Fourthee Five 45

1.4K 116 0
                                    

"Abba ya ban maganin baffa in kai masa, Nazo zan shiga, abunda kunnuwana suka ji yasa ni tsayawa, na kasa gaba, na kasa komawa, Ji nayi kamar an dasa ni a wurin."

Nan Salim ya kwashe labarin da yaji daga bakin sheikh ya gayawa yan uwan nasa.

" ban taba tunanin rashin mutuncin matar nan yakai haka ba sai yau? Kace abinda take yiwa yahh nafila ne." Zaid ya fada cikin fushi da tashin hankali.

Sadiq ya nisa " gaskiyar Salim, ko ni a kawa haka, kun bar ganina har abada."

"A bun da yake daure min Kai daya?! New brother bai taba zuwa Nigeria ba sai wannan Karon, Ya a kayi yake da friends har haka?" Zaid ya fada.

" me be yana yin aikisa, da kuma yanayin zamani na social media, Zaka iya yin friends a ko ina a duniya."

" no I can't believe it, daga haduwa a social media ba zai sa ya ya yadda dasu sama da mu yan uwan Saba, They have been some things else."

Sadiq yayi murmushi " now I understand!!! Ranar da na fara ganinsa na ganshi da friend dinsa yusuf, Ranar har nake ce muku na san shi but na manta inda na taba ganin sa, Do you remember?"

"Yes anyi haka." Salim ya fada

Murmushi sadiq yayi. " he is the best security guard to our president son, Mustafa Mai lafiya."

"what?" Suka ce a tare.

" yes that is the truth, ranar da mu kayi celebration a aso rock na karra mamu da akayi , saboda nasarar da muka samu, na yaki da yan ta'adda  A yankin gabas, A ranar na ganshi a cikin security din da suka zo tare da Mustafa Mai lafiya. uniform dinsa ya fita daban dana sauran, Alama ce na kasan cewarsa babba a cikin su, Don irin uniform din security din president ne a jikin sa. Tun ranar da na gansa, nake ta ko karin tuno inda na sanshi. Cikin friend dinsa na yola, akwai security Dayan army ne ma, Wanda su kazo yanzu suka dauke shi, akwai security a cikin su. Duk inda security ko wani mai uniform ya shiga, akwai yadda muke iya gane juna. But they try very hard su boye kansu."

Shiru su kayi na dan lokaci.

Zaid ya katse shirun da tambayar " me Kake ganin alakarsa da Mustafa Mai lafiya?"

" ban Sani ba gaskiya, but koma menene alakace mai karfi ce a tsakaninsu, Tunda har zai iya bashi irin wannan kariya. Shi kanshi new brother in ka kalleshi da kyau, ba karamin mutun bane, Duba da kayan da yake sawa, motar da yake hawa, yanayin fatar jikinsa, da yanayinsa kawai ya isa kasan hakan."

" haka ne, ance kakansa babban Bishop ne da ake ji dashi a chardi, Pastors ma kaga yadda suke fachaka da kudi a kasar nan, balle kuma bishop."  Cewar zaid.

"So yanzu menene abunyi?" Salim ya fada

" muje kowa yayi tunanin abin da yake ganin ya dace ayi, zuwa gobe sai mu tattauna, mu tsaida mafita, But karmu manta mu yi kokari mu tashi yau Don neman jagoranci a wurin Allah." Zaid ya fada yana bude kofar motar, Nima ku sani a addua, don tunda nazo garin nan gabana ke faduwa, I don't know why."

"In sha Allah, ba komai sai alkhairi." Salim ya fada.

" bacci nake ji na gaji da yawa, Sadiq ya fada yana kulle motar, suka nufi masaukinsu.

             *********************

"Yayyo!!!!!  Allah na- Wayyo bayana!!!! " Asma ta fada tana zubewa a saman katifar dake dakin.

Duka zainab ta dada mata. Saboda jibguwa da tayi a kanta.

"Wayyo aunty zainab, abin bako tausayi, Kin san kalan wahalar da muka sha yau.? Duk jikina ciwo yake."

"Da yake ni na aike ku ba.? Dole ki huce kaina."

Ashty tayi dariya" kunyi missing wallahi, yau munsha rawar lillhore,. Kafafuna jinsu nake kamar takarda. Da kyar suke dau kana."

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now