Nineteen 19

1.4K 179 0
                                    

"Salamu Alaikum. Haba yan'uwa I'm new in writing novels,  wannan ne first. Vote dinku shi zai Kara min kwarin gwuiwar cewa sakon da nake kokarin isarwa yana karbuwa."

"You can comment, Also."

Gaba dayan su, sun hallara a compound din,  bayan idar da sallar.
Ibrahim ne dai har lokacin shiru,  Wanda dau kacin hankalin iyayen yana kan kofar shigowa.

Hajjajo kam, kin fitowa tayi,  sai da sheikh ya nuna mata matukar bacin ransa sannan ta fito, Kamar dazu su asma na kusa da hajjajo a Capet,.
Kowa yayi zugun - zugun tare da ko karin has a so abin da ke faruwa, Kasan cewar har lokacin iyayen nasu basu, basu wani haske ba,  Dan gane da abin da ke faruwa, sai kus-kus suke a tsakaninsu. Shigowar sa yasa duk suka mai da hankalin su kansa.  Banda iyayen da dama hankalin su na kan kofar. Kujerar dake kusa da doctor ya zauna Don da alama don shi aka tanada.

"Sorry for the delayed "  a bin da ya iya fada kenan tare da ci gaba da danna wayar dake hannun sa,  ba tare daya Kalli kowa ba. Duk ido na kansa,  Wanda shi kan shi yaji hakan a jikin sa. Sallama sheikh yayi  bayan sun amsa ya Fara bayani cikin harshen turanci, sabanin da da baya yadda yayi kowane yare a cikin iyalan nashi sai fulfulde.

"Alhamdulillah *3 hakika you ranar farin ciki ne,  muna Mika godiya GA  Allahu S.W.A da ya nuna mana wannan rana Mai matukar muhimmanci, Mun dade muna fatan wannan rana. Wanna da kuke gani" ya fada yana nuna musu Ibrahim. ba kowa bane face dan uwanku,  kuma yaya a gareku, Shine jika na na farko da na samu daga dana Ibrahim, Ibrahim ya auri mahaifiyarsa kafin kammala degree dinsa, sun hadu da Jasmin a makaranta lokacin Tana karatun deploma, shi kuma yana degree. Allah ya saka soyayya juna a zukatansu, Soyayyarsu sai da tayi karfi sannan Muka farga, A lokacin nayi iya kokarina ganin Ibrahim ya rabu da Jasmin amma Abu yaki yi wuwa.

Da gani har hajja munyi iya yinmu ganin ya rabu da ita Abu ya gagara.
Ana cikin haka, Ibrahim yazo da labarin cewa Jasmin ta yadda zata musulunta, matukar zai aureta.
Wanna Abu ya min dadi,  cikin kan kani lokaci, Jasmin ta karbi shahada,  jin wannan labari yasa hankalin iyayenta ya tashi,  nan fa aka Fara dauki ba dadi.  Har kotu yayanta yakai Ibrahim kan ya tilastawa kanwarsa shiga addinin musulunci,  Kasan cewar Jasmin tana zama da yayanta a maiduguri,  karatu ya kawota Zaria,  inda ainihin iyayenta ke zaune a N' djamaina. Sharia sosai akayi, daga karshe aka bata zabin zaban addinin  da ta keso, Nan take ta zabi musulunci. Wanda Sanadiyyar haka yasa yayanta,  da sauran yanuwanta suka yanke duk wata alaka dake tsakanin su da ita.
Ganin haka yasa ni yanke hukuncin daura auren su, Wanda hakan bai ma hajja da diba.  Mun samu sabani sosai Wanda sai da iyayenmu suka shiga maganar  sannan aka samu maslaha.

An daura auren Ibrahim da Jasmin, wadda ta zabi suna juwairiyyah, Bayan musuluntarta. Juwairiyya yariyace Mai hankali da na tsuwa, ga gimama na gaba da ita, Uwa uba rikon Addini, Ta dage sosai wurin koyan karatun addini, da sauran ibadun musulunci. Zamansu da hajja abun ba dadi, hakika juwairiyya tayi hakuri kuma ta kauda kanta kan abubuwa da yawa.

