WANI GARIN YAFI GABAN KUNU

225 24 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*.........🍚






*HUMAIRAH B MELODY*


    

             25

HUMAIRAH na kwashe da dariya nida sauran friends Dina.
******
Arfat ce kwance shememe batada lafya cikin ikon Allah babu tantama ciki gareta tayi fari ta dashe Koh ina a jikinta yayi bulbul taciko Kuna babu Alu babu labarinsa Tunda yagama Da ita Daman mayawaci ne shi daga Nigeria har nijar zuwa yakeyi, hankalin arfat ya tashi sosai bata nemi kowa ba sai babanta murna kamar Ya kasheshi saboda sunkusa cinma burinsu, yace "Kinga ai sai a sanarda Mairo tasan halinda kike ciki waya Ya dauka bugu daya hajiya Mairo ta daga sallama tayi babu yabo babu fallasa.

Yakara dacewa yajikin ameer dafatan yanajin sauki? "eh" kawai tace a takaice Daman Inaso insanar dake koh kinsan cewa arfat tana dauke da ciki koh?  Hajiya taji abun banbarakwai namiji da suna hajara chan kasan ranta tace Amman sunusi bashida kunya koh na miskala.

Mairo Kinyi shuru tace Inaji "yana gadon asibitin ne ya iyayi mata ciki koh yaya wannan maganar yakamata a tauna kafin a fadeta saboda baiyi kama dana masu baseerah ba, watan king daya a asibiti sau daya taje gaidashi koh sau biyu Amman tace ciki Toh babu tantama karya takeyi wannan zancen naku bai karbu ba saidai ta nemamai uba saboda shegene Amman ba jinina ba" tafadi tareda kashe waya tace ai idan Maye yaci Ya mance Toh uwar da bazata manta ba kuma cin tuwon kishiya ramako ne.

baba sunusi Ya Saki baki yace lallai Mairo Dani take xance harni zata dasawa magana lallai idan tasan wata Toh batasan wata ba, asibitin zani Yanzu.


*****
Alu ne zaune yaje gaida king sannan ya bashi hkr sannan Ya saita zancenshi nacewa matarsa bin Maxa takeyi Yanzu hk tana dauke da ciki karya sake ya aminche dashi a matsayin da koda ya hkr yaci gaba da zama Da ita sannan yasanar masa Da shirin arfat akansa sannan yasanar masa yabar aiki kudi king yaba Alu na mota yayi masa godiya Amman king yashiga rudani.

Alu nafita ta kofar baya saiga baba sunusi bai nuna mishi komai ba iyakaci murmushin daya saki Wanda Nikaina dake rikeda alkalamina nakasa baiyanawa Mai karatu nameye,
guri yanema ya zauna suka gaisa yace jiki yayi kyau ambil ce ta Mike Don maganar Alu baa gabanta akayiba Amman akunnenta suke baba sunusi yabi ambil da kallo har saida king ya gane Ya katseshi dacewa baba ya harkoki yace "Lafya lau wai ameer har Yanzu bazaka maida yarinyar nan wajen yan uWanta ba?  King yayi murmushi yace "ai ambil yarinyar Alhaji Ibrahim LAWAL yabo ne wane Ga hajiya tawa daga baya mukaji labarin komai kaga baba yarda arfat Take gareni haka take a wajena.

Jikinsa yayi Sanyi yace "kanwarka batada lafya Kuma dagani ciki gareta" king yace baba Ya akayi Kasani kaida ba likita ba?
"Eh  ai jiya bayau ba nasan Duk wasu alamomi" king yace Allah ya raba lafya.
Daga wannan king baice komai ba iyakaci wani Kuna dayakeji.

baba sunusi Yasha jinin jikinsa Ya tashi king yabashi kudin mota sukayi sallama yana fita king yafara hauka sai warwatsar da abubuwa yakeyi ambil ta firgita nurses takira Amman sun kasa komai saida likitoci suka taimakeshi da alluran bacci juyowa sukayi suna kallon ambil sukace "meye abunda kikasan yaji na karshe?
ambil tace kanin mahaifinsa ne yaxo kuma daga fitansa naji kara daban daban.



*DEDICATED TO MY FANS*❤🤝

WANI GARIN.....yafi gaban kunuWhere stories live. Discover now