PART Thirteen 13

1.6K 115 5
                                    

Wanna shine dan takai taccen tarihin haduwa ta da lawan.

Asma tace "lallai kam, da na dauka ai bakwa soyayya sai dai hadi, Ashe su umma mairo ansha love." Duka umma mairo takai mata, "ja'irar yarinya." Duk kansu suka sa dariya, Umma mairo ta tashi, "Bari in yi Inda nafi wa yau, Inna biyeku sai mukai safe, Anan."

Kwance suke kan kwaton gadon hajjajo 7 by 7, ziyyah da Ashty sunyi nisa a baccin su, da alama baccin yana matukar musu dadi.

Asma kam juyi kawai take, Bacci yaki zuwa, fankar dake ta aikin juyawa take kallo tare da lulawa tunane- tunane. Ikon Allah, wato kowanne mutun da irin halittar da Allah yayi masa, wadda takan zama cikin kaddararsa. Ita tata halittar kenan," ya Allah ka min sauki da sassauci, ka jibanci al' amarina, Cikin dukkan yanayin da zan samu kaina."

A gogon dake manne a bangon ta kalla 2:14am mikewa tayi ta nufi toilet din dake manne a dakin, ta dauro Alwala. Bayan ta idar da sallah, tare da zikirai, ta gabatar da adduoin, sosai takai kukanta ga mahaliccin dukkan komai. Wata natsuwa ce ta shigeta, tare da lafawar duk wani yanayi da ta tsinci kanta a ciki.

A hankali ta Fara dukan kafar Ashty, tsaki Ashty taja, tare da janye kafarta. Cikin muryar bacci tace "ohhoh wai Don Allah daren ma baza a bar mutun yayi bacci ba.?"

Murmush Asma tayi, inda sabo ta Saba, "in kin Hakura da yaya zaid din, sai ki cigaba da baccinki, Ni ma na huta tashinki kina min sababi." Ta fada Tana gyara kwanciyarta.

Ai da sauri Ashty ta duro daga gadon, har tana make ziyyah da kafa. Yi hakuri kinji, karki ce bazaki dinga tashina ba.

Murmushi kawai Asma tayi, ta bita da kallo har ta shige toilet din, Ta kada Kai, "Ikon Allah, ita kuma Ashty Nata jarabawar kenan."

Asma taso tashi da Azumi a ranar amma ba halin hakan, saboda ranar ta kasance Saturday, kuma ranar family meeting.

                    ***************

Kafin karfe 4pm sun gama komai da za'a bukata, daya danganci abinci, da abin sha. Sun gyara ko ina, sun shimfida carpet tare da jera kujerun roba, Gurin yayi kyau kwanin sha'awa.

Bayan sunyi wanka, light mekup su kayi, yau ma Asma da Ashty, shiga iri daya suka yi, na doguwar Riga material, mai santsi, nervy blue da pusher pink, an mishi adon stones. Sunsha kyau kamar ka sure ka gudu.

Ita kanta hajjajo kasa dauke idon ta tayi kan jiko kin nata, Hamdala, tare da tasbihi take don godiya ga Allah, da ya azurtata da wannan zuria, Masu baiwa iri- iri. Tana alfahari da hakan.

Nervy blue din hijab mai hannu, wanda yazo har gwuiwa, suka sa. Kasan cewar pusher pink din yafi yawa a jikin material din, Nervy blue din takalmi.

"Masha Allah lakuwwata Illa billah."
Shine Abinda Hajjajo ta iya furtawa Tana mai murmushi cike da jin dadi.

Dadi ne yakama su, musamman Ashty, wadda tana son in tai kwalliya ace tayi kyau.

                 ***************

Masha Allah gidan sheikh gyambu yau cike yake da ya'ya da jikoki,.

Anty maimuna da Anty khadija, sai Anty karima ( uwar gidan sulaiman) ne basu samu zuwa ba, A Manya. Jiko kin ma irin su Abdullah duk basu samu zuwa ba, Amma dai Alhamdulillah, taro yayi Armashi.

Bayan Ismail ya bude taro da addua. Sheikh ne ya fara da sallama, Cikin farin cikin ganin iyalan nasa, Wanda fuskarsa ta kasa boye hakan, " Masha Allah lakuwwata illah billah," kuwa ya jata ba adadi a kan harshensa.

Bayan godiya ga Allah S .W .A cikin harshen fulatanci Wanda su kansu yaya da jikokin sun San yana daga ka' idar sheikh tsauri kan yaransa, baya yadda su yi Hausa a gabansa, Kasan cewar kowa najin fulatancin, yana kuma mayarwa.

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now