Seventeen 17

1.5K 122 0
                                    

After 3 hours

Kowa ya samu natsuwa an zazzauna, kowa ka kallah yana cikin farin ciki da Anna shuwa.

Gefe can inda yafi ko ina kayatuwa a wurin Na hango saurayin nan da naji an Kira da Joseph, cikin wani hadaddun English wares shirt dark blue and white, da black trouser. Yayi matukar kyau ,kana ganin sa Kasan yana cikin farin ciki.

Granfah da grandma suna kusa dashi suna hira, da alama hirar ta musu dadi sai dariya suke.

in ka dauke shi da murmushi yaki barin fuskar shi.

Grandpa ne ya tashi ya Fara jawabi cikin harshen French, Nan danan na kalli kawar da nayi, kun sanni da shishshigi ko Dan inji kokof, nace pls be my ears.

Tai murmushi tafara fassaramin abinda grandpa yake fada. " adduar coci yafara, sannan sai godiya ga yan'uwa, da abokan arziki da suka zo tayashi murnan zuwan jikansa, abin alfaharinsa.

Wannan shine zuwansa Na farko N'dmaina, Tare da gabatar mai da yan'uwan sa da matsayin ko wannen su a gareshi, Sannan ya rufe dama kowa fatan komawa gida lfy, Tare da godiya mai yawa.

Joseph ne ya tashi shima yai jawabin godiya,  tare da nuna Jin dadin sa, na karramasa da sukayi, Tare da musu fatan alheri.

Anci ansha,  da yake abincin ba irin Wanda na sani bane,  tsakura kawai nima nayi, sai nama da naci na gyatse, Har yamma can sannan taro ya watse.

Bishop Joseph Awudd, Mazaunin garin n'djamaina, shuwa Arabs ne.
Languages dinsu shine Chadian Arabic sai French. Matarsa daya Teresa, yaransu uku. John, jerom, sai autarsu Jasmine. Suntaso cikin kulawa tare da so da kauna mai yawa daga iyayen su.

Joseph Awudd yana rike da matsayin; The cathedral in n'djamaina ( bishop) na central Church. John shine babba a yayansa,Bayan kammala degree din John ya samu Aiki da NNPC dake Nigeria. Da kyar Bishop Joseph ya yadda ya je nigeria Aiki, yafison yana kusa dashi, gashi, shi yake sa rai ya gajeshi,. Shekara Biyu da Fara aikin sa aka mai transfer zuwa Maiduguri. A wannan lokacin, yayi aure da matarsa  Rose. Yaronsa na biyu jerom ya Gama nashi karatun doctor, ya fara Aiki da babban hospital Na n'djamaina.

Bayan shekara daya jesmin ta kammala secondery dinta, Inda zamanta ya koma wurin John da zama.

Wannan kenann........

Joseph Abraham Awudd  shine asalin sunan sa. dan shekara 27aduniya, Da' ga jesmin Joseph Awudd. Rayuwarsa kaf a America yayita, Bai taba zuwa Africa ba sai wannan Karon.

        Muryar da naji sama- sama,  ya Sani saurin nufar falo inga meke faruwa.

Haba my son, banji dadin abin da kayiba, Duk abinda mutanen nan sukayi mana,amma kabi irin ra'ayin su? Duk da dai kana da right din kayi zabin abinda kake so, amma banji dadi ba. Murmushi Joseph yayi, "karka damu grandpa kawai ra'ayin nane ba wai don su nayi wannan zabin ba." "Yanzu dai bar wannan maganar ya labarin company din?" Grandpa yayi murmushi "komai lfy, yana Aiki yadda ya kamata  In ka huta uncle Dinka zai zagaya da kai ka gani, harda gonakin duka. Sannan ya kamata ka Fara maganar aure."

Joseph ya yi murmushi "karka damu zanyi nan da lokaci kadan by the greats of God."

"In bazaka damu ba akwai yan'mata kyawawa, zan ma grandma Dinka magana, tayi arranging din komai sai ka zabi wadda taimaka."

"Whoww!!!! You are not serious? grandpa don't worry I have my own wife, is just a matter of time, You will now her."  "Wace ce ita"? "Zaka Santa very soon." Grandpa ya daga hannu "thank you God."

Nan suka koma main fallow inda grandma da sauran jikokinta suke tasu hirar, Aka ci gaba da hira.

