WANI GARIN YAFI GABAN KUNU.......

270 23 0
                                    

🍚 *WANI GARIN*.........🍚






*HUMAIRAH B MELODY*



            27
Sai dariya Sukeyi farinciki fal wata yarinya ce tafito tace Jabbama waigowa ambil tayi taga yarinya Wacce zatakai kimanin shekara hudu zuwa biyar, Ambil tace Baffa malam Wacece wannan?
Cikin murmushi baffa malam yace Kanwa kika samu bayan tafiyanki.
Ambil ta  Sunkuceta tayi wajen hajiya tace hajiya Allah yayi halitta a anan kaman ba yar kauyen runhu ba Inna kibani ita intafi da ita innuna Mata so yadda kuka nunamun, me sunanki tayi dariya tace HURUL'IN ambil tace Nyc name shiyasa kikayi kamada masu sunan, baffa malam ka taimakeni kabani hurul in tafi da ita zata zama abun alfahari a gareku, baffa karka manta ni yar halak ce yaxama wajibi in San Wanda Yamun abun kwarai.
Ambil Kenan dadina dake zance mushiga daga ciki, guri aka shinfida musu suka zauna aka kawo musu fura da suga, tuni Inna ta Milka musu tuwo miyar kuka babu yabo babu fallasa aka yanka musu zabbi kwarai su baffa malam Mutanen Kirkine.
Duk sunci sun koshi babu wani space nan aka Fara hiran Yaushe rabo ambil tasanar dasu cewa Tana karatun lauya saboda har Yanzu burinta yananan Kuma tasanarda su baffa malam cewa king Dan uwanta ne hajiya kuwa goggonta ce nan akayita kakabi.

kwanansu biyu a GARIN ambil har gidan amatul-jabbar taje amatu tayi aure harda yaro ambil Takai mata shatara ta ARZIKI ambil bata mance kuruciya ba, neehlah kuwa sai washe baki takeyi saboda tanason kauye Kodan Karin ilimi, saboda Akwai life iri daban daban king ya bada wata shawara nacewa zasu wuce dasu baffa malam zuwa birni koh Dan Sana'a Yasamun masa ita kuma hurul tasamu gurbin shiga makaranta saboda yalura ambil batada wani farinciki illah su baffa malam,
Haka akayi suka saida bisashensu baki daya basu kwashi komai ba sai tsummo karansu sukayiwa yan uwa da abokan arzuka bankwana yan bakin ciki Nayi masu cewa saidasu ambil zatayi suna cewa abun sai Dua'ii.
ZARIA BIRNIN ILIMI
gidanda arfat tafita nan aka sasu baffa malam Inna kuwa Duk tabi ta rude haka rayuwa taci gaba ambil taci gaba da neman iliminta kamar KULLUN Allah shine abin Godiya sun shafe shekarun suna  karatu kafin su kare akayi hidimar biki harda na ambil Don hajiya tace bata aminche da tariya kandas ba,  kowacce ankaita gidanta Neehlah ta angwance da abba jumare a matsayin mata tabiyu saidai neehlah tayi hakuri saboda ta hadu Da kishiya shuuma Amma komai yayi zafi maganinsa Allah, ranan Da king yasan ambil ranan komai yadawo masa sabo ranar yasan cewa yayi aure a iya zamamsa Da arfat saboda ambil ta waye Don tayiwa Kanta abunda ya dace Da ita sannan tasan Duk wani jadawalin zama Da miji shiyasa ta tsinci rayuwarta abun shaawa girki kwaliya iya magana kissa shagwaba baa barta a bayaba Don tasamu kulawa wajen aunty Zainab kwarai Wacce itace role model dinta bakowa bace illah AUNTY SIS.

*Bayan wasu lokuta*

ambil anzama babbar lauya Don har school of law Dake Abuja taje Dukda izinin king Wanda Ya ajiye aikin likitan mata yakoma kasuwanci tsundum daga China xuwa Nigeria zuwa Dubai, Ambil tasamu goyon baya wajen kawayenta SALMA LAR Wacce ta tsunduma wajen farauto mata alhaji chile Wanda a majiya Mai karfi ance yananan Da ransa, Alhaji chile yayi kaurin suna wajen neman Mata Da kashe musu kudi SALMA LAR ba yar Iska bace Amman taci alwashin dankan chile a Hannu tareda kwace Duk wani abunda ya mallaka Da karfin Sharia sannan tareda Yankee masa hukunci yadda addinin musulunci Ya tanadar koh ince constitution,
Har office Dinsa SALMA taje Don neman aiki Amman ganinta yasa dukya rude Ya aminche da SALMA a matsayin sakatariyya taji dadi yadda yayi saurin amincewa Da ita Dukda fuskarta batayi kamada masu Kirki ba sunyi labari Sosai Da ita har yake sanarda ita cewa arzikinsa yanada mafari taso tambayansa mafari saita fuske saboda sanin aikinta Duk abunda salma take  recording takeyi saboda gaba, kamar KULLUN ambil ta shirya zuwa wajen aiki Don zuwa lectures dayake a off campus take SALMA ta sanarda ita komai yaji dadi tace gobe zamuje MAITAMA SULE saboda in nuna miki gidanmu Don nasan gidan saidai idan an chanza mishi tsari saboda koda Nake yarinya ba kasafai na mance komai ba.
WACECE SALMA LAR
SALMA LAR yar asalin GARIN kogi ce wato yarenta IBRA ne gaba Gidansu su biyarne inda itace ta hudu gaba daya rayuwarta a Los Angeles California tayishi saboda Aiki daya kai mahaifinta musulmace Amma mahaifiyarta tuba tayi Amman tsarinsu da shigarsu irinta turawa ne Amma tarike Addinin musulunci Hannu bibbiyu,  tayi karatunta a crescent university Abeokuta bayan sun dawo kasa Nigeria a school of law suka kulla kawance da ambil har take sanarda ita labarinta shine ta dauki alwashin ganin bayan chile kuma iyayenta sun aminche sunkuma Goya mata baya Dari bisa Dari.
Sunje MAITAMA ambil ta nuna Gidansu yananan yadda yake buga gidan sukayi wata mata ta leko suka gaisa Sosai SALMA LAR tace "Idan baxaki damuba pls mushiga daga ciki"Mata tayi kasake taki motsi alaman ban yarda dakuba ganin hk yasa ambil tace koh zaki iya sanar damu  wajen Wanda kuka siya wannan gidan?
mata tace "Eh wajen wani mutumi muka tsiya kuma ance mana gidan marayune zaa raba gado shiyasa ake neman masu siya"
Ambil tayi tsaye tace biri yayi kamada Mutum koh zamusan sunan mutumin? Matar tace Alhaji chile ambil tace cikin ranta zanyi hukunci Da yatsuna saboda alhaji chile ya gamamun da rayuwa, sallama sukayi da Matar suka wuce kowacce na sake sake a ransa Ambil tace SALMA LAR Inaso indauki mataki a hannuna  in kashe chile harsashin bindiga........

WANI GARIN.....yafi gaban kunuOnde histórias criam vida. Descubra agora