WANI GARIN YAFI GABAN KUNU..... 23

240 19 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*.........🍚






*HUMAIRAH B MELODY*

   



            23

Doctor imran ne yashigo yace kowa yafita akanme Mutum baida lafya acikashi Da surutu ambil dake waje itada neehlah tace "AI shine mata kamar karya batada aiki sai haushi Mutum ma baida lafya Amma baa kyaleshi ba mtww"
Haka kowa ya fice daga likita sai abba jumare suka zauna don tattauna matsalar king.

Abokina Amir bai rasa komai ba gameda kudi dukiya Amman ina gaya maka imran king yarasa farinciki acikin gidansa yarasa kwanciyan hankali acikin gidansa yarasa kula so kauna acikin gidansa Toh ka gayamun taya Abokina bazai shiga tunani ba? Gashi yakamu dason yarinyar da dawuya ta aminche dashi saboda rashin Kyautawan dayayi mata a baya just tell me Taya king zai samu farinciki?.

Imran yayi ajiyan zuciya yace Abba dole ne Asama mishi abunda yakeso Kuma dolene yakamu kulawar daya rasa inkoh ba hk ba zan iya cewa zamu rasashi lokacin Da ake matukar bukatansa.

Abba yace Bari muga meye results din suka kumsa saboda gaskiya Abokina yana cikin damuwa kwarai basu rufe bakiba king ya farka yanata kakari yana kokawa da numfashinsa Nurse!!!!!!  Imran ya kwala musu kira suka shigo a gigice hajiya taji wani radadi a ranta batasan lokacin datace ya Allah kaba dana lafya Dan tsarkin mulkinka shine farincikina tun bayan mahaifinsa hawaye masu zafi Suka kwaranyomata tuni ambil taji jikinta Ya mutu ta matsa kusada hajiya tace "hajiya Duk wata damuwa da yaya king yake ciki waccan Matar itace sila tun zuwana cikinku nasan cewa king yana cikeda damuwar arfat ba ita kadai ba harda iyayenta musamman mahaifinta.

Kici gaba dayi masa adua don yana tareda musiba hajiya Kiyi hkr king dan'uwanane kuma nasan ni wata bangarece ta rayuwarsa Amma Ya tsaneni hajiya taya kike gani zan taka muhimmiyar rawa a birnin zuciyarsa hawaye ke zuba a gurbin idanun ambil neehlah ma lokaci guda itama tafara zubda kwalla.

Hajiya sanadin king idan baki taba luraba kalli idanuna glass din dake makale a idonta ta yakice tace hajiya kalli kalli idona, ganin idanun ambil hajiya ta gigita tace "ambil kina tareda wannan problem din Amma kika zauna ya janyo ambil tace kiyafema king dafatan basuyi miki ciwo ambil tace "ba kasafai nake ganiba kuma dalilin dayasa kikaga nake yawan sa glass shine idanuna sun juye yazuwa harara garke.

basu Ida magana ba sukaga an wuce da oxygen na ceto numfashi arfat tasaka kuka Mai karfi "king karka mutu pls inasonka wallahi I need you as life need air idan ka tafi ka barni babu da yazanyi da rayuwana" koh kallo bata ishi su hjy ba adua kawai suke yimai nasamun sauki.

saida aka shafi kimanin awa Daya kannan suka fito abba yace waxai kwana dashi hajiya tace itace zata Kwana arfat zatayi magana hajiya tace  "Maxa ki wucegida ayita sallah ana mishi adua Ambil tace Bari tasiyo musu abinchi cikin daren tanemo musu abinchi harda kayan shayi dayake akwai Flask a dakin dayake haka suka wuce tareda arfat Tana gaba su ambil suna biye Da ita da ambil taga tukin gadara takeyi tuni ta yimata over taking.

Daren da arfat ta isa gida ta rude takira baba sunusi tana kuka tace "baba nashiga uku baba wai menayine daban haihu ba? Baba king yana asibiti zai mutu wazai gaji dukiyarsa banida da banida kowa baba burinmu baxai taba cikaba Kenan? 
Baba sunusi yace tun tuni nace kinemi koda mai gadin gidanki ne kibashi WANI Abu ku kebe daganan saimu kasheshi Kinga koda duniya da abunda ke cikinta ne babu Wanda yasan abunda ke faruwa.

dif arfat ta dauke wuta tace baba kisa fah kace yace mata mukayi alwashin kashe Amir bare maigadi karamin alhaki arfat kinsan yadda muke da dabi tsakaninmu da Mairo kinsan cewa hameedu yabar dukiya taje Tasamo shege tace dansa ne Haka muma zamu kwashi ganimar, a hands-free tasa wayar mai gadi yaji komai a kokon kunnensa arfat tayi ihu tace ina cewa uwa maganin kukan danta yau baba kaine maganin kukana.


mai gadi yarude yace tabbas alhaji baiyi dacen Mataba Ashe hk wasu iyaye suke tabbas arfat bakiyi dacen uba ba inkowa na takama da uba kebakyasa bakiba zaa kasheni tabbas sunyi shuka a idon makwarwa.

sando yayi yafice saida dare yayi arfat ta mance da king yana ciwo ta fita xuwa dakin maigadi Alu dayake Sun sake sabo Alu kwankwararren Dan duniya ne Kuma Kar yake kallon kowa bugun kofa Yaji Ya leko yaga arfat Daman shima a rike yake saboda tuzuru ne Kuma baida mata a birni tana kauye.

"Alu kabude mana" karaf ya bude tace ya biyota har dakin king tadinga mishi hira Daman shima kiris yake jira tuni sukayi abunda dace har saida gari ya waye kannan ya kakkabe bujensa yakoma bakin aiki arfat ta zauna shuru dasafe tana nazari sai a lokacin ta tunada tanada mara lafya shiri Takamayi tayi yan kwabe2 ta tashirya a basket wajen karfe shadaya zuwa asibiti Taje ta taradda su neehlah Da ambil suna kwashe kayan break zasuje shirya na rana Sakato tayi a cikin ranta tace danasani banzo ba muncigaba da more rayuwa nida Alu Amma danba Kara ambil zata wuce Tace "kinemi guri kizauna Tunda baki iya gaisuwaba kin tsaya kerere".

WANI GARIN.....yafi gaban kunuحيث تعيش القصص. اكتشف الآن