1 week Joseph yayi yana zagaya dangin Maman shi, da ziyartar wurare masu muhimmanci, Sannan ya Fara shirin zuwa Nigeria. Wanda kwata- kwata baima su grandpa dadi ba, don ba yadda zasuyi ne kawai suka gyaleshi, saboda basa son abinda zai bata ransa, ko kadan.

Don shi din wani blessing ne a rayuwarsu gaba daya, they love him very much.

           **********************

A kwana a tashi ba wuya,  Awurin Allah yau kusan wata daya kenan da hukuncin yaya zaid akan su Asma.  Sun kai Kara gun duk Wanda suke zato zai sa zaid ya sassauta hukuncin daya yanke masu, amma abin yaci tura.

Ammy ma dake daure musu kafa,  wannan Karon, itama cewa tayi ba ruwanta.

Dan dole ba dan sun so ba,  suka koyi girki,  Don baza su manta ranar da suka yi wata jollop rice,  gishiri da ruwa ya zarce, Ranar sunga tashin hankali. Zainab ce ta Kira yaya zaid ta fada masa, Ba a dau lokaciba sai gashi, Tasa su yayi gaba sai sun cinye kayan su,  haka su naji suna gani suka dinga tura Loma, suna hawayen wuya, sai da yaga suna kokarin yin amai, sannan ya gyalesu akan cewar zasu cinye sauran zuwa dare, in sun kasa shi zasu dun-duma suci da safe, basu ba wani abinci har sai sun cinye wannan, don baza ayi waste din abinci a banza ba.

Ya hana abasu wani abinci har sai sun cinye wannan,  Sunaji suna gani shi suka ci da daddare sauran suka ka rasa da safe.

Tun daga lokacin suka shiga tai tayisu, Suka maida hankali sosai wurin koyon girki, duk da dan banzan wulakancin da suke sha a hannun Zainab.

Wannan hukuncin yayi ma yahh dadi sosai, Don yanzu kam ta tabbatar sun fara hankali, Tare kuma da horuwa da ayyukan gida.

              *******************

Yaune bikin uncle  Muhammad,  su  Ashty kawayen amarya wohoho,  zo kaga rawar Kai, Su Asma sai wani fiffizga ake a dole an girma.

Alhamdulillah anyi biki lafiya an Kai amarya dakin ta.

Bayan bikin ne sheikh ya koma sabon gidansa,  ummi a sama,  hajjajo a kasa, Masha Allah.

Marayu primary and secondary school  ta fara aiki cikin nasara.
Wanda yayi daidai da kammala jarabawarsu Asma na W.E.E.C  da NECO.

             ********************

Yau ne family meeting,  kamar yadda family din sheikh Gyambu ke gudanarwa duk bayan 3 month.

Wannan shine meetting na farko da za'a fara gudanarwa a sabon gida.  An kawata farfajiyar gidan da kujeru na roba,  da carpet.

Wannan Karon Ashty Asma da Zainab suka yi duk girke girken, bisa dokar yaya zaid,  sai juwaira da hafsat sukayi kunun aya,  Jinger, da zobo drink. Sai smoothie.

Afra yarinyar major sulaiman tayi cake.

Wannan Karon dau kakin yaya da jikokin sheikh in ka dauke maimuna da rashin lafiya ya hanata zuwa sai yaranta maza, Kowa ya hallara.

Bayan mazan sun dawo daga sallar laasar,  bayan an motsa baki da snack da drink kowa ya natsu.

Sheikh ne ya fara jawabi bayan abdurahman ya bude taro da addua.

" kamar yadda muka saba biyawa wasu daga cikin mu, wa'anda basu sauke farali ba, Don suje su sauke farali, To wannan Karon ma haka, Zamu biyawa mutun uku, wannan Karon sabanin bibbiyu da muke biya a baya. Wanda zasu samu wannan damar kuwa sune : maryam,  saratu sai  Ibrahim yaron gwaggonku."

Zo kaga farin ciki a wurin wannan zuria musammam ummi wadda harda hawayenta, don farin ciki, Ita ko mai Zata cewa wannan family, ??
Nan fa aka shiga taya su murna, Da fatan yin aikin hajji karbabbe.

Ashty da Asma na like jikin hajjajo saman carpet, Aliyu ya samu Aliyun mejor da yaransu maryam, sai rigima suke. 

Shigowan doctor Abubakar ne ya ja hankalinsu ga kofar, bayan amsa sallamar da sukayi, don da yawansu basu Lura baya nanba,  kasan cewar sun dawo masallaci dashi.

Wanda ke bayan sa ne yasa daukacin yayan sheikh da shi kansa tashi cikin kidima........

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now