Naso matuka in raba musu gida,  amma lokacin bani da karfin yin hakan, Kasan cewar shi kanshi Ibrahim din ba wani kwakw'kwarar sana'a yake da ita ba. Wahal 'halun gidannan kaf juwairiyya
Ita ke yinsu,  nayi fada har na gaji, Samun cikin juwairiyya duk baisa hajja tausayawa bai'war Allah nan ba.

Sai wata sabuwar fitina data bullo dashi, Wai bazata hada jini da na ar'na ba. Nan ma  sai da nayi ta mata nasiha sannan muka samu sauki.

Tafiya ta kamani zuwa Sudan Karo karatu,  lokacin cikin juwairiyya yana wata bakwai. Komai na bukata dai dai karfina na siya na ajiye musu,  a wadace hatta ragon Suna,  kayan yara da ita kanta maijegon da sauran abubuwan da zata bukata. Na dawo bayan wata shida,  na samu juwairiyya bata nan, San nan shi kuma Ibrahim yana cikin halin rashin lfy. Tambaya nayi ina ita juwairiyan saboda naga su abubakar ne ke kula dashi Ibrahim din. Shine hajja ke shai damin ai ina tafiya ko sati ban yiba,  juwairiyyah ta tattara kayanta ta gudu, Sun ne meta amma basu same taba. Da ibrahim yaje gun yayanta a maiduguri, shi yake shaida masa ta tafi gida can n'djamana.

Beyi kasa a gwuiwaba ya wuce Ndjamena, Wanda zuwan bai yi dadi ba don babanta sawa yayi aka tsare shi bayan dan Karen wahalar da suka bashi, sannan suka sa dole ya rubuta mata takardar saki. Wanda tun dawowar shi ya kwanta rashin lafiya.
Hakika mun shiga rudani da tashin hankali a lokacin. Ibrahim ya Dade yana jinya kafin sauki ya samu.

Munje n'dmaina nida abokina Sheila saleh da Ibrahim don a sa santa.  Amma abun yaci tura,  Munyi iya ka kokarin mu Don muga Jasmin da abunda ta Haifa amma ina abun yaci tura. Shi kansa baban Nata bai yadda ya gan muba. A bakin yaronsa muke jin juwairiyyah ta haihu namiji wata hudu da suka wuce, Sunan yaron Ibrahim. Haka muka dawo ba kwarin gwuiwa. Bayan nan munyi zuwa yakai 4 n'djamaina amma duk zuwa,  bama samun ganin shi kansa babanta haka ita ma da yaron duka. Addua ita ta zamo mana makami, tare da fatan Allah ya hada fuskokinmu da Ibrahim, ya sa muna da rabon rayuwa a tare, Saboda duk wani hanya da muke ganin zamubi Don ganin Ibrahim da mahaifiyarsa sun dawo garemu abin yaci tura, ganinsu ma ya gagara. Kasan cewa mahaifinta babban mutun ne Wanda ake ji dashi a Chad, Sannan kuma shugaba Wanda ke rike da matsayin Bishop."

Nan fa gida ya hau tsine da murnan ganin dan uwan nasu. yaya babba ne ya iso wurin Ibrahim ya rungume shi cikin tsananan farin ciki.

"I'm happy to see you brother " shima rungumeshi yayi tare da jin wani farin ciki na ratsa shi, Wai duk wa'annan yan uwansa ne?  kuma na jini. Hakika abin farin ciki ne a gareshi, Haka sauran yan'uwan suka din ga zuwa suna nuna farin cikinsu tare da gabatar da kansu. Aliyu kam jikin Ibrahim yaje ya makale mishi, don tun shigowar Ibrahim yaso zuwa wurin shi yahh ce ta hanashi, Ganin aliyu a jikinsa yasa sauran kananan yaran suma suka taru a gurin shi, Kasan cewar sa mutun Mai son yara yasa ya fara jansu jikinsa. Tare da tambayar sunayensu. Wai!!!!! aiko yasha turanci....  Su kansu iyayen da yayan duka dariya su keyi jin irin wannan turanci.

Bayan an natsa ne Sheikh ya bukaci Ibrahim da yayi musu, takaitaccen bayanin rayuwarsa. Murmushi yayi sannan ya fara kamar haka.

" Sunana Joseph Abraham Awudd....

  

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now