Shigowar hafsat da ziyyah ya katse umma mairo daga fara basu labari.
Da gudu suka tashi Suka taro ziyyah, suka rungume juna suna farin cikin ganinta.
"Ni sake ni. Tun dazu nake jiran zuwanku, amma kuka shanyani."
Ashty tace "haba Betsy very sorry, munje ganin matar Uncle ne, kin Santa da surutu, bamu bar gidan ba sai kusan magarib, Shi yasa bamu karaso ba."
Asma tace "dama da sassafe muke son mu zo." "Na Hutar daku tunda gashi ni nazo." Ta fada tana tura baki." Ta gaishe da su hajjajo suka nemi wuri suka zauna.
"Kakus bata San kuna nanba da ta shigo, ita ta koroni." Cewar ziyyah. Umma mairo tace "ayyah kice da hirar tafi dadi."
"Kwarai kuwa, Fishi take don nace yau nan zan kwana." Hajjajo tace "banda abin kaka randa kikayi aure fah ???" "Barta kawai nima yau nadan sarara." Hafsat ta ce "ko kuma ita ta huta da ke ba, yau za tayi bacci harda saleba."
Umma mairo ce ta fara basu labarin haduwar ta da mijin ta... Malan lawan.
"Mairamu daso dutse baki San tsoroba, Shi kanshi tsoron ma tsoron ki yake, Yar gidan iya Mai fura, tilo ta malam garba,"Kirari na kenan a kauyen mu.
Na rasa mahaifiyata tun ina shekara daya a duniya. Na taso hannun kishiyar uwata iya, wadda akafi sani da Mai fura. Mata mai mutunci da dattako, Tarike ni amana, bansan rashin uwaba.
Mahaifina malan garba sana 'arsa saida kayan miya, yana noma, kuma da kiyo. Ban rasa komai ba, wani abun ma a wurina ake fara ganin sa, a kauyenmu.
Rashin tsorona, shi yasa ni fice a kauyen mu,. Ina da kawaye, sosai, Amma munfi shiri da Indo, Sai dijama, Makotan mu ne Mun taso tare.
Lokacin da na zama budurwa yar shekara sha daya, Sai samari suka min cahhh, ba wani kyau nake dashi ba, Sai dai Nasamu tarbiya Mai kyau.
Ban taba damuwa da in saurari kowa ba, tun abun baya damun mahaifina har yazo yafara damuwa, Lokacin Indo da dijama an sa musu Ranar aure.
Ranar juma'a Mun fito talla, Bayan mun sayar, Muna hanyar komawa gida, Dai -dai filin masallaci, muka samu ana wasa da maciji. Indo da dijama suka ce baza su jeba suna tsoro, "Don Allah muje ba Abin da Zai muku."Indo tace "gaskiya ba zan jeba, Duk lokacin da na Kalli maciji Bana iya bacci, na dinga tsorata kenan cikin dare, nikam na tafi. "Sai ki ta tafiya ai, na fada tare da Jan hannun dijama, Dole badan taso ba ta bini, muka kutsa Cikin Dan dazon yara.
Muna Cikin kallo dijama tace "lahhh kinga Dan maigari dake binni can, Shima yazo kallo."
Da sauri na waigo "yana Ina?" Ina son in ganshi Saboda yadda Yan matan kauyenmu suka mato a kansa.
Wani dogon tsaki naja "Wai Dama wannan shine Dan maigarin da kuka ishi mutane da sunansa. Na dauka zanga wani kyakyawan saurayi." Kai mairo menene makusarsa?
Tsaki na kuma ja, "Kinaga hancinsa kamar an buga daddawa, ga katon baki, Ji kofofin hancinsa kamar kofar shigowa gari......"
Ai ban karasa ba Saboda wani sanyi da naji a kaffuwa na, Kallon kafar nayi don ganin abin da ya hau min kafar, Daya daga cikin macizan da ake wasa da shi ne, ya nannade min kafa, tare da fasa Kai,Nan take nai suman tsaye, tare da sake fitsari, saboda azabar tsoro.
