake wake kamar taxare bugun kofa sukaji neehlah ta tsorata tace kinjishi koh ambil tace ke Dadina dake zabuwa ce king din kikewa hk eh fah, falo tafito zata kitchen ya tashi ya sheketa kamar zata mutu yace zanyi ajalinki ambil zanyi sanadin barinki duniya matukar kika cigaba da batamun rai bari kiji ambil  I LOVE YOU SO MUCH you are a woman nyc with ol quality kisani ni mijinki ne kinsan cewa zunubi kike kwasa ambil help me please karki kula kowa, duk zancen dasuke neehlah naji ai bakaramin firgita tayi ba tace daman ambil matar yaya Amir ce?  Dole ambil ta fedemun biri har wutsiya don ingano bakin zaren.
Ambil tayi shewa tace "ahayyeeeeh nanaye daman wannan lokacin nake jira taxo bari kaji yaya Amir  I HATE YOU SO MUCH HATE SEEING YOU ada baka soni ba sai yanzu dana gama hada komai na cikata Mace? Koh Ka mance kazama ambil kohka mance yadda kake guduna ina wari koh Ka mance cewa baxaka taba Kirana matarka ba?  Allah shi kyauta kazama mijina muneer nakeso He and he alone kayi tafka babban kuskure Ashe Inada rana kasani kaine sila nima a yanzu naxama Raina kyakkyawar sarauniya baka isa ka sani cikin damuwa ba har yakaiga anyimun dashen zuciya kasani cewa wanda Allah yaso shiyake maidawa sarki, kasani duk zaman tsanani yanada iyaka, kuma cikinda baaso yana iya haifar da da mara ido, wannan haukar naka baya rasa nasaba da Jarab El ghira, ka sauwakemun aurenka pls.

ai tun king yana tsaye y akoma ya zauna saboda ambil na neman tarwatsa mishi sauran rayuwanshi daki ta ruga tashige ta rufe kofa tana kuka bakomai take tunawa ba sai iyayenta na ainihi wayanda aka kashe,
Kuka takeyi neehlah tafito daga toilet ta dafa ambil tace
"Kiyi hkr komai yayi farko zaiyi karshe kiyi hkr da yaya amir baya bukatan komai sai kulawanki yanzu nasan yayi ladama na hakika kiyima yaya Amir biyayya Don samun aljannarki ki rabu da muneer.
Dakata neehlah dakata bakisan mafarin abuba karki yanke hukunci ban taba baku labarina ba da saikun tausayamun Amman yau zan fede muku biri har wutsiya amma sai a gaban hajiya inaji a jikina ku jininane saboda kidubi kamanninmu neehlah gaban mudubi suka nufa said neehlah taji tsaro ambil tace labarina yanada matukar tsawo ne neehlah tace bari hajiya tadawo.
Karar mota sukaji neehlah taleka taga ba motar King saina hajiya da motar ambil dake rufe da tampol, da gudu neehlah ta sauka wayar king tagani tayi saurin dagawa tace hello yaya kaiwa ambil waya, cikin sauri takoma yace
"kibarma zuciyanki ambil zan jurewa rashinki Amman karki tona sirrin dake a boye karaf yana gama magana ya kashe.
falo neehlah takoma tasanarda hajiya komau

WANI GARIN.....yafi gaban kunuМесто, где живут истории. Откройте их для себя