WANI GARIN YAFI GABAN KUNU.... 21

247 21 1
                                    

🍚 *WANI GARIN*.........🍚






*HUMAIRAH B MELODY*





             21

Da wannan tunanin Aka kira king yayi godiya sai a lokacin ya fahimci idon ambil akwai Marsala angama komai an watse ta amshi gift dinta tasa a bayan mota Kannsn suka wuce.

King bai damu daya shiga ba yana xuwa kofar gate yace "alhamdllh mun kawo zan wuce" ambil ta fara fita kannan suka mara mata baya tafe take tanaji aranta zata iya kashe king saboda illar dayayi mata amman akace Dan hakkin daka raina shizai tsole maka Ido.

Gida king ya nufa yana shiga yaci karo da arfat yace "Pls dakata karki batamun rai nasan magana kikeso kiyi I'm not interested please let's take the bull by the corner".
Arfat tayi tsaye tace ikon Allah wannan shine mulkin mallaka gani da baki magana ya gagareni hmm wannan shi ake kira watsa da dama opportunity comes but onces.

*Tabbas duk matar datayi da wasa da damanta lokacin da ake damawa da ita tabbas idan ta kubuce mata zata Zama abun tausayi kamar yadda arfat tasamu kulawa amma tasama ranta fitina kisani abunda hakuri bai bakiba toh rashinshi bazai taba bakiba muje zuwa mahaukaci yahau kura.*

Yana Shiga ya Kwanta a kan gado ya Saki AC dayake da ranane, a takaice duk wanda yaga king yasan yana cikin tashin hankali gashi yasanar da Abba jumare amma baya wani Abu akai.

Saida yamma yafito yayi wanka arfat tayi mishi sannu yajuyo a fusace yace,, "banda bukatar sannunki donba ciwo nakeyiba mtwww"
Arfat tayi sauri ta rikeshi tace "Yaya amir idan baka sona pls ka sauwakewa rayuwana pls idan kuma bazaka sauwakemun ba kasamamun aiki saboda inje in gwada baseerata pls".

King yace Arfat nidake mutu karaba takalmin kaxa amman inaso kisani ruwa cikin chokali ya ishi Mai hankali wanka,  kuma aiki bayanzu ba cikin gidannan anan nake bukata ki zauna koh nanda gate ban aminche kijeba".

inaso kuma kishirya nabiya mana aikin hajji danida kowa da kowa kuma nasiya miki wata mota wannan nakin kiyi kyauta dashi...........

Fit yafice bai wuce wani guriba sai filin polo inda ake wasan dawakai game din dake burge king Don ada yanayin wasan.

wayarsa yaciro Don daukan video kawai juyawan dazaiyi ya hangi ambil zaune ta harde Tana kallo cikin sauri yacire no respect din dake fisland yace Wat!!!!!   Me ambil taxoyi ni humairah na kwashe da dariya nace king kai mekazoyi?  Tashi yayi yaje inda ambil take ya zare madubin idonta yace meyasa baxaki taba hankaliba kinsan yanzu bada bane you are a lady know you are matured cos you have someone like me.

Ambil ta tashi cikin mutane yace
"this is strange episode I have ever encountered in my life for God sake whr do I know you some guys are stupid fah daganin Mace saikazo kayi Mata magana dubeka kazami Kawai kana ganin ka hadune mtww toh kayi kuskure pls matsamun hannu tasa ta fizge mudubin ta daya zame mata jiki saboda illah da king yayi mata saboda Marin daya taba yimata, kaxami kaje ka nemi irinka kuchakai marasa kamun kai ambil takama hanya tafita harabar wajen mata sai dariya suke mai wani haushi yasashi bin ambil amma tuni tashige motarta da aka dade ana koyamata motar Data ciwo saboda kwazonta a makaranta.

Shima motarsa yashiga yabita itakoh gudu take ferawa basu Tsaya koh inaba sai a round about dake PZ ya tareta kannan yafito itakoh dayake tinted glasses ne anrasa wake cikin motar gashi taki fitowa shikuma ya haye saman mota gashi sun tare hanya sai an kutsa ake iya wucewa saida ambil tayi mintuna goma kannan tafito..

saida ta burge kowa mutane sai cewa suke Ashe macece, tsaye tayi tana kada mukulli tace "Ka kyauta kayi abunda ya dace kasani ni ba kanwar lasa bace amma nabaka minti goma ka dauke motarka inba hk ba yanzu ba sai anjima ba zansa a daukemun ita. Cikin motarta ta koma ta zauna sai horn takeyi motarta kirar Lexus SUV tanayi tana kallon time minti goma daidai tafito takarasa gabansa tace "kabar ganin allura karama toh kasani karfe ce kayi dakai kamar uwar turwa me ake da mutum irinka ka aje gashin baki kamar kakan bunsuru banyi dakai saboda bana abota da zabbi masu dogon Doro, Ambil kina iya komai wallahi Nasan cewa na chanchanta amma kisani ana barin halak Don kunya kuma ninayi miki komai".

dakata pls kawai malam kace inbiyaka kudin hidiman dakamun kayi mini illah kuma kasani sainayi maka illah waya tadauko takira masu kauda mota cikin minti kalilan sukazo tamika musu kudi suka kauda motar din ta shige tabar king tsaye cizon yatsa yayi yabi motarsa abun haushi cincirindon mutane daya gani Shiya kunyatashi a lokacin farko.


DEDICATED TO AUNTY MAI JIDDAH MUCH LOVE ANA TARE KAWAI KIHUTA ALLAH YA TAIMAKA KIN NUNAMIN SO TA DALILIN LITTAFINA ALLAH YAKARA DAUKAKA GIRMA DA TSARON ALLAH.

WANI GARIN.....yafi gaban kunuWhere stories live. Discover now