Earteen 18

1.3K 119 0
                                    

Cikin rawar baki sheikh ya nufi  bayan doctor Abubakar,  yana mai kiran Ibrahim tare da rungume shi,  hawaye Mai dumi nabin fuskar sa.

Shima rungumeshin yayi yanajin wani farin ciki na ratsa shi.

Hajjajo kuwa, cikinta wani kuka da yayi hatta yahh dake can gefe dasu ammy sai da su kaji karan cikin. Cikin tsananin firgici ta Mike Tana layi kamar wadda Tasha kayan Maye, Ta nufi part dinta.

Ganin yanda take hada hanya Tana neman faduwa,  yasa su Asma kamata zuwa part din ta zuciyoyin su cike da tambayoyi. Suna shiga toilet ta wuce tare da rufo kofar.

Doctor Ibrahim kam yana nan tsaye ya rasa a ina kansa yake, A hankali ya sulale zai zube a kasa,  cikin hanzari major ya taro shi amma ina ya Riga ya sume.

Cikin tashin hankali samarin suka yo kansa, cikin tashin hankali suka  kinkime shi zuwa falon hajjajo,  kwantar dashi sukayi tare da kunna fan,  ruwa Mai sanyi major ya Fara shafa Mai. Tuni su Asma dake tsaye a dakin suna jiran fitowar hajjajo, Daga toilet, hankali a tashe.  Ganin an shigo da abban su a sume yasa suka fara kuka.

A compound din kuwa,  sheikh ne ya kamo hannun bakon da ya Kira da Ibrahim suka nufi part din hajjajo.
Kusa da inda aka kwantar da doctor ya zaunar da bakon,  abokinsa da sukaxo tare ya zauna kujerar kusa dashi. Sheikh ne ya amshi ruwan tare da tofa adduoi cikin ruwan, Zama yayi sosai ya daura kan doctor a cinyarsa yana shafa masa ruwan a kan fuskarsa zuwa kirjinsa.

Dau kacin yaran duk Wanda ka kalla yana cikin tashin hankali da damuwa, Ganin yanda lokaci kadan,  gaba daya iyayen sun shiga wani Hali, Sun rasa dalilin hakan. Doctor Abubakar ne yama yaran a lama dasu basu wuri.

A hankali suka dinga ficewa, Cikin damuwa, da dun bin tambayoyi.

Dogon Ajiyar zuciya doctor yaja, tare da bude idon sa a hankali, IDon sune ya hadu da bakon dake zaune kusa dashi,  idon sa cike da kwalla. Cikin rawar murya da bata fita sosai,  ya daga hannunsa yana nuna bakon,  "ibrahim kaine ko mafarkin da na Saba ne "?

Hannunsa bakon ya riko tare da rungume juna, a tare suka saki kuka, Kam doctor ya rungumeshi yana kuka yana cewa "Allah na gode maka, daka dawomin da farin cikina."

Gaba daya yanuwan doctor har sheikh kuka suke,Wanda ni kaina na rasa na menene?

Sun Dade rungume da juna kafin ya sakeshi, yana rike da hannunshi kamar za'a kwace Mai shi.

Cikin gurba taccen turanci Mai surke da French Wanda aka Kira da Ibrahim yace " I'm glad to see you,  today is very important in my life,  For the first time in my entire life I see you for the first time, I'm dreaming for this day."

"Me too son."  Cewar doctor yana shafa kansa,. Cikin tsananin shaukin son yaron.

A hankali ya tashi yaje ya dauro  Alwala yazo ya Fara gudanar da sujudush shukur. ( sujada don godiya GA  Allah bisa wani niima data sameka)

Hakan yaba Doctor Abubakar damar gabatar da mejor,  Ismail,  uncle Muhammad,  da kuma sheikh ga Ibrahim,  tare da bayanin matsayin kowanne a wurinsa..

Sunyi matukar farin ciki da ganinsa. 

Ibrahim ya gabatar musu da friend dinsa yusif Ahmad Yusif.

Asma ce ta fito don duba ko Hajjajo ta fito daga toilet din,  Amma still a kulle, Juyowa tayi don tayiwa abbanta magana, Karaf idon su ya hadu Dana Ibrahim Wanda tun fito wanta idonshi na kanta.

Hatta hanjin cikin ta sai da ya kada, da sauri ta dauke idonta.

"Abba" Ta Kira doctor Abubakar) " "meya faru?" Ya tambayeta cikin harshen fillanci. "Hajjajo tun dazu ta shige toilet ta kulle kanta, Har yanzu bata fito ba."

A tare suka mike zuwa kofar toilet din, Sheikh ya kwankwasa "hajja bude kofar nan." Shiru, magiya suka fara mata, amma shiru, sai sheshshekar kukanta da suke jiyowa. Hankalin su ya masifar tashi ganin taki bude kofar. Major ne yace a balla kofar kawai, Da alama ba lafiya ba.

Ganin da gaske ba hakura zasuyi ba, kofar zasu balla yasa ta budewa, Kallo daya suka mata hankalin su ya tashi.  Bedroom dinta ta wuce kai tsaye.

Zasu bita sheikh ya dakatar dasu " lokacin magriba ya gabato, mu tafi in mun dawo, koma menene ya biyo baya."

Compound din suka fito,  sun samu sauran samarin, Nata alwala,  don haka ba bata lokaci,  suma suka dau butoci Don gudanar da tasu alwalar.

Ibrahim ne cikin harshen French ya ke cewa abokin sa Ahmad, " kayi joining din su,  zamu dan fita da emeca. By 7:30 zan dawo."

"OK" ba Matsala Ahmad ya fada tare da tashi Don raka abokin nasa wurin motar da su kazo da ita,  inda emeka ke zaman jiransu.

Doctor Ibrahim ne ya tambayi inda zasu cikin rawar murya, don ya gaza hakuri. Ahmad ya masa bayanin Ibrahim din zaije ya dawo,  by 7:30.

Danin hankalin su doctor ya tashi,  don gani suke kamar in ya tafi ba dawowa zai yiba, takowa yayi  zuwa kusa da doctor din.

Cikin murya Mai dadi,  yace " zan dan je wani wuri ne kafin ku kammala, so ga Ahmad nan, Nima ba dadewa zanyi ba."

Innalillahi wa'inna ilaihir rajiun abin da doctor ke mai-mai tawa kenan a ransa, Wani tashin hankali ne yaji ya ziyarci zuciyarsa, Me yake shirin faruwa da shine?"

Doctor Abubakar ne ya dafa kafadar sa, Dago ido yayi ya sauke akan Dan uwan nasa, Wanda da gani shima yana cikin tashin hankalin.

Kai ya girgi zama dan uwan, Alamar ya kwantar da hankalinsa, Hatta su sheikh suna cikin kaduwa, da tsoron abinda yake  tun karosu.

Har motar da suka zo da ita C R V jeep  Ahmad ya rakashi,  sannan ya koma suka wuce masallaci da samarin.

Hajjajo kam sallar ma dakyar ta samu tayita,  cikin rashin natsuwa da tashin hankali,  hakika tayi babban kuskure a rayuwarta,  Wanda har yau bata san yadda zata gyara wannan kuskuren ba. Ada tana ganin kamar abin zai wuce a haka har abadan,  Wanda shine fatan ta, but amma yanzu ta tabbatar da abin ba haka yake ba. Dak dau kacin surukanta da jikokin ta suma suna cikin damuwa,  ganin the hole mighty hajjajo,  you tayi Sanyi,  ga hawaye da yaki barin idon ta,  duk da iya da barar da take kar suga hawayen nata,  amma abun ya gagara.

Tabbas wani babban alamari ne ya tunkaro wannan family.

KUSKURENMU ( Completed )Where stories live. Discover now