Nan fa hankalin masu wasa da macijin da sauran jama'a ya tashi.
Yara kuwa suka watse kowa ya nufi gidansu yana ihu.Su kansu masu wasa da macizan sun rasa yadda za suyi su daukeshi daga kafar tawa, don yanda ya fusata ya fasa Kai yana huci. cikin hukun cin Allah bai bi ta kaina ba, da fitsarin Dana sake ya wanke shi.
Dan maigarin mu Wanda ake Kira lawan, ne ya lallabo a hankali da babbar rigar abokinsa da sukazo kallo tare,. Cikin zafin nama, ganin shi, macijin ya kawa mai sara, yayi tsalle tare da Rufe shi da babbar rigar, ya fara wuntsil 2, yay maza ya chafke wuyan shi, Man fa aka dau tafi, Saboda wannan jarumta da rashin tsoro, da ya nuna.
A hankali ya karaso kusa dani " Kee keee" Ina nikam nayi nisa a suman tsaye. Ya sa hannu ya jijjiga kafadata sai na zube kasa, a sannan suka gane suma nayi.
An samin ruwa sosai amma ban farfado ba,. Juyowa yayi yana tambaya yar gidan waye? "Yar didan malan garba Mai kayan miya ce."
Cichchibana yayi ya nufi hanyar gidanmu Dani yara suka rufa masa baya ,cikin jimami Don Sun dauka mutuwa nayi.
Kafin mukarasa har ankai ma iya Mai fura da babana a kasuwa labarin abin da yafaru, cikin tashin hankali iya ta fito sukayi kicibis a soro ana shigowa Dani, ganin yanda aka shigo Dani yasa iya rushewa da kuka don itama ta dauka mutuwa nayi.
babana ma ya shigo a firgice ko takalmi babu, hula a hannu, ganin yadda suka dimauta yasa lawan yace "ku kwantar da hankalin ku, ba mutuwa tayi ba, dogon suma ne."
ruwa mai sanyi aka watsa min, nai dogon ajiyar zuciya, tare da tashi a ra zane ina ihu, baba ne yai saurin rikoni, "mairamu kwantar da hankalinki"
Ido na dinga zarowa ina dube -duben inda zanga macijin, Ban ma Lura da dan dazon yara da manyan dake kaina ba, cikin alhinin abin da ya faru dani.
Muryar aminin babana naji yana hamdala.
Sai lokacin hankalina ya Fara dawo wa jiki na. Jina nayi kamar a jikin mutun nake kwance,.
A hankali na tashi tare da waigawa in ga Wanda na kwanta a cinyarsa.
Ido hudu mukayi da lawan, nan take gabana ya fadi, Ko karin Mike wa nake da sauri.
Babana ya taroni, "zauna tukunna mairo." Don ya lura har lokacin bana cikin natsuwata.
Godiya sosai babana yayi wa lawan, tare da sa Mai albarka, Su kai sallama da babana ya tafi.
Kwana kusan uku ina cikin halin rashin natsuwa, saboda firgita da nakeyi, da Abu yadan tabani zanyi saurin razana.
Sai da babana yasa aka min taimako tukun na samu natsuwa.
Duk kwanakin nan kullun sai lawan yazo duba jikina, tun bana sakewa dashi, har muka Saba. Bayan sati daya na war ware, na ci gaba da hidimomi na.
"Mairamu daso dutse baki San tsoroba, sai na maciji."
Shine sabon kirarin da aka koma yimin.
Soyayya ce da shakuwa ya shiga tsakanina da lawan, cikin lokaci kadan kowa ya San labarin soyayyata da lawan, Abin ka da karamin kauye.
Bamu dauki lokaci ba, iyaye suka shigo cikin maganar. Bayan bikinmu da wata biyu, Lawan ya daukoni zuwa nan Zaria, inda yake aiki a railway......

ESTÁS LEYENDO
KUSKURENMU ( Completed )
RomanceLabari ne da ya kunshi ilmantarwa, fadakarwa, tare da nishadan tarwa. sannan yazo da sabon salon da yasha banban da sauran labaran da kika/ka taba karantawa.