Part One

7.9K 311 1
                                    

🚘"KUSKURENMU"🚖

Part 1
Dedicated To All Readers

Writting By Zulayihat Aliyu (Mmn RJ)

Bismillahir'Rahmanir'Rahim

Government Girls Secondry
School Zaria.

Break Time

Bebygirls mai ziyyah takeyi a group din Housewife's? Kwana biyu sai wani kuskus sukeyi, ko ni kadai na lura da hakan?. Kin san ziyya da shishshigi ai, Allah yasa ba wani tsiyar take kulla musu ba.
daya daga cikin yan matan ta fada tana tabe baki. Bari tazo koma me nene yau sai tayi mana bayani dayar ta fada tana faman shan rakenta, da alama yana mata dadi sosai.Asmau( Asma), Fatima (tima), Aisha(Ashty), Halima(haly). Kena yan matane kyawawa ajin farko, duka- duka basu wuce 17 years ba.
Wadda suka kira da Ziyyah ce ta iso inda suke dauke, da murmush h!!! Bebe meye labari? Fatima ce ta fara magana yana wurinki, don duk nan jiranki muke muji, meye hadinki da Housewife's group? Ziyya mai zatayi ban da dariya. Sake baki sukai suna kallonta, inda sabo sun saba da halinta, saida tayi mai isarta sannan tace" Ta samu" karan ararrawa ne ya katse musu zancen. Aisha tace"bari kawai sai antashi kinga yanzu zaa koma break. Ok no prb. Mikewa sukai gaba daya suka nufi class. SS 3A naga an rubuta a saman class din, kujerune masu daukan mutun hudu jere, gafe da gefe da wasu a tsakiya. A hankali kowacce ta nemi wurin zamanta. Sit dinsu ne a farko by right. Ziyya ce ta mike to nikam na koma tsakiya, don wannan dan akuyan yanzu zai tsigo,niko ba ganewa nake ba. Ok kawai sukace, can desk din tsakiya by right ta nufa,

Hi frends ta fada tana musu murmushi, owoo!!!! Ziyya I'm not going Any were. Daya daga cikin yan matan ta fada. Haba maryam bama haka dake, karkisa a mana dariya mana. Ziyya ta fada da fuskar ban tausayi. Maryam tace nima fa yau karatun novel zanyi don nima ba ganewa nakeba. Zoki zauna ni bari in koma can din. Ta kusa da maryam ta fada, tashi tayi taba ziyya wurinta, ta koma wurin ziyyah. Baki da mutunci maryam. Ko kuma bamu da mutunci ba. Ta mayar mata.
Yauwa Akwai sabon littafine? Ziyya ta tambayi maryam. Maryam ta bude jakarta tafito da books sunkai biyar, kin gansu sababbin fitowa ne, ziyya ta zabi biyu 1&2. Oya ban kudina yau ba bashi. Yau maryam na lura rashin mutunci kikeji yau. Ta ciro 40 ta mika mata.
Book din biology ta dauko ta saka novel dinta a ciki, kai ka rantse da Allah biology take karantawa. Ga m bello nan zuwa, abin da naji daya daga ciki ta fada da karfi, nan danan kowa ya gyara zamansa. Wai gawar da zanyi naga Asmau ta dirka ta windo fatima ta jefa mata jakarta, ta gyara zamanta kamar ba'ayi komai ba.
Asmy na hango bayan wata bishiya, ta zauna.ta bude jakarta karamin qurani naga ta fito dashi da note book, da pen. Suratul Ankhabut ta bude, ta fara rubuta ayoyin tana bita. Kyan rubutun da yadda take karatun cikin fitarda harruffan tajwid din ya burgeni na shagala sauraron zazzakar muryarta. Kararrawar changing period ne ya kada. Maida komai tayi jaka , cikin sanda da gudun kar wani ya hangota ta nufi class dinsu.
tayi saa m. Bello ya fita, ta windo ta haura. Ashty ce tace ina kika tsaya? Tun dazu ya fita. Na tsaya hadda tane, ban rubuta ba, kin san yau m. Kabir zai karba. Wayyo Allah na, sis na manta nima banyi ba wallahi, na shiga uku. Ta fada tana daura hannu akai. Kafin next teacher ya shigo kiyi sauri ki rubuta. Muna komawa gida kiyi kokari ki haddace kafin time din islamiyyah. Asmy ta fada mata tana mika mata quranin.

A hanyar dawowar su daga sch. Yauwa ziyyah, bamu lbrn abinda ya hadaki da yan houswife group.Ashty ta fada tana tsare ziyya da ido. Ziyya mai zatayi banda dariya, har suka fara jin Haushinta.
Bebs kunsan me? Ta fada tana kokarin maida dariyarta. Kun san dai graduation dinmu ya kusa, ga ashobi da contribution na party. Ni kuma banda kudi, ban da in da zan samosu. Ina tunanin yadda zan hada kudin sai idea ta fadomin. Kun san mai? Duk sun kagu suji mai za tace. Zan fara business wanda zai kawo kudi in no time. Asmy ce tace kamar mefa?

Maganin mata.......